HANYAR TSIRA

1

A Gida babu aminchi, a Makaranta babu aminchi, akan hanya babu aminchi, a kasuwa, a Asibiti, a Tasha, a gurin taro, a masallachi..... ko inama babu aminchi.

Duhu mai girma ya baibaye ko'ina hatta cikin zukatan mafi yawan mutane yayi bakikkirin, jinin dake gudana daga zuciyarmu zuwa sassan jikinsu yayi bakikkirin........... ganin idonmu yayi rauni bama iya banbace abubuwa masu kamanceceniya da wayanda basu da kamanceceniya....... 

Menene ya janyo hakan duka?
Ko shakka babu son zuciya ne ya kawo haka.

Da za'a zuba tsaron duka duniyar nan, amma ya zamana zukata basu gyaru ba, to tabbas babu aminchi.
Da za'a halicci rana guda goma a sararin samaniya don su haske duniya, to da tabbas za'aci gaba da rayuwa cikin duhu domin kuwa hasken dake cikin zukata shine haske bawai hasken dake waje ba......

Tarbiyya ta lalace, zina ta yawaita, sata, neman maza/mata, karya duk sun mamaye al'umma.😭

Da kanmu mun bude kofar rashin aminchi da tashin hankali kuma mun afka cikin birnin Sabon Allah tare da sauya tafiyar da magabata suka barmu akai......

A wannan rubutu zamu tattauna akan wani yanki na matsalolin da muka ambata musamman tarbiyya saboda itace da an sameta to tabbas komai zai daidaita.

2
Komai karfin ganin idanu ba zasu ga komai ba idan aka shiga cikin duhu, to kamar hakane komai taka-tsantsan din mutum akan tsaro ko bawa kansa da makusantansa kariya idan har bai nemi tallafi daga koyarwar musulunchi ba, tofa bazai taba samun nutsuwa ko aminchi ba. Domin kuwa tun farko ya kaucewa koyarwar addinin Allah.....

Idan har mutum ya yarda shi musulmi ne, to dole ya yarda da ajiye dukkanin buri, da biyewa dukkanin wata wayewa ko koyarwa face wadda ta dace da koyarwar addinin musulunchi.
_kace musu, Hakika ni sallata da yankana da rayuwata da mutuwata ga Allah suke Ubangijin talikai_.
Don haka rayuwa dukkaninta a wajen musulmi bautace, bawai a iyakar ramadan kawai ake musulunchi ba, ko kuma a iyakar cikin masallachi ba.

*Abin haushi shine wasu sun dauki ibadar tana farawane daga kabbarar harama zuwa sallamar idar da sallah*.....

Alhalin ita ibada tana farawane daga farkon rayuwa zuwa karshe domin Ibada itace _dukkanin abinda Allah yake so kuma ya yarda dashi_, idan a haka ne to dukkanin rayuwar musulmi ibada ce domin anaso musulmi ya rayu bisa abinda Allah yakeso kuma ya yarda dashi.

Yaya musulunchi ya bukaci musulmi ya tsara rayuwarsa?
Yaya alaqar maza da mata take a musulunche?
Menene tsarin rayuwar musulmi a rayuwarsa da wanda ba musulmi ba?
Menene ya janyo mana fadawa cikin halin da muke ciki?

Duka wayannan tambayoyi ne garemu musulmai.

Tarbiyya tana tabarbarewa ne tun gabanin auren iyayen yaro....

Ana warwareta tun daga shirye-shiryen bikin auren iyayen yaro.

Ana lalata tun kafin a dauki cikin yaro.

_Tayaya yaron da tun yana ciki yake jin maganganun shaidanu da ayyukansu bazai lalace ba?_
_Tayaya yaron da shaidanune suka karbi haihuwarsa, shaidanu suka raineshi, kuma shaidanu suka zama abokansa a gida, makaranta da sauran gurabe bazai zama shaidani ba?_

3
Idan ana lissafo abubuwan da suka taka muhimmiyar rawa wajen kaucewa hanya da tabarbarewar tarbiyya abinda za'a fara ambata shine yayewar hijabin dake tsakanin maza da mata..... Idan har ba'a lissafa yayewar hijabin a matakin farko ba, to na tabbata magana akan lalacewar tarbiyya bazata taba zama cikakkiya ba sai an ambaci yayewar hijabin dake tsakanin maza da mata.

