Posts

Showing posts from June, 2018

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU. Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. 👉🏼Lokacin da akace musulmi ana nufin wani mutum wanda ya mika wuyansa ga Allah, ya hakura da son zuciyarsa, kuma ya zabi yayi rayuwa yadda musulunchi ya tsara masa. 👉🏼Idan akace Musulunchi, to wani addinine wanda bai bar komai ba saida yayi magana akansa, tun daga kan bautar Allah har zuwa shiga bandaki, cin abinci, kallon madubi, taje kai da kuma yanayin tsarin kwalliya. 👉🏼In kuwa hakane musulmi yana da kyau ya zama musulmi, kuma yana da kyau ya zama mai bin koyarwa addinin musulunchin. Bana mantawa da wani umarni da ubangiji ya bayar cewa _A shiga musulunchi gaba daya, kada abi hanyoyin shaidan_. Wato dukkanin tsarin rayuwa ya zama yadda Allah ya tsara bisa koyarwar sunnar masoyi (S.A.W) ba tare da an karkace anbi hanyar shaidanu ba. 👉🏼A watan azumi ana kokari mutuka wajen bauta, da kuma komawa ga Allah, saidai kuma azumi yana wucewa sai wasu abubuwan sun kunno kai wayanda suke nuna cewa mutane lamb

RAMADAN SERIES

RAMADAN SERIES 01. "Mai gida ka tashi lokacin sahur fa yayi.... Ragowar abinda ya rage bai wuce minti 15 ba...." Maryam ta fada lokacin da kokarin ficewa dauke da abinci. Umar ya mike zaune, yana mai furta addu'ar tashi daga bacci. Bayan nan yayi maza ya fice daga daga dakin. A gaggauce ya wanke bakinsa gami da daura alwala dama kuma fitowarsa daga wanke kenan bacci ya dauke shi. Yana gamawa ya nufo dakin da suke ya zauna don cin abincin sahur tare dasu. "Hanan, Humaira da Aliyu ina yaya Usman?" Mai gida umar ya fada lokacin dayayi turus a bakin kofar dakin. "Yace shi bazai sahur ba yau", Hanan ta bada amsa. Wadda dama ita take biyewa Usman wanda yake da kimanin shekaru 20, sai ita da take da 17 sai kuma Humaira kanwarta mai shekaru 12 biye da ita kuma dan autansu ne Aliyu mai shekaru 8. Tana gama furta hakan dattijo Umar ya juya ya nufi dakin Usman ya taso shi. Bayan sun hallara dukkansu, sai Dattijon arziki umar ya fara da cewa.... "An