Posts

Showing posts from August, 2020

KNOWLEDGE AND ITS NEGATIVE EFFECT...

Image
Nowadays, sources of knowledge such as books, videos, audio, and apps are readily available, including Islamic knowledge. However, the availability of such knowledge can have both positive and negative effects. Islamic knowledge, or Sharia, is valuable and applicable in any situation, regardless of how good or bad the circumstances or people are. But in the olden days, people had to make tireless efforts to acquire knowledge, unlike the lazy instant gratification generation of today. These days, an uneducated person can simply download or buy weighty books without any guidance or instruction. However, simply reading voluminous books doesn't equate to knowledge. Without proper guidance and education, readers may develop negative perspectives on various issues, leading to terrorism or a lack of regard for Islamic principles. As such, it's crucial to seek knowledge from pious scholars and listen to respected sheikhs who are admired for their breadth of knowledge and th

MAFI SOYUWAR MUTANE A WAJEN ALLAH!

*MAFI SOYUWAR MUTANE A WAJEN ALLAH*. Hadisi daga Ibn Umar (R.A), Masoyi (S.A.W) yana cewa _“Mafi soyuwar mutane a wajen Allah shine wanda yafi amfanar da mutane”_. *Silsilat-Assahiha* na Albaniy 906 Abu Umar Alkanawy yace  “Idan har mafi soyuwar halittu a wajen Allah sune mutane, to tabbas mafi soyuwar mutane a wajen Allah sune masu taimakon mutane. Ko ba'a fito fili an gaya maka ba zaka gane idan kayi la'akari da wasu abubuwa kamar haka. ★ Allah yana ninka sakayyar alheri cikin ayyukan da suke na taimakon bayinsa. Misali, wanda yayewa wani bakin ciki Allah zai yaye masa nasa bakin cikin anan duniya da lahira. Wanda yaji qan wayanda suke kasa, wanda yake sama zaiji kansa. Wanda ya ciyar da wani shima Allah zai ciyar dashi tare da shigar dashi Aljanna. Wanda ya bawa wani dama ya rinqa tatsar nonon dabbarsa don yasha (koda akuyace) Allah zai shigar dashi Aljanna. Wanda ya dauke dutse daga kan hanya ko wani abu mai cutarwa, Allah zai shigar dashi Aljanna. ★ Allah ya jingina sababi

JAYAYYA DA ALFAHARI BA SHI NE ILMI BA

```MU KULA!```  Yawan surutu, yawan jayayya, yawan aibata malamai, ƙwaƙulo kura-kuran malamai, yawan hayaniya, yawan zuwa da wani abu wanda ya saɓawa wanda ake kai da kuma uwa uba tutiya da tinƙaho ba su ne alamun ilmi ba. Da a ce yawan jayayya da binciken aibin mutane shi ne ilmi da sahabbai sun fi kowa jayayya... Amma sai muka samu su ne mafi iya rufa asirin mutane da kuma kawar da kai daga jayayya. Ƙasa ba ta taɓa ɗaukar wani mutum mai kawar da kai da yiwa mutane uzuri sama da Annabi (S.A.W) ba. Kuma mun sani shi ne mafi cikar ilmi na addini da rayuwa. Don haka sai mu gane cewa addini ba hayaniya ko hauragiya ba ne, addini nutsuwa ne, sanin yakamata da kuma tarbiyya. Wannan kuwa shi mu ke kira ilmi. Abu Umar Alkanawy.

Next Generation!

Next Generation! .....Overloaded traveling car moving on the road loaded with huge amount of goods..... Not as usual, today its only three children are running after the ramshackle overloaded old car. They are shouting while running saying a word "Kiyaye!". An old driver who manage to share his seat with an additional passenger managed and threw three pieces of sweets to the three children. As they are doing frequently..... To my astonishment, children started fighting, strongers want to take either all three sweets or two, and the latter, the weakest one trying to make every effort to survive with one......... Think about it my people. These are our next generation. We really need to do our utmost to save the next generation..... What is your suggestion? Let us share ideas! Naseeb Auwal Abu umar Alkanawy!

MANYAN GOBE.... CI GABA KO CI BAYA?

..... Akwalar motar ta sukwano akan lalatacciyar fasashshiyar kwalta mai ramuka a dama da hauni wayanda yanayin damuna yasa suke cike da gurbataccen ruwa wanda ya jirkita sakamakon cakuduwa da ruwan toshashshiyar kwatar da shara ta toshe gami da tare hanyar da ruwa ya dace yabi..... Motar, an mata lodi da kaya wayanda sunfi karfinta.... Kujerun baya an ciresu an cakudasu da kayan da akai lodinsu, mazauninsu shima an makare shi da wasu kayayyakin, kan motar kuwa gani zakai kamar gashin wata mata mai wadatar gashi yayinda ta tsefeshi ta barshi a tsaitsaye... Wasu gungun yara da suke aikace-aikace a gefen titin wasu suna wanke yalo, dabino, goba wasu kuma mangwaro, suna ganin wannan motar ta sukwano da yawansu suka bar aikin da suke suka tsaye a gefen kwaltar suna fadin "Kiyaye..."   Direban motar wanda yake takure matuka saboda su biyune a kujerar tasa ya murtuke fuska gami da yiwa yaran muzurai....  "Kiyaye..." Wasu yaran suka kuma firtawa suna biye da motar da gudu