Posts

Showing posts from March, 2018

Babban Sako.

BABBAN SAKO. Musulmai da dama a cikin kaso 99% na Qur'ani suna amfana ne da iyakar 1%.  Wayannan ina maganar musulmai masu karantashi ne bawai masu ajiye shi sai jefi-jefi ba. Da dama suna karanta Qur'anine don samun lada kawai sun manta da cewa. Yana maganin bakin ciki. Yana kawar da damuwa ga mai damuwa. Yana yalwata arziki. Yana haska zuciya. Yana karfafa fahimta. Yana sanya kwarin zuciya da tabbatuwa. Yana kawo _firaasa_. Yana zama sababi na amsa buqatu. Yana bada kariya daga cututtukan cikin jiki, kama daga kan na sassan jiki har zuwa na wasu organs na jiki. Yana bada kariya daga cutukan da suke a zuciya irinsu hassada, kyashi, kishi mara amfani da sauransu. Yana saka hangen nesa. Yana kawar da son duniya. Yana saka karfin gani da karfin sauran sassa kamar hakora, ji, da sauransu. Kai mutum kamar ni bai isa ya fadi kashi 3% daga 100% na amfanin Qur'ani ba. A takaice zan iya cewa Qur'ani kamar ruwa ne, wasu suna amfani dashi wajen sha ne kawai. Wa

Tasirin fina-finai da littafai a rayuwarmu.

*Tasirin fina-finai da littafai a rayuwar mu*. Naseeb Auwal Abu Umar Alkanawy. Abinda kake tunani, da abinda kwakwalwarka take hange da kuma tsarin rayuwarka duk suna chanjawa sanadiyyar abubuwa da dama da suke faruwa. Mafi girman abinda yake sauya tunani kai tsaye ko kuma ta bayan fage shine kallon fina-finai da kuma karanta littafai.... Lokacin daka lizimchi karanta littafai masu kyau da manufa to tabbas zaka tsinci rayuwarka tana zama mai kyau da samun ingantacciyar manufa. Don haka ne zaka samu babu littafin dayake shiryarwa irin wanda aka saukar daga sama. Hakanan yadda kake karanta littafai marasa kyau, marasa manufa ko masu wani mummunan sako a kunshe a ciki a hankali zai sauyaka zuwa wannan yanayin. Don haka ne zaka samu mata masu kallon fina-finai da karanta littafai marasa kan gado basa wadatuwa da abinda mijinsu zai musu domin tuni zuciyarsu tayi gaba akwai tunanin irin mijin da take, don haka maimakon ta gode akan wani abin saikaga ta raina. Ita yadda taji ance mijin