Posts

Showing posts from July, 2021

HANYAR TSIRA

1 A Gida babu aminchi, a Makaranta babu aminchi, akan hanya babu aminchi, a kasuwa, a Asibiti, a Tasha, a gurin taro, a masallachi..... ko inama babu aminchi. Duhu mai girma ya baibaye ko'ina hatta cikin zukatan mafi yawan mutane yayi bakikkirin, jinin dake gudana daga zuciyarmu zuwa sassan jikinsu yayi bakikkirin........... ganin idonmu yayi rauni bama iya banbace abubuwa masu kamanceceniya da wayanda basu da kamanceceniya.......  Menene ya janyo hakan duka? Ko shakka babu son zuciya ne ya kawo haka. Da za'a zuba tsaron duka duniyar nan, amma ya zamana zukata basu gyaru ba, to tabbas babu aminchi. Da za'a halicci rana guda goma a sararin samaniya don su haske duniya, to da tabbas za'aci gaba da rayuwa cikin duhu domin kuwa hasken dake cikin zukata shine haske bawai hasken dake waje ba...... Tarbiyya ta lalace, zina ta yawaita, sata, neman maza/mata, karya duk sun mamaye al'umma.😭 Da kanmu mun bude kofar rashin aminchi da tashin hankali kuma mun afka cikin birnin S

WAIWAYE ADON TAFIYA 46 - 50

WAIWAYE ADON TAFIYA (46 - 50) Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W) Annabi bai bar Da'if ba har saida yayi musu addu'ar shiriya. A wannan shekara ta takwas bayan Hijira aka haifawa Annabi santalelen yaro, Mariya ce ta haifeshi. Anas (R.A) wanda rainon Annabi ne yana bada labari cewa bayan an haifi Ibrahim (R.A), Annabi Muhammad ya fito ga sahabbai yake sanar dasu cewa, da daddare an haifa masa yaro kuma ya sanyawa yaron sunan Babansa Ibrahim (A.S).  Matan madina suka rinka tururuwa cewa suna son su shayar da wannan dan albarkar yaro suna masu neman albarka saboda mahaifiyar yaron tana da karanchin abinda zata shayar dashi. A karshe Annabi ya damka Ibrahim a hannun Ummu Saif. Wannan sahabin wanda ya samu tarbiyya a gidan manzon Allah wato Anas Bn Malik yake kara cewa bai taba ganin mutum mai so da jinkan iyalansa ba kamar manzon Allah, domin ya kasance yana yawaita shiga inda Ibrahim din yake ya daukeshi ya kuma sumbaceshi.  A shekara ta tara sai shugabanni suka rinka bijirowa su