Posts

Showing posts from September, 2020

DAMISAR TAKARDA...

Image
Da Sunan Allah mai rahama mai jin kai. Mafi girman abinda yake kara daraja da kimar mutum a rayuwa shine ilmi, gwargwadon darajar abinda mutum ya ilmantu akansa gwargwadon kimarsa da darajarsa. Don haka ne zaka iske mafi darajar mutane sune Annabawa, domin sunfi kowa ilmi, kuma ilminsu shine mafi darajar ilmummuka. Tabbas ilmi yana da darajar da duk wahalar da akasha akan nemansa ko kuma duk dukiyar da aka salwantar dominsa ba'ayi asara ba. Saina tuno kissoshin da muka karanta da kuma wayanda muka ji labari na irin dawainiya da wahalhalun da magabatan wannan al'umma suka sha a wajen neman ilmi, wannan ya hada da tafiye-tafiye da wahalhalu mabambanta. Kissoshi masu taba zukata, masu cike da almara, ababen tausayi da kuma dimbin darussa. Kissoshin suka sakani cikin wani yanayi na tsananin mamaki, saidai mamakin yana kaucewa idan na tuno da girma da darajar abinda suke nema wato ilmi. Idan muka kewayo wannan zamanin, wanda muke rayuwa a ciki. Za muga tabbas akwai gagar