Posts

Showing posts from October, 2018

SHUGABANCHI 2

Tun bayan fitowar matashi Umar daga dakin jarrabawar yake ta sake-sake a zuciyarsa gami da tunanin makomar wannan jarrabawa tasa, amma abinda yafi damunsa shine dubu dayar da aka karba daga hannunsa. “Idan naje gida me zan cewa Baba, tunda dai da ita suka dogara a matsayin cefanen gobe.” saurayin ya fada yana mai zurfafa tunani akan mafita. Duk da wasu daga yan'uwansa masu zana jarrabawa suna ta iface-iface domin kuwa yaune ranar kammala jarrabawar, yayinda wasu masu adadin shekaru basa wannan iface-iface, wasunsu ma tuni sun bar harabar makarantar... Tabbas wayanda suke baki a wajen zana wannan jarrabawar sunfi kowa murna da hauka gami da wauta. “Gaskiya ka burgeni da naga ka ware gefe ba'a wannan shirmen da kai,” wani mutum wanda yake da kimanin shekara 35 ya fada lokacin da yake mikowa matashi Umar hannu. Murmushi kawai umar yayi gami da amsa sallamar wannan mutumin. “Nifa wannan shine zana jarrabawata ta shida, kuma abu daya kawai nake nema. "Maths", shiyasa