Posts

Showing posts from December, 2022

JAN HANKALI GA ƊALIBAN KIMIYYA

Sai yanzu na gane... Na riski maganganun malamai da yawa da suke cewa "Qur'anin ba littafin kimiyya ba ne, littafin shari'a ne. Sai dai ana samun ilmin kimiyya a cikinsa a matsayin mu'ujiza..." A lokutan baya sai in rasa menene hikimar yin wannan togaciya cewa Qur'ani ba littafin kimiyya ba ne. Yanzu kam alhamdulillah na gano wasu daga cikin dalilan da yasa malamai suke wannan maganar. Ga kaɗan daga ciki. ★ Dalilin saukar da Qur'ani shi ne shari'a, don haka duk wani abu da za a samu a cikinsa koma bayan shari'a ne. Don haka, idan aka ɗauki ayar Qur'ani mizanin da za a fassarata da shi, shi ne mizanin mutanen da Qur'anin ya sauka a cikinsu (Sahabbai). Su kuwa Sahabbai ana samun bayanai akansu ne a cikin littafan sunnah ingantattu. To ashe idan muka samu aya magabata sun fassarata da wata ma'ana, to ɗaukar abin da suka fassarata da shi, shi ne dai-dai. Maganar wasunsu daga ɓangaren malamai ko masana kimiyya tana iya biyo baya mutuƙar bata