Posts

Showing posts from December, 2020

WAIWAYE ADON TAFIYA (26 - 30)

WAIWAYE ADON TAFIYA (26) Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W) Yanayin yanda sahabbai suka ga Annabi ya basu umarni, da kuma yadda suka ga bai damu da cewa da yawansu su fita ba sai sukayi tsammanin ba yaki za'a gwabza ba. Don haka adadin musulman yayi karanchi sosai. Domin kuwa wayanda suke da dabbobi amma a nesa Annabi bai basu umarni suje su dauko ba, hasalima da sukai niyyar su dauko dakatar dasu yayi bai kuma tsaya jiransu ba yayi gaba tare da sauran sahabbai.  A karshe Annabi ya fita da sahabbai adadin Dari uku da goma sha uku (313). Cikinsu mutum dari biyu da arba'in da yan kai duka mutanen madina ne, wato Ansarawa, ragowar kuwa mutanen Makkah ne ma'abota hijira wato muhajirai.   (Nurul Yakeen 89) Kasancewar Abu sufyan masanin hanya, bayan ya turawa kafiran Makkah abinda ke gab da faruwa na tare ayarinsu da za'ai, saiya sauya hanya, kuma cikin sa'a sai ya kewaye wa su Annabi. Ganin ya tsira saiya tura da sako zuwa ga kafiran Makkah yana umartarsu dasu koma tun

WAIWAYE ADON TAFIYA (21 - 25)

WAIWAYE ADON TAFIYA 21 Tatacciyar sirar ma'aiki...  Kamar yadda muka ambata cewa mutanen madina sunata tururuwa da don su tari Annabin rahama (S.A.W) haka suka kasance tsawon kwanaki. Mun riga munji cewa mafi yawan mutanen madina sun musulunta tun kafin zuwan ma'aiki (S.A.W). Cikinsu harda wata uwa wadda ta musulunta kuma ta lakkanawa danta musulunchi, ana kiran wannan mata da Gumaisaa'u ko Rumaisaa'u. A wannan fita da ake tarar Annabi harda wannan dan nata dan shekara goma. Haka zai bi tawagar yara (kamar yadda ake fita tawaga-tawaga manya da yara...), wasu kuwa su rinka hawa dogayen gurare don dai su fara gano Annabin rahama... Kowace rana wannan yaro dan gidan Rumaisa haka yake fita amma haka zai dawo tare da yan uwansa yara yana mai mutukar bakin cikin rashin ganin abinda yake son gani wato Annabin rahama (S.A.W). Idanuwansa suna zubda hawayen rashin dacewa da ganin abin kaunarsa haka zai juyo zuwa gida... Shi kuwa can Annabin rahama ya yada zango a Quba, Ranar liti