ILMI KAFIN AURE.
Ilmi shine ginshikin ko jigon da yake jagorantar rayuwar mutane zuwa ga inda ya dace a lokacin da ya dace. Da ilmi ne al'umma take samun cigaba, hakanan da shine abokan adawa suke cin galaba akan kishiyarsu, da kuma shine din dai al'umma take samun kariya daga sharrin abokan adawarta. Ilmi nada mutuqar muhimmanci...... Idan muka juyo da idanuwanmu zuwa ga rayuwar mu a cikin gidajenmu, zamu ga cewa ilmi na taka muhimmiyar rawa wajen nuna mana yadda zamu tafiyar da rayuwarmu data abokan zamanmu..... Mu dauki rayuwar aure wadda a yanzu tana daga cikin manyan matsaloli anan kasar hausa, duba da yadda mace-macen aure yake kara yawaita da kuma rashin zaman lafiya. Wanda idan kayi nazari kayi bincike a karshe zaka tarar da cewa 90% na matsalolin ana samu ne saboda karancin ilmi, ragowar 10% dinma idan ka tsawaita yawatawa da tunaninka tofa zaka tabbatar da cewa rashin ilmin dai ba wani abuba. Kafin aure akwai abubuwa da dama daya kamata mutum ya sani dangane dashi auren, amma haka...