Posts

WAIWAYE ADON TAFIYA 16 - 20

WAIWAYE ADON TAFIYA 16 Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W) Munji cewa Sahabi Umar ibn Khaddab (R.A) ya musulunta, kuma muka ambaci cewa Annabin tsira da Aminchi ne yayi addu'ar cewa Allah ya karfafi addinin musulunchi da Umar... Wannan shine abinda ya tabbata a ruwayoyi wayanda na riska, saidai guda daya wadda Nana Aishatu uwar muminai take cewa abinda ya tabbata shine Annabi yace “Allah ka daukaka umar da addinin musulunchi...” dalilinta kuwa shine, tace “Shi musulunchi wani baya iya daukaka shi, saidai shi ya daukaka mutum.” Wannan fahimtarta ce.  Allah ne mafi sani. ★ Kafirai da sukaga musulunchi yanata daukaka kuma sukaga duk matakin daya kamata su dauka sun dauka amma abu yaki ci yaki cinyewa sai suka sauya shawara.  Suka nemi a basu Annabi, a sallama musu shi, su kasheshi, zasu musanya shi da wani daga cikinsu, sannan zasu biya dukiya mai tarin yawa... Abu Dalib da yaji bukatarsu sai yace amma gaskiya wannan abu nasu ya bashi mamaki, wannan wanne irin shirme ne, ya basu dan...

WAIWAYE ADON TAFIYA 11 - 15

WAIWAYE ADON TAFIYA 11 Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)... Duk da barazana da tsoratarwa da sukewa Annabi amma babu abinda hakan ya kara masa sai himma da kuma kara zage damtse wajen kira, don haka suka takurawa Abi Dalib akan sai ya damka musu Annabi ko kuma ya basu dama su cimma sa, amma hakan bata samu ba...  Ka duba ka gani, kafiraine, amma kuma suna girmama na gaba dasu kuma suna jin nauyin cin zarafin mai shekaru a cikinsu, ba irin matasa da muke dasu yanzu ba, wanda wani sai kaji bama gama-garin mutane yake zagi ko cin mutunchi ba, malaman addini da shuwagabanni zakaga yana zagi kuma ko a jikinsa, kaga sannan jahilcinsa yafi jahilcin jahilan jahiliyya... Daga karshe da suka rasa yadda zasuyi, sai suka yanke shawarar cewa kowane dangi yaje yayi maganin wayanda sukai imani a cikinsu... Khabbab ibn Aratti saboda ya musulunta riga ake cire masa, a baza garwashi a kasa a kwantar dashi akai sannan a kirawo kato ya taka kirjinsa ya danne shi... Amma hakan bai saka yabar musulunchi ...

TSARABAR JUMA'A DAGA ABU UMAR ALKANAWY

Image
*Tsarabar Abu Umar Alkanawy*. (3) Lokacin Khalifancin Sahabi Abubakar (R.A) ya shugabantar da Khalid bn Walid, bayan Sayyadi Abubakar shi kuma sahabi Umar bn Khaddab (R.A) saiya cire Khalid (R.A) ya maye gurbinsa da Abu Ubaida bn Jarrah (R.A)... Ko menene dalili? Shaikhul Islam Ibn Taymiyya (R) yace “Shi Abubakar (R.A) mutum  ne mai sanyi mai sauki, saboda haka saiya shugabantar da Khalid (R.A) wanda mun sani cewa shi mutum ne mai tsanani. Shi kuma lokacin da Sahabi Umar ya hau Khalifanci, mutumne mai tsanani don haka saiya sauya Khalid ya shugabantar da Abu Ubaida (R.A) wanda shi kuma mutum ne mai sanyi... A tsari na shugabanchi haka akafi bukata a hada zafi da sanyi, kada a hada zafafa biyu sai tsaurin yayi yawa, hakanan kada a hada sanyaya biyu sai sanyi ko sakaci yayi yawa. Nace: Ka duba lokacin da Allah ya turo Annabi musa mana, saboda yasan yanada tsanani sai ya sanya masa dan'uwa mai sanyi wato Haruna (A.S). 

