Posts

Showing posts from September, 2021

TARKON SHAIDAN

Tarkon Shaidan 1 SHIMFIDA Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci su tabbata ga shugaba jagaba (S.A.W), da ɗalibansa kuma abokanan rayuwarsa (Sahabbai) da kuma mafiya tsarkin iyali a doron ƙasa (Ahlul baiti). Bayan haka.  Lokacin da ubangiji (S.W.A) ya halicci Annabi Adam tare da Nana Hauwa'u kuma ya sanyasu a cikin Aljanna, da Shaiɗan yaso ɓatar da su, bai zo musu kai tsaye da sunan mai ɓatarwa ba, hasalima ce musu yayi "Haƙiƙa ni a gareku mai yin nasiha ne..." baya ga rantsuwa da ya yi musu ya kuma ƙawata umarninsa da  wasu abubuwa da suke so duk don ya ɓatar da su... Kuma ya samu nasara. Mu tuna lokacin Annabi Nuhu da mutanensa, tabbas Shaiɗan bai ɓatar da su ba sai da ya yi amfani da tarkonsa ta hanyar nuna musu cewa lallai su akan gaskiya suke kuma shi wanda aka turo ɗin bashi da girman da za a turoshi zuwa garesu. Duba Annabi Yunus, shi ma Shaiɗan bai hanashi yaɗa da'awarsa ba, amma sai ya ɗana masa tarkon fushi, inda ya fusata mutuƙa lokacin da m