Abin sanine cewa musulunchi addinine mai tsari, wanda a cikin tsarinsa yana bijiro da abubuwan da suke maslaha ga lafiya da kuma kariya ga imaninmu. Wanda yasan illolin da zina, shan giya da caca suke haifarwa bazai kokwanto akan abinda muka ambata ba.

Duk inda aka samu tarayya da cakuduwar maza da mata tabbas kasuwar shaidan tana ci a wannan waje.

Tasirin shaidan yana farawane tun daga lokacin da mutum ya kyallara ido ya hango mace. Domin shi kallo kamar yadda ma'aiki (S.A.W) ya siffantashi cewa yayi _Kallo mashi ne ko kibiya daga kibiyoyin shaidan_. 
(ko kamar yadda yace)

Shiyasa Annabin tsira (S.A.W) ya umarci daya daga cikin sahabbai cewa _Kada kabi kallo bayan kallon farko, domin kallon farko naka ne (an halatta maka), amma kallo na biyu ba naka bane_. 
(ko kamar yadda yace)

Sa'annan akwai Athar daya tabbata cewa Shaidan yana fadar cewa _Mace da namiji basa kebancewa a wani waje, face ya zama dan aike a tsakaninsu_.
Dan aike yana nufin yaje zuciyarta ya kimsa mata mugun abu, sannan yaje zuciyar namijin ya kimsa masa wani abu.... Idan tsoron Allah ya rinjayi abinda shaidan  din yake gaya musu saisu bijire masa, idan kuma Shaidan ya rinjayesu sai a aikata abinda bai kamata ba.
Muna neman tsarin Allah daga hakan.
Ameen

Akwai wata kunya da take tsakanin maza da mata wadda yanzu an wayi gari babu ita, anyi watsi da ita da sunan wayewa.
Uba zai tarar da yarsa tare da kato a kofar gidansa amma babu abinda ya dameshi.
Kai wata har tana iya budar baki ta furta cewa ai abokintane, lokacin da uban ya tambaya.

Akwai misalai da yawa wayanda da yawansu mun ambata ga wayanda suka leqa rubutunmu mai taken _Social media wanne_ gudun tsawaitawa bazai bamu damar ambatarsu ba.

Abin nema anan shine mafita. Da kuma jin tsarin da musulunchi ya shimfida cikin alaqar namiji da mace.

4
Waiwaye, masana kan kirashi da adon tafiya.
A baya kadan mun ambaci cewa sakacin iyaye shine yake sanya yaro ya fandare. Domin kuwa daga cikin abubuwan da suke taka muhimmiyar rawa wajen samar da dabi'un mutum akwai iyaye da kuma al'ummar daya taso a cikinsu. Shiyasa zakaji ana cewa maza su samarwa ya'yansu uwa ta gari. Kamar yadda suma matan zakaji ana cewa su samarwa ya'yansu uba na gari. Hadisai mabambanta akan wannan maudu'in tabbatattu sunada mutuqar yawa....... 

Saidai tare da hakan akwai qaddara, domin zaka samu akwai iyayenda sunbi duk hanyar data dace wajen tarbiyyar yaro, amma sai ubangiji ya jarrabesu da yaron kodai don ya gwada imaninsu ko don ya daukaka darajarsu ko kuma don ya kankare musu zunubansu. Don haka ba kowane yarone zai fandare ba ace laifin iyaye ne.

Hakanan kuma zaka iya samun wayanda iyayen ba mutanen kirki bane amma sai Allah ya fitar da ya'ya nagari daga jikinsu.

