Posts

Showing posts with the label Jan hankali

Maraba da Ramadan

Image
Kowane bawa yana da kyau da Allah ya nuna masa wannan lokaci na zagayowar watan alfarma. Wata ne wanda ake daukaka darajar bayin Allah. Wata ne wanda ake 'yanta bayin Allah. Wata ne wanda ake bude kofofin rahamar Allah. Wata ne wanda ake kulle kofofin wuta. Wata ne da ake ibadar da babu wanda yasan sakamakonta sai Allah. Wata ne wanda bayi suke sadaukar da jin dadinsu don farantawa mahaliccinsu. Wata ne wanda mahalicci yake sakawa bayi don samuwar jin dadinsu. Wata ne wanda nutsuwa take mamaye zukatan muminai. Wata ne wanda aka saukar da qur'ani. Wata ne wanda a cikinsa ake samun lailaitul qadari. Muna godiya ga Allah ga wannan falala.

KARATU YANADA DADI.

Tabbas duk lokacin dana samu littafi mai kyau, mai ingantaccen bayani, wanda bayanin ya cakuda da ingantaccen hankali kuma yake fitar da wani sako wanda yake da girma da kuma samarwa da kwakwalwa bayanai masu gamsarwa, tare da daukarta ya kaita wata duniya mai tattare da wasu bayanai wayanda bata san da su ba, nakanji cewa inama ace duniya bazata tashi ba. Nakanji cewa inama ace duhu bazai shammaceni ba ta yanda zanga tabbas lokaci ya tafi harma in shirya rufe abin karatun don shiga wata harkar dabam....... Mafi kyawun littafi da shiryarwa shine littafin Allah....... Mafi kyawun dunkulallen bayani wanda masu sharhi basa iya fitar da zunzurutun fa'idarsa shine hadisin manzon Allah (S.A.W).... Mafi kyawun abinda ababen halitta suka rubuta, shine rubutun da aka yishi da salo ko goyon bayan abinda ya gabata daga na farko da na biyun....... Mafi munin rubutu kuma shine wanda yaci karo da wayannan biyun ko ince ukun in an kaara dana ukun. Naseeb Abu Umar Alkanawy.

Babban Sako.

BABBAN SAKO. Musulmai da dama a cikin kaso 99% na Qur'ani suna amfana ne da iyakar 1%.  Wayannan ina maganar musulmai masu karantashi ne bawai masu ajiye shi sai jefi-jefi ba. Da dama suna karanta Qur'anine don samun lada kawai sun manta da cewa. Yana maganin bakin ciki. Yana kawar da damuwa ga mai damuwa. Yana yalwata arziki. Yana haska zuciya. Yana karfafa fahimta. Yana sanya kwarin zuciya da tabbatuwa. Yana kawo _firaasa_. Yana zama sababi na amsa buqatu. Yana bada kariya daga cututtukan cikin jiki, kama daga kan na sassan jiki har zuwa na wasu organs na jiki. Yana bada kariya daga cutukan da suke a zuciya irinsu hassada, kyashi, kishi mara amfani da sauransu. Yana saka hangen nesa. Yana kawar da son duniya. Yana saka karfin gani da karfin sauran sassa kamar hakora, ji, da sauransu. Kai mutum kamar ni bai isa ya fadi kashi 3% daga 100% na amfanin Qur'ani ba. A takaice zan iya cewa Qur'ani kamar ruwa ne, wasu suna amfani dashi wajen sha ne kawai. Wa...

Tasirin fina-finai da littafai a rayuwarmu.

*Tasirin fina-finai da littafai a rayuwar mu*. Naseeb Auwal Abu Umar Alkanawy. Abinda kake tunani, da abinda kwakwalwarka take hange da kuma tsarin rayuwarka duk suna chanjawa sanadiyyar abubuwa da dama da suke faruwa. Mafi girman abinda yake sauya tunani kai tsaye ko kuma ta bayan fage shine kallon fina-finai da kuma karanta littafai.... Lokacin daka lizimchi karanta littafai masu kyau da manufa to tabbas zaka tsinci rayuwarka tana zama mai kyau da samun ingantacciyar manufa. Don haka ne zaka samu babu littafin dayake shiryarwa irin wanda aka saukar daga sama. Hakanan yadda kake karanta littafai marasa kyau, marasa manufa ko masu wani mummunan sako a kunshe a ciki a hankali zai sauyaka zuwa wannan yanayin. Don haka ne zaka samu mata masu kallon fina-finai da karanta littafai marasa kan gado basa wadatuwa da abinda mijinsu zai musu domin tuni zuciyarsu tayi gaba akwai tunanin irin mijin da take, don haka maimakon ta gode akan wani abin saikaga ta raina. Ita yadda taji ance mijin...

MU FARKA YAN NIGERIA

Bugun zuciyar yana tafiya da sauri tamkar karar kofaton ingarman doki lokacin dayake sharara gudu a dandaryar kasa, yayinda ruwa ya taso daga cikin ido ya cike saman idon wanda hakan ya bada damar ganin komai dishi-dishi.... Kafin daga bisani ruwan ya rikede ya zama hawaye sakamakon satatowa da zaiyi ya wanke wadataccen filin fuskar...... A zahiri kenan, a badini kuwa bakin ciki cike yake da zuciya wanda sanin ciwon kai da kishin al'umma su suka haifar da wannan bakin ciki.... Ba imani, ba kudi, ba ilmi, ba tarbiyya, ba shugabanchi, ba tausayi, ba jinkai, ba...ba...ba........ Abin da yawa, bawai babu su bane gaba daya, akwai su amma sunyi karanchi... Wanda wani sashen ma babu wasu gaba daya. Ta yaya al'ummar da jahilanta suke mulkarta zataci gaba? Ta yaya al'ummar da manyanta basa tausayawa kanana, kuma kananan basa girmama na gaba zataci gaba? Tayaya rashin tsaro, rashin tsari, rashin tarbiyya, rashin imani, rashin ilmi zasu cakuda basu haifar da abinda yake barazana ...