TABARBAREWAR ILMIN ZAMANI... INA MAFITA?

Ga wanda yake rayuwa cikin mutane, kuma yake cudanyuwa da yan makaranta, kuma yake zantawa dasu akan yanda karatukansu suke gudana, nasan ba zai jayayya ba idan nace tabbas ilmin zamani da hanyoyin samunsa suna cikin tsaka mai wuya. Musamman a arewacin Nigeria.


Makarantu nawa ne suke gudanuwa ba tare da malamai ba...?

Wata sananniyar makarantar gwabnati kwanaki haka dalibanta yan SS1 suka zo min, lokacin suna gab da barin ajin, suka sanar dani cewa basu da malamin biology tun farkon shigarsu SS1. Suka ce dani da can wani dan bautar kasa ne yake koyar dasu, tunda ya tafi kuwa basu da wani tsayayyen malami. Yaran sune wayanda ake tunanin sune masu son karatu a ajin. Amma idan kaji basic abubuwa na biology da basu sani ba sai abin ya daure maka kai.

Abin mamakin shine su wayannan yaran ba zasu iya gina maka jimloli masu kyau na turanchi ba, ballantana azo maganar biology, physics, chemistry ko uwa uba mathematics. 
Ka gaya min don me zamu ji mamakin idan yaran nan sun kasa cin jarrabawa?

Gwabnati tayi watsi da ilmi, ace yanzu ankai matakin da indai kana son danka ko yarka tayi karatu saidai ka sanyasu a makarantun kudi, ko kuma ka kokarta kayi gwagwarmaya ka samar musu guri a daidaikun makarantun da suke da sauran kima ta fuskar ilmi... Ba don gudun tsawaitawa ba dana fadada wannan gabar...

Wani zaice to ai bawai iyakar yaran talakawa ne suka fadi jarrabawar ba... 
Tabbas, saidai suma yara masu gatan kusan koda yaushe hankalinsu yana kan wayoyin hannu da fina-finai... To waima wa yake maganar yaran da amsa musu waec ko neco ake?

Idan nayi rantsuwa bazan kaffara ba cewar littafin da ake rabawa na jamb din kansa kaso saba'in cikin dari na masu zana jarrabawar jamb basu karanta shi ba. Amma zai wahala sati ya zagaya basu kalli fina finai ba...

Tabbas idan ba'a farga ba ilmi zai durkushewar da tasoshi abune mai mutukar wahala.

kwanaki takardar wasu dalibai tazo hannuna don inyi musu marking, abin haushin shine wasu harda hausa suke gwamutsa bayanin da ake nema. Yayinda wasunsu suke amfani da turanci irin wanda suke yi a chat "nyc, olryt, gud..." da sauransu.

Tun daga tushe an banzatar da ilmin ne, banzatar da ilmi tun daga hanyar da ake bi wajen daukar malaman. Wani hanya ce dashi, wani kuma siyar offer din yayi. Don haka saika iske an jibga bahagon malamai alhalin ga wayanda suka cancanta sunata yawo a gari daga wannan guri zuwa wancan. 

Wani kwanaki haka yake sanar dani cewa shi malami ne, amma malaman da suke koyarwa tare da su duk yayan manya ne, kuma saima sunga dama suke zuwa... Kuma babu damar ayi musu magana domin sunsan manya...

Ta yaya ilmi ba zai gurbace ba?

Tabbas mun kai lokacin daya kamata kodai muyi kokari ta karfin tsiya da dimokradiyya ta bamu muyi kokari mu tura wakilanmu a siyasance don kawo gyara. Ko kuma mu musan yadda zamuyi mu hada kai da kai mu taimaki juna.

Ina mafita?

Naseeb Auwal

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.