Posts

Showing posts from May, 2018

Maraba da Ramadan

Image
Kowane bawa yana da kyau da Allah ya nuna masa wannan lokaci na zagayowar watan alfarma. Wata ne wanda ake daukaka darajar bayin Allah. Wata ne wanda ake 'yanta bayin Allah. Wata ne wanda ake bude kofofin rahamar Allah. Wata ne wanda ake kulle kofofin wuta. Wata ne da ake ibadar da babu wanda yasan sakamakonta sai Allah. Wata ne wanda bayi suke sadaukar da jin dadinsu don farantawa mahaliccinsu. Wata ne wanda mahalicci yake sakawa bayi don samuwar jin dadinsu. Wata ne wanda nutsuwa take mamaye zukatan muminai. Wata ne wanda aka saukar da qur'ani. Wata ne wanda a cikinsa ake samun lailaitul qadari. Muna godiya ga Allah ga wannan falala.

KARATU YANADA DADI.

Tabbas duk lokacin dana samu littafi mai kyau, mai ingantaccen bayani, wanda bayanin ya cakuda da ingantaccen hankali kuma yake fitar da wani sako wanda yake da girma da kuma samarwa da kwakwalwa bayanai masu gamsarwa, tare da daukarta ya kaita wata duniya mai tattare da wasu bayanai wayanda bata san da su ba, nakanji cewa inama ace duniya bazata tashi ba. Nakanji cewa inama ace duhu bazai shammaceni ba ta yanda zanga tabbas lokaci ya tafi harma in shirya rufe abin karatun don shiga wata harkar dabam....... Mafi kyawun littafi da shiryarwa shine littafin Allah....... Mafi kyawun dunkulallen bayani wanda masu sharhi basa iya fitar da zunzurutun fa'idarsa shine hadisin manzon Allah (S.A.W).... Mafi kyawun abinda ababen halitta suka rubuta, shine rubutun da aka yishi da salo ko goyon bayan abinda ya gabata daga na farko da na biyun....... Mafi munin rubutu kuma shine wanda yaci karo da wayannan biyun ko ince ukun in an kaara dana ukun. Naseeb Abu Umar Alkanawy.