Posts

Showing posts with the label Aure

Matan Aure a Musulunci: Hakki, Daraja da Kyakkyawar Mu’amala.

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. Kowanne abu ba cikakke ba ne, duk halittar da Allah ya yi babu kamar mutum, amma shi kansa mutum tara yake bai cika goma ba, a dabi'ance, lafiyance da addinance. To haka idan ka duba abubuwan da suke kewaye da mu, masu rai da marasa rai za ka iske kowanne yana da bangaren da ya cika yana da kuma bangaren da ya ke da tawaya. ALLAH Buwayi Gagara Misali shi kadai ne cikakke, kuma gwargwardon kusancin bawa zuwa ga Allah gwargwadon cikarsa, kimarsa da darajarsa. Shi yasa Annabin Rahama ﷺ ya fi kowa zama cikakke domin ya fi kowa kyakykyawar alaka da Allah Mai Girma. Idan muka dauki ayyuka da kuma tsarin rayuwa za mu iske cewa cike take da kalu-bale mai yawa, kuma cike take da misalai ga masu hankali na irin hanyoyin da ta bi ta dilmiyyar game da hallakar da wayanda suka daukaka sha'aninta, kamar kuma za mu ga ba ta bar na kirkin ba, domin kuwa kowa akwai irin matsalolin da ya yi fama da su, kuma ya ke fama da su, kuma zai yi fama da su a nan gab...

AUREN DOLE.

Image
Wannan takaitacciyar fadakarwa ce a kan auren dole, hukuncinsa a addini da kuma shawarwari... Mun tattara bayanan ne don amfanuwar al'umma baki daya. Aikin da mukai na dai-dai daga Allah ne, wanda mukayi na kuskure kuma dama mu yayan Adam ne, muna rokon Allah da ya gafarta mana. Ya kuma sanya rubutun ya zama mai amfamarwa ne ga daukacin yan'uwa musulmi. Dan uwanku. Abu Umar Alkanawy Da yar'uwarku Shifaa Khamis Adam AUREN DOLE  Tabbas soyayya jigo ce mai girma a zamantakewar auratayya. Shi yasa Allah da kansa yake cewa... "Yana daga cikin ayoyinSa ne, ya halitta muku matan aure daga rayukanku, domin ku nutsu zuwa gareta, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani." Rum:21 Hakanan Annabin rahama yake fada cewa "Banga abin da ya fi dacewa da masoya biyu ba sama da suyi aure". Wannan hadisi ne shahararre wanda matasa da dama suke amfani da shi, kuma lalle yana nuna darajar aure da matsayinsa...