Posts

Showing posts from June, 2021

TABARBAREWAR ILMIN ZAMANI... INA MAFITA?

Ga wanda yake rayuwa cikin mutane, kuma yake cudanyuwa da yan makaranta, kuma yake zantawa dasu akan yanda karatukansu suke gudana, nasan ba zai jayayya ba idan nace tabbas ilmin zamani da hanyoyin samunsa suna cikin tsaka mai wuya. Musamman a arewacin Nigeria. Makarantu nawa ne suke gudanuwa ba tare da malamai ba...? Wata sananniyar makarantar gwabnati kwanaki haka dalibanta yan SS1 suka zo min, lokacin suna gab da barin ajin, suka sanar dani cewa basu da malamin biology tun farkon shigarsu SS1. Suka ce dani da can wani dan bautar kasa ne yake koyar dasu, tunda ya tafi kuwa basu da wani tsayayyen malami. Yaran sune wayanda ake tunanin sune masu son karatu a ajin. Amma idan kaji basic abubuwa na biology da basu sani ba sai abin ya daure maka kai. Abin mamakin shine su wayannan yaran ba zasu iya gina maka jimloli masu kyau na turanchi ba, ballantana azo maganar biology, physics, chemistry ko uwa uba mathematics.  Ka gaya min don me zamu ji mamakin idan yaran nan sun kasa cin jarrabawa?

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

Image
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Hadisi yazo daga Mu'adh bn Anas, wanda imam Ahmad ya rawaitoshi da kuma Imam Tirmidhi (514) cewa "Annabi ya hana zaman Ihtiba'i (zaman hade gwiwa da hannu kamar yadda yake a hoton sama) yayinda liman yake huduba." Zaman ihtiba'i shi ne mutum ya haɗe ƙaurinsa da cinyarsa a zaune sannan ya kewaye su da hannayensa.  Wannan hadisi Imam Albaniy da wasu daga masu tahƙiƙin musnad sun ingantashi. Imam Nawawiy kuma da Ibnul Arabi sun da'ifanta hadisin tare da wasu malamai. (Tahzeeb Attahzeeb 4/258) Sai dai an samu cewa wasu daga cikin sahabbai sun yi irin wannan zama, yayin da liman yake tsaka da huɗuba, cikinsu akwai Abdullahi Bn Umar da Anas Bn Malik Allah ya ƙara yarda da su. Ibn Qudama cikin littafin Mugniy na sa, ya nuna babu laifi idan anyi wannan zama, harma ya nuna wannan itace fahimtar Ibn Musayyib, Hasanul Basariy, Ibn Sirin, Imam Malik da kuma Shafi'i da sauransu. Allah yayi musu rahama baki ɗaya. Ibn Qud

IDAN 'BERA DA SATA...

Da sunan Allah mai jin kai.  Duk lokacin da akace tarbiyya to ana maganar rayuwa ne baki daya, domin tarbiyya ke kawo kwanciyar hankali, zaman lafiya, albarka da abubuwa da dama na morewa zaman duniya. Mutane nawa ne suke da dukiya amma babu kwanciyar hankali ba kuma sa jin dadin dukiyar domin rashin aminchi da fargaba sun dabaibayesu?  Idan ka fahimchi wannan saika gane me muke nufi da morewa zaman duniya.  Idan muka karkato da tunaninmu zuwa ga rayuwar yara masu tasowa tabbas duk mai kula hankalinsa zai tashi. Bari mu kasa yaran gida uku don bayanin yafi fitowa fili. Kashi na farko, sune yaran da suke da gata kuma iyayensu suke kokari wajen basu kyakkyawan ilmi na zamani. Zaka iske irin wayannan yara suna tasowa da tsananin tsabagen rashin tarbiyya da wani tunani na babu wanda ya isa ya ja dasu ko kuma kaga suna jin cewa babu wanda ya isa ya taka su.... To ai sunada kudi sunsan indai a wannan kasar ne indai kanada kudi to sai yanda kayi da hukuma. Irin wayannan yara zaka iske basa gi