Posts

Showing posts from May, 2023

HAKA MISALINKI YAKE!

HAKA MISALINKI YAKE!!! Wata ɗaliba ce a wata makaranta, bayan sun kammala karatun zango sai aka tsara musu jarrabawa, amma abin mamaki sai ta ƙi rubuta komai a takardarta duk da tana ganin ƴan uwanta sun duƙufa suna ta rubutu... Bayan an karɓe takardunsu duka sai ɗalibai suke tattaunawa akan wannan jarrabawa, sai wannan ɗaliba tace ai ita babu abin da ta rubuta alhalin ta sani kuma tana sane, "AISHI ILMI BA A TAKARDA YAKE BA, A ƘWAƘWALWA YAKE..." a cewar wannan ɗaliba. Sauran ɗalibai suka ɗauka da wasa take, sai da jarrabawa ta fito sai suka ganta tana ta kuka. Wata ƙawarta ta zo kanta ta tsaya tace "KINGA ABIN DA MUKE JIYE MIKI KO? RUBUTUN DA ZA KAI A TAKARDAR JARRABAWA SHI NE YAKE NUNA CEWA TABBAS KAYI KARATU, KUMA AKWAI KARATUN A KWAKWALWARKA." Yar'uwa wannan shi ne misalin matan da suke shigar banza kuma suke fakewa da cewa IMANI A ZUCI YA KE. Wannan shi ne misalin matan da suke ƙin yin biyayya ga Allah a aikace suna da'awar ai imani a zuci ya ke. Wannan