MU FARKA YAN NIGERIA

Bugun zuciyar yana tafiya da sauri tamkar karar kofaton ingarman doki lokacin dayake sharara gudu a dandaryar kasa, yayinda ruwa ya taso daga cikin ido ya cike saman idon wanda hakan ya bada damar ganin komai dishi-dishi.... Kafin daga bisani ruwan ya rikede ya zama hawaye sakamakon satatowa da zaiyi ya wanke wadataccen filin fuskar......
A zahiri kenan, a badini kuwa bakin ciki cike yake da zuciya wanda sanin ciwon kai da kishin al'umma su suka haifar da wannan bakin ciki....

Ba imani, ba kudi, ba ilmi, ba tarbiyya, ba shugabanchi, ba tausayi, ba jinkai, ba...ba...ba........ Abin da yawa, bawai babu su bane gaba daya, akwai su amma sunyi karanchi... Wanda wani sashen ma babu wasu gaba daya.

Ta yaya al'ummar da jahilanta suke mulkarta zataci gaba?
Ta yaya al'ummar da manyanta basa tausayawa kanana, kuma kananan basa girmama na gaba zataci gaba?
Tayaya rashin tsaro, rashin tsari, rashin tarbiyya, rashin imani, rashin ilmi zasu cakuda basu haifar da abinda yake barazana ga al'umma ba?

Kayi tunani, ka kuma ji cewa zaka kawo gyara. Duk abinda wani yayi zaka iya fiye da hka.

Sign
Naseeb Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.