Posts

Showing posts from October, 2021

ALFAWA'ID 1

ALFAWA'ID   Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, tsira da amincin Allah su tabbata ga zaɓaɓɓe fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).  Wannan wasu taƙaitattun bayanai ne ko kuma tunatarwa da na tsarasu don ƙaruwarmu baki ɗaya. Allah subhanahu wata'ala ya sanyamu mu amfani da abinda zamu karanta, ya kuma yafe mana kura-kuren da suke ciki. Kamar sauran rubuce-rubucen mu, wannan ma muna bada damar za'a iya yaɗawa yan'uwa domin shi aikin umarni da hani yana kan kowa da kowa. Allah nake roƙo daya sanya mu cikin bayinsa tsarkaka ma'abota Aljanna maɗaukakiya. Kuma shi nake roƙo daya karɓi wannan aiki namu. Haƙika shi mai karamchi ne mai kuma afuwa. SAƁANIN AL'UMMA Wasu matasa biyu sunyi sabani, har ta kaisu ga tada jijiyar wuya...  Sai wani dattijo yazo ya riskesu, ya tambaya ko akan me suke tada jijiyar wuya. Saina farkonsu yace, ce masa nayi mutanen duniya dukansu batattu ne, shiryayye shine wanda yabi shiriyar Allah da manzonSa (S.A.W)." Na biyun kuma sai y