Mai karatu zai iya tuno wani yaro wanda abokin Annabi musa ya kashe, saboda iyayensa salihai ne shi kuma bai yiwo suba, a cikin suratul kahf. 
Mai karatu zai iya tuno Dan gidan Annabi Nuhu wanda ya bijirewa mahaifinsa.
Zai kuma iya tuno mahaifin Annabi Ibrahim da yake dora masa tallan gumaka.
Kai mai karatu anan unguwarku zaka iya tuno wasu iyaye salihai masu wani yaro kangararre.
Kema da kike tunanin kwarai kinsan wane dan gidan wance idan kika kara tunani to zaki tuno wasu iyaye masu sakaci amma sai suka samarda yaro mai addini.

Shin sanin hakan zaisa mu dauke hannayenmu daga yayanmu muce mun barwa Allah rainonsu da tarbiyyarsu?

A'a bazamuyi haka ba, abinda zamuyi shine muyi iyakar iyawarmu, sannan muyi addu'a. 

Idan muka ce zamu sakankance to munyi koyi da shaidan, wanda shima da akace ya gaishe da Annabi Adam, sai ya bijire. Amma daya tashi magana saiyace ai Allah ne ya batar dashi. 

*Ci gaba*
Alhamdulillah, Alaka tsakanin namiji da mace wadda ba muharrama ba, bamu santa ba saidai inda wata lalura ta sanya alaqar. Misali neman ilmi, harkar lafiya ko wanin haka.
Shima tare da taka tsan-tsan. Idan mai karatu yana tare damu munyi rubutu akan wannan maudu'in. Saidai zamu kara zakulo wasu abubuwan da yake da kyau mu ambacesu.

★. A musulunchi babu abota ko kawance tsakanin maza da mata, kamar yadda matasan yanzu suke aikatawa. 
Wanda social media ya taka muhimmiyar rawa a wannan fannin.
Dukkanin alaqar da babu amfanar da juna a cikinta to abar gudu ce, mafi muninta da hatsarinta kuwa shine alaqar jinsi biyu. 

5
Duk yadda mace takai ga kame kanta, da kuma nuna halin ko in kula ga samari saika samu cewa an samu masu kokarin kulla alaqa da ita, wanda mafiya yawansu ba don Allah suke sonta ba.

Wani abin haushi shine, akwai wanda shi burinsa shine samun mace nutsatstsiya, zaibi duk hanyoyin daya dace don kulla alaqa da ita daga bisani saiyayi gurbata tunaninta a karshe ya mai da ita mutuniyar banza irinsa..... komai nutsuwarta indai zata saurareshi yau da gobe da jibi to shikenan an gama......

Don haka yan'uwa mata bayan dagewa da tarbiyyar kai saikin hada da addu'a.... domin mumini bashi da makamin daya wuce addu'a. 

Shin kina so a kanki a tozarta mahaifanki ranar alqiyama? Ko kuwa kina so a karramasu saboda ke ranar alqiyama?
Dukkanin mutum nagari zaiso a karrama magabatansa... in kuwa hakane to hanya mafi sauki ta samo musu wannan karramawar shine ki tayasu kula da tarbiyyarki.

Sau nawa kawarki wance take ikirarin bata da abinda zata sakawa iyayenta dashi, alhalin ga babbar dama tanada ita na tsayawa tsayin daka da tayasu kula akan tarbiyyarta?

Sau nawa kike tunanin wata bajinta da iyayenki sukai miki har kika zubar da kwalla saboda tsananin soyayyar da suka nuna miki? Shin basu chanchanchi kiyi abinda za'a karramasu ba ranar gobe qiyama?

Sau nawa kike nuna bacin ranki akan an taba mutuncin iyayenki? Shin lalata tarbiyyarki ba shine mafi cin mutuncinsu ba?

Tabbas sakamakon kyakkyawa, kyakykyawane.

★       ★        ★
Allah ya kawo mu wani zamani wanda hatta muharraman ma ba ababen amincewa bane.

Allah ya jiqan Sheikh Muhammad Hassaan na misra ba don ya mutu ba, a cikin littafinsa *Amraadul Umma*, yake cewa "Wallahi bazai iya zama da kaya na shan iska ba (shimi da gajeran wando) a inda akwai yayana manya da kanana... ballantana har in iya fita da su waje.........."