TSARABA DAGA SHEHU USMAN DAN FODIO

Image
*Tsarabar Abu Umar Alkanawy* Shehu Usman Dan Fodio yana cewa... “... Daga cikin bidi'o'i akwai addu'a bayan idar da kowace sallah ta wata fuska abar sani, itace liman ya rinka addu'a su kuma mamu su rinka amsawa da ameen, wannan bidi'a ce makruhiya a mazhabar imam malik, wasu malaman kuma sukace bidi'a ce mustahsana, wasu sukace bidi'a ce abar so.  Shehu Usman Dan Fodio yaci gaba da cewa... “...Sai dai abin da yake na asali shi ne kowane mutum yayi addu'arsa, sai dai fa ba a yi saɓani ba cewa ba a rawaito daga Annabi (S.A.W) yayi sallama daga sallah sannan ya ɗaga hannunsa yayi addu'a mamu kuma sukace ameen ga addu'arsa ba, hakanan ba a rawaito wani daga halifofinsa shiryayyu yayi haka ba, Gaba ɗayansu.  Shehu Usman ɗan Fodio bai tsaya haka ba sai ya ci gaba da cewa... “...Shi kuwa duk abin da Annabi (S.A.W) bai taɓa aikata shi ba, haka nan ko ɗaya daga cikin sahabbai. Babu shakka barin wannan abin shi yafi akan aikatashi... كتاب بيان...

WAIWAYE ADON TAFIYA. (6 - 10)

WAIWAYE ADON TAFIYA 6 Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)... Masoyi (S.A.W) tun daga yarintarsa ya taso da dabi'u mafi kyawu, dubi yadda muka bada labari  yadda kwanakin jahiliyya suke, amma sai Allah ya bawa Annabi muhammad kariya daga dukkanin wasu halaye ababen kyamata.  Da ace a yarintar Annabi an sameshi da wani laifi, kamar karya, rashin girmama na gaba, tsananin son mulki da sauran halaye to da abokan adawarsa sun tada jijiyoyin wuya akan abinda aka sameshi dashi mara kyau. Amma sai Allah ya tsarkakeshi tsarkakewa. Mafi girman abinda larabawa suka himmatu akai a wayannan kwanaki akwai caca, shan giya da kuma bautar gumaka, amma Annabi bai taba yin koda daya daga cikin wannan ba. Domin ya haramtawa kansa shan giya, caca, bautar gumaka ko kuma cin abin yankan da aka yankashi ga gunki. Tun a yarintarsa ya tsani gumaka kamar yadda ya tsani waka da alfasha... (Nurul Yaqeen 23)  Har saida mutane suke kiransa da sunaye na girmamawa da karramawa, cikin wayannan sunaye akwai A...

KASATA NIGERIA

Image
Shekaru lambobi ne kawai, aikin da akai a cikinsu shi yake mayar da shekarun su zama ababen sha'awa ko ababen kyamata...  Ko kana iya tuno wata shekara da wani abin burgewa ko sha'awa ya faru?  Idan ka tuno me kake ji? Hakanan ko kana iya tuno wani lokaci da kayi wani abin kunya, abin kyamata ko haushi? Idan ka tuno me kake ji? Wannan kadai ya isa ya tabbatar maka da cewa shekaru, watanni da kwanaki lambobi ne kawai, kuma aikin da aka aiwatar cikin wayannan lambobi shine abin dubawa ba yawan lambobin ba. Wani lokacin zai iya zama abin kunya ace ga tarin shekaru amma babu wani abin amfani a cikinsu, abin kunyar yana karuwa idan akace bayan shekarun akwai damammaki na amfanar shekarun amma ba'ai amfani da wayannan damammakin ba. Kasata Nigeria! Alfarma ta sanya ma'aikatan da zasu cicciba kasar zuwa ga tudun tsira mafi yawansu nakasassu ne, domin ba nagarta ake dubawa ba, alfarma ake dubawa. Cin hanci da rashawa sun saka ayyukan alheri sunki aiwatuwa a wannan k...

DAMISAR TAKARDA...

Image
Da Sunan Allah mai rahama mai jin kai. Mafi girman abinda yake kara daraja da kimar mutum a rayuwa shine ilmi, gwargwadon darajar abinda mutum ya ilmantu akansa gwargwadon kimarsa da darajarsa. Don haka ne zaka iske mafi darajar mutane sune Annabawa, domin sunfi kowa ilmi, kuma ilminsu shine mafi darajar ilmummuka. Tabbas ilmi yana da darajar da duk wahalar da akasha akan nemansa ko kuma duk dukiyar da aka salwantar dominsa ba'ayi asara ba. Saina tuno kissoshin da muka karanta da kuma wayanda muka ji labari na irin dawainiya da wahalhalun da magabatan wannan al'umma suka sha a wajen neman ilmi, wannan ya hada da tafiye-tafiye da wahalhalu mabambanta. Kissoshi masu taba zukata, masu cike da almara, ababen tausayi da kuma dimbin darussa. Kissoshin suka sakani cikin wani yanayi na tsananin mamaki, saidai mamakin yana kaucewa idan na tuno da girma da darajar abinda suke nema wato ilmi. Idan muka kewayo wannan zamanin, wanda muke rayuwa a ciki. Za muga tabbas akwai gagar...