Posts

Showing posts from July, 2020

Kwarafshan

Kwarafshan!  Menene kwarafshan? Kwarafshan shine lokacin da wannan yarinyar take bawa iyayenta kudi saboda suyi gum da bakinsu su zuba mata ido ta kula kowane kowane banza. Kwarafshan shine wannan saurayin da zaije yayita yiwa budurwa karyar kudi kawai don cinwa wata manufa tasa ta banza. Kwarafshan shine lokaci da kace "eh" sukace "a'a". Suka biyaka kudi don kace " a'a", kuma ka karba kabi hanyarsu ta banza. Kwarafshan shine lokacin da shugaban kasar nan ya bada sunan wani a matsayin minista, su kuma yan majalisa suka nemi wanda aka bada sunan nasa daya basu kudi indai yana so su tabbatar dashi... Shikuma saboda son abin duniya ya basu kudin shima ya zama mutumin banza. Kwarafshan shine lokacin da wannan Dan sanda ya karbi kudi a hannun mai laifi kuma ya sakeshi. Kwarafshan shine lokacin da dalibai suka biya wannan malamin kudi don jarrabawarsu tayi kyau. Kwarafshan shine lokacin da aka baka kudi ranar zabe kuma ka zabi mutumin da bai chanchanta b

SHALL I GIVE UP?

Naturally, animals are in love with their habitat; where they inhabit. It is habitat that gives them good chance and provides a favorable conditions to play their roles in a perfect way. A fish likes water, man likes good land, certain worm choose to be under earth beneath stone or something else and a better feeling of bird is flying on the air from one place to another. Let us move to non-living things, a cloud remains in the sky, while a mountains are always attach to the sand or earth. Why all this? It is because nature provides a good habitat for them to inhabit, and this gave birth to the love they (animals) have for their habitats. What if the the habitat is not good for them...... Will they lose their love for it? Let us imagine fish living in a hot water or a man on a land of fire... Will they still love habitat like this which threatens their lives? What if the habitat is country and leading class and elders refused to make it better place for you to live.  ★I am a Nigerian!

HANKALI BABBAN MA'AUNI

Wasu sukace hankali shi ne marabar mutum da dabba... Ni kuwa nace: Shin dabbar da take bambance abinci da guba ba ta da hankali? Ko kuwa dabbar da take sadaukar da rayuwarta don tsare ƙananun ƴaƴanta ba ta da hankali? Ko kuwa dabbar da take gina gida ta zauna itama babta da hankali? Idan hankali shi ne marabar mutum da dabba shin ta ya ya zamu gane haka? Hankali shi ne abin da yake zama banbanchi tsakanin mai hankali da mara hankali, rashin hankali mataki-mataki ne kamar yadda shima hankalin mataki mataki ne. Shin mutum nawa ka sani waƴanda suke daukar cewa sune mafiya cikar hankali a cikin al'umma yayin da gama garin mutane suke musu kallon cewa su ɗin mahaukata ne? Ko kasan Neanderthals; wasu mutane da akai shekaru aru-aru kafin zuwanmu duniya? Indai aka tambayeka su din suna da hankali ko basu dabshi me zaka bayar a matsayin amsa, in suna da shi menene bambancinsu da dabbobi? Tabbas hankali yana iya zama banbancin mutum da dabba amma idan ya cakuɗu da abubuwa guda biyu. Addini d

MUMMUNAR RAYUWA

Mummunar rayuwa itace rayuwar da ake yinta cikin rashin samun abincin da zai gina jiki, da ruwan dazai kori kishirwa, da muhallin da mutum zai rufawa kansa asiri, da ilmin da zai tafiyar da rayuwarsa dashi.... Mafi munin rayuwa kuma itace rayuwar da akayita ba tare da ciyar da zuciya abincin imani ba, ba tare da suturce zuciyar da jiki daga sharri ba, ba tare da koyi da magabata ba, ba tare da sani da karantar zamanin da mutum yake rayuwa a cikinsa ba. Tabbas muna cikin rayuwa mafi muni, muna cikin duhun da bama iya hangen abinda ke gabanmu, ga fitilu a hannunmu amma mun kasa kunnasu domin ana kunnasu ne da zuciya, mu kuwa zukatan namu sunyi nauyi, ko mun kunna tofa chajin imanin da yake cikin zukatanmu baida wani haske na azo a gani dazai haska mana abinda zai wadatar damu. Zukatan sunyi tsatsar da wankesu da fitar da tsatsar abune da zai dauki lokaci mai tsayi abune gagararre saida a gurin Allah madaukakin sarki. Babban tashin hankalin shine muna cikin kungurmin daji mai cike da ramu