KASATA NIGERIA
Shekaru lambobi ne kawai, aikin da akai a cikinsu shi yake mayar da shekarun su zama ababen sha'awa ko ababen kyamata... Ko kana iya tuno wata shekara da wani abin burgewa ko sha'awa ya faru? Idan ka tuno me kake ji? Hakanan ko kana iya tuno wani lokaci da kayi wani abin kunya, abin kyamata ko haushi? Idan ka tuno me kake ji? Wannan kadai ya isa ya tabbatar maka da cewa shekaru, watanni da kwanaki lambobi ne kawai, kuma aikin da aka aiwatar cikin wayannan lambobi shine abin dubawa ba yawan lambobin ba. Wani lokacin zai iya zama abin kunya ace ga tarin shekaru amma babu wani abin amfani a cikinsu, abin kunyar yana karuwa idan akace bayan shekarun akwai damammaki na amfanar shekarun amma ba'ai amfani da wayannan damammakin ba. Kasata Nigeria! Alfarma ta sanya ma'aikatan da zasu cicciba kasar zuwa ga tudun tsira mafi yawansu nakasassu ne, domin ba nagarta ake dubawa ba, alfarma ake dubawa. Cin hanci da rashawa sun saka ayyukan alheri sunki aiwatuwa a wannan k...