Posts

Showing posts from June, 2022

MUTUM DA HANKALI

Image
Mutane da Hankali 01 Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaba, Ja gaba, tare Ahalinsa da Sahabbansa.  Hankali shi ne mafi girman abin da Allah ya bawa ɗan Adam, ba wai don bai bawa sauran halittu shi ba, sai don yanda ɗan Adam yake amfani da hankalin na sa ya sha bambam da yanda sauran halittu suke amfani da na su hankalin. Hakan kuma ya samo asali ne saboda shi tunanin ɗan Adam yana samun jagoranci ne daga shari'a wadda Allah ya aiko manzanni da ita, don haka sai ɗan Adam ya zamana yayi fintinkau a ɓangaren kowace ɗabi'a mutuƙar.  Wani zai ce ai tun kafin a saukar da Shari'a mutum ya ke da hankali, sai mu ce, Allah da ya halicci Annabi Adam, ya halicceshi ne akan fiɗira, kuma haka aka ɗorawa Annabi Adam nauyin ɗora ƴaƴansa akan wannan tafarki wanda aka ɗorashi a kai.  Allah Mai Girma da Ɗaukaka ya na cewa: كَانَ النَّاسُ أُمَّةً وَاحِدَةً فَبَعَثَ اللَّهُ النَّبِيِّينَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ الْكِ