HANKALI BABBAN MA'AUNI

Wasu sukace hankali shi ne marabar mutum da dabba... Ni kuwa nace: Shin dabbar da take bambance abinci da guba ba ta da hankali?
Ko kuwa dabbar da take sadaukar da rayuwarta don tsare ƙananun ƴaƴanta ba ta da hankali?
Ko kuwa dabbar da take gina gida ta zauna itama babta da hankali?
Idan hankali shi ne marabar mutum da dabba shin ta ya ya zamu gane haka?

Hankali shi ne abin da yake zama banbanchi tsakanin mai hankali da mara hankali, rashin hankali mataki-mataki ne kamar yadda shima hankalin mataki mataki ne. Shin mutum nawa ka sani waƴanda suke daukar cewa sune mafiya cikar hankali a cikin al'umma yayin da gama garin mutane suke musu kallon cewa su ɗin mahaukata ne?

Ko kasan Neanderthals; wasu mutane da akai shekaru aru-aru kafin zuwanmu duniya? Indai aka tambayeka su din suna da hankali ko basu dabshi me zaka bayar a matsayin amsa, in suna da shi menene bambancinsu da dabbobi?

Tabbas hankali yana iya zama banbancin mutum da dabba amma idan ya cakuɗu da abubuwa guda biyu. Addini da Al'ada. 

Kenan mutum mara addini da al'ada babu laifi idan ka jinginashi a sahun dabbobi domin bai samu banbancin da ake buƙata ba don cikarshi a matsayin mutum dan'adam.

Mutane da dama sun kauce hanya saboda tunaninsu na ganin cewa hankali kaɗai zai iyayi musu jagoranchi a rayuwa ba tare da addini ba, mafiya ɓatan mutane kuwa su ne wayanda suke tsammanin shi kansa addinin da hankali zasu jagoranceshi. Don haka zaka samesu shari'a tazo da wani abu sai suce ba haka ya kamata ba, a ƙoƙarinsu na kowawa Allah gyara a hukunce-hukuncensa da siffofinsa. Mafi munin ɓata kuwa sune wayanda bayan jifa da addinin da sukai sai kuma suke tunanin cewa hankali zai shirya tsarin rayuwar da ya dace da halittu fiye da abin da addini ya zo da shi.

Hankali kamar haske ne, shi kuma addini kamar idanu ne. Ka kula ka gani, komai hasken ɗaki indai mutum ba shi da ido hasken zai zamo na banza domin babu abin da zai gani. Hakanan idan mutum yanada ido kuma akace babu haske shima wannan hansken babu abin da zai amfana masa. Don haka nema a addini akace ba a karɓar aikin mahaukaci mara hankali har sai ya warke, domin a wannan misalin yana da ido amma babu haske a tare da shi don haka ga idon amma a cikin duhu zai yi ta sagarabtu...

MENENE MAHANGAR ADDINI GAME DA HANKALI
An rawato daga Nana Aisha take cewa ....
قد أفلح من جعل الله له عقلا.
Ma'ana; Hakika wanda Allah ya bawa hankali ya rabauta.
 Zammul hawaa (8)
Hankalin wanne? Babu makawa ana nufin wanda ya cakuɗa da addini.

Ibn Abbas yana ba da labari cewa an haifarwa Kisra yaro sai aka kirawo wani masani aka tambayeshi cewa wane abu ne mafi alkhairi da za a bawa wannan yaro?
Sai yace "A haifeshi tare da hankali"
Raudatul muhibbeen (8).

Ibn Qayyim yake cewa wani sashe na ma'abota ilmi suna cewa ".... Lokacin da Allah ya saukar da Annabi Adam zuwa ƙasa, sai Jibreel yazo masa da abubuwa guda uku.
1. Addini
2. Ilmi
3. Hankali.
Sai akace masa Allah yace masa a cikin abubuwa ukun ya zaɓi ɗaya. Sai Annabi Adam (A.S) yace "Ya jibreel, ban taba ganin abubuwa masu kyau kamar wayannan ba sai a aljanna. Sai ya kai hannunsa ya ɗauki hankali, sai ya sanyashi a jikinsa sannan yacewa ragowar biyun ku tafi sama. Sai sukace masa "ai mu an umarcemu mu kasance tare da hankali a duk inda yake. Sai duka ukun suka kasance ga Adam".
Aqlu wa fadluh (26)

A karkashin wannan zamu gane cewa idan mutum yana da ingantaccen hankali to dole za a sameshi da addini da kuma ilmi. Idan akace ilmi ba wai ana nufin zurfin ilmi a addini ko wani fanni ba, ana nufin ilmin rayuwa da sanin yadda za'a magance matsalolin rayuwa.

Wahab Ibn Munbah yake cewa "Na karanta a sashen abin da Allah ya saukar cewa, hakika shaiɗan ba ya tarar da wani abu mai wahala kamar mumini mai hankali..."
Hilyatul auliya (4/26)

Saboda mumini mai hankali ba zallar bautar kawai yake ba, ba kuma karatun ne zalla da shi ba. Kamar yadda magabatanmu suke faɗa mana akwai bambanchi tsakanin Ilmi da Karatu.

Hassan yake cewa "Addinin mutum ba ya cika har sai hankalinsa ya cika"
Raudatul muhibbeen (9)

Addinin kansa ba ya karɓar aikin mara hankali har sai hankali ya dawo gareshi.

An tambayi Abdullahi bn Mubarak, menene mafi falalar abin da za a baiwa bawa bayan musulunchi?
Sai yace "Kaifin hankali"

Nace (Abu Umar): 
"Hankali shi ne abin da ya dace da shari'ar Allah da kuma sanin abubuwa a yadda suke tare da yin ayyuka a yadda suke.... Hakan kuwa ba ya samuwa sai da shiryarwar nassi.... Don haka ne zaka ga cewa BABU HANKALI GA MARA ADDINI. 

Abu Umar Alkanawy!

Comments

  1. Allah ya kara basira da Jagoranci. Allah ya bamu ikon kiyaye hankalin da ya bamu ta hanyar riko da Addinin Allah da kuma Kyawawan Al-adunmu.

    Mungode Mal. Naseeb

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.