Shin munada irin wannan kunyar? 
Masu irinta kadan ne.

6
Har yanzu ina tuna wata magana ta larabawa, wadda suka ce, "Kayiwa kanka riga-kafi (katanga ko shinge ko wata kariya) daga mutane ta hanyar munana musu zato...." a lokacin dana fara cin karo da maganar sai naga rashin dacewarta domin munana zato ga mutane baki daya ba abune mai kyau ba. 
Saidai yanzu ina daf da yarda da wannan maganar saboda abinda nake ji, nake gani da kuma wayanda suka riskeni daga hanyoyi mabambanta.

Lalacewar tarbiyya zuciyoyinmu har ya kai ga cewar mutum yana iya cin amanar wanda ya amince masa... bafa amana muke magana ta kudi ba... ba kuma amanar mutuntaka ba, ba kuma amanar kadara ba. A'a dukkaninsu kananu ne idan ka kwatanta su da cin amanar iyalan wanda ya amince maka.

Irin wannan cin amana itace irin alaqar nan da take gudana tsakanin almajirin gida da yaran gida mata, yara ne ko kuwa sun kai a kirasu da yammata.... Inda zaka iske yana kebewa dasu yana musu wasu wasanni wayanda babu kunya ko tarbiyya a ciki, wani ma yakanyi kokarin wuce inda kake tunani... Domin koda yaushe abu yana gaba ne, kamar wucewar kwanaki.

Irin wannan cin amana itace dai wadda take wakana a makarantun boko kama daga kan kananu har zuwa jami'a inda zaka iske dalibai a tsakaninsu suna cin amanar iyayensu.... babu kunya babu tsoron Allah.

Irin dai wannan cin amana itace dai wadda malamai a makarantu suke amfani da maluntarsu su ci amanar iyayen yaran da suka kawo yaransu makarantunsu... musamman makarantu na gaba da sakandire...

Kada fa kayi tunanin a makarantu na kasa da sakandiren hakan baya faruwa, suma hakan yana faruwa sosai. Wani abin bakin ciki shine har a makarantun islamiyya ana samun wannan matsalar....
Wanda ya rayu jiya da yau, ya kuma ji labaran da suke yawo jiya da yau bazai musun wannan bayani ba.

Kai bari ma, kanin mahaifi ko kanin mahaifiya yana cin amanar wansa ko yayarsa..... 

"Mallam muharramata ce, babarta yayatace."
A cewar wani matashi da muka hau abin hawa tare dashi.
"Don muharramarka ce kuma sai akace kuyi irin wannan wasannin? Yanzu ko matarka ce akan idon mutane ai bazaka aikata hakan ba....... Sannan kuma ka sani duk abinda kayi akwai masu rubutawa, idan kaje saika gayawa Allah cewar ai muharramarka ce... ko kuma ke ki ari bakinsa ki gayawa Allahn haka...." kwatankwacin wannan amsar na bashi. 
Jikin macen ne ya fara sanyi, tayi istigfari sannan ta daure fuska tace masa "karka qara taba ni....." nasan dai yaji haushi kamar ya cilloni waje daga abin hawan amma sai yaga na fishi auki😊

Irin wannan cin amanar fa lokaci ya kawomu da tana faruwa tsakanin uba da yarsa.
Ko mutum da kanwar matarsa.
Ko mata da kanin mijinta ko abokinsa ko yaronsa a kasuwa ko wajen aiki.

Ina zamusa kanmu? Shin ba dole muyita ganin bala'i kala kala ba? 
Allah dai ya kyauta.

Ina tuno wata amsa da Annabi (S.A.W) ya bawa sahabbai lokacin da yake magana akan hana mutane shiga gidajen masu aure... sai suka ce ya ma'aikin Allah yanzu kamar kanin miji fa?
Sai manzon Allah (S.A.W) yace "KANIN MIJI MUTUWA NE".... kenan kanin miji yafi kowa hatsari.

To idan abinda yasa aka fadi hakan akansa yanzu yazo kan kawunnai (uncles) kinga suma zamuce sunfi kowa hatsari kenan.

Koda yaushe muna kokarin gayawa mutane ba duka aka taru aka zama daya ba.

Wannan tunatarwa ce, wanda yaga dama saiya riki hanya izuwa ubangijinsa.......

7
Driver daka amince ka sakar masa yayanka ya rinka kaisu makaranta yana dawowa dasu shi kansa ba abin amincewa bane dari bisa dari... domin abin ya kazanta.

Wata wutar sha'awace take damun mutane yanzu wanda saika rasa menene ya janyota....

Shin mutanen da suka rayu shekaru aru-aru baya basu da irin wannan sha'awar?
Ko kuwa sunada ita sun fimu kunya ne kawai?
Ko kuwa muma munada kunyar, jin labarin wannan yayi wancan yayi, anyi a unguwa kaza, a gidan radio kaza an ambaci wani ma yayi.... da wanin haka sune suka sanya nauyin abin ya ragu a idanunmu?
Ko kuwa kallon fina-finai marasa fa'ida shine ya haifar mana da hakan?
Ko kuwa wasu littafai da muke karantawa ne, suke rage mana nauyin abin a zukatanmu?
Ko kuma imaninmu ne yayi karanchi?

Babu wanda idan ka dauka bazai zamo hujja ba cikin tambayoyin sama, dama wasu tambayoyin.... wasunsu sunyi nauyi bazasu ambatu ba, wasunsu kuma gudun tsawaitawa yasa na ajiye su.....

Mai karatu nasan ya tuno wata matsala da bamu ambata ba, matsalar da take faruwa tsakanin maza da mata a yau. Musamman matasa.

"Nasan haramun ne" a cewar wata yammata, "nasan haramun ne.... saidai ina sonsa" ta kammala maganarta kanta a kasa alamun tana jin kunya.
_Lallai wannan soyayya ta isa tunda har zaki iya halatta jikinki gareshi gobe kiyama kuma wata ta tsarkake inda ya taba....._.

"Ustazu you are out of date", a cewar wani gaye zuwa ga abokinsa, "Indai bazakai yadda na gaya maka ba duk wadda kaje kasaka za'ayi........"
_Idan har sai mun kauce hanya (Romancing, shan minti koma dai da wanne suna aka kirashi duk daya ne) sannan zamuyi soyayya to bama bukatarta_.......

Madallah da matashi da matashiyar da suka yarda da cewa su musulmai ne, suka hakura da biyewa shaidan.... har zuwa lokacin aurensu, ko kuma rabuwarsu idan Allah bai kaddara musu auren ba.

JAN KUNNE.....
Komai kankatar abu komai girmansa ana rubutashi a littafinka ko littafinki kuma za'a bijiro dashi a gaban kowa ranar Alkiyama.....

Shin bama jin kunyar abokan arziki suga abinda muka aikata?
Shin bama jin kunyar iyaye suga abinda muka aikata?
Shin bama jin kunyar Masoyinmu Annabin rahama (S.A.W) yaga abinda muka aikata......?
Shin baza muji tamkar mu nutse ba yayinda Allah ya tambayi Annabi (S.A.W) akan shin ya gaya mana wannan aiki haramun ne koba haramun bane?
Zaka iya dago kai ku hada ido da manzon tsira a wannan lokaci?

Shin bama jin kunyar Allah, wanda yake kallonmu a inda muke kebewa muna aikata ba dai dai ba?

Allah muke roko daya yafe mana zunubanmu.
Ya Allah mun zalunchi kawunanmu, idan baka yafe mana ba, kuma baka ji kanmu ba, tabbas zamu zamo a cikin tababbu masu asara....

Anan muke kawo karshen wannan rubutu.
Allah yasa muyi aiki da abinda muka karanta, abinda mukayi kuskure Allah ya yafe mana.
Sai kuma a wani rubutun dabam.

Rubutawa
Naseeb Auwal 
Abu Umar Alkanawy 
Da
Shifaa Khamis Adam
S.K.A Samha

Comments

Popular posts from this blog

MUTUM DA HANKALI

EYE OPENER... (SIWES)

LIKITAN ZUCIYA...