Posts

Showing posts with the label Hausanovel

SHUGABANCHI 3

Umar ya nufi waje daga cikin gidan yana rike da takardar da mahaifiyarsa ta bashi. Soron cike yake da kashin dabbobi wayanda suke kiwatawa, tare da cewa kullum sai an share soron amma hakan bai hana kasar wajen cakuduwa da fitsari gami da kashin dabbobin ba, sanadiyyar haka yasa zakaji yanayin soron wani iri. Ya sanya hannunsa ya jawo kofar gidan wadda take a sakaye, duk tayi tsatsa. Tayi wata kara gami da tirjewa, amma sai gogan naka ya sanya karfi ya fincikota, karfin jan dayayi mata ya sanya kofar ta sallama ta budu tare da cewa tana tirjewa game da kartar kasa tamkar bata son motsawar. Ya kalli layin nasu wanda yake cike da ledoji barkatai, dududu fadin layin ko keke napep bazai iya shigowa ba. Tsakiyar layin kuma wata kwata ce wadda gurbataccen ruwa ya dankare ya tsaya a cikinta, a haka yaci gaba da tafiya kansa a kasa daga bisani ya samu guri kebantacce a gefen layin inda aka ajiye wani kututture, ya zauna akai. Ya kalli dama da hauni, yaga babu kowa inka dauke tatta...

SHUGABANCHI 2

Tun bayan fitowar matashi Umar daga dakin jarrabawar yake ta sake-sake a zuciyarsa gami da tunanin makomar wannan jarrabawa tasa, amma abinda yafi damunsa shine dubu dayar da aka karba daga hannunsa. “Idan naje gida me zan cewa Baba, tunda dai da ita suka dogara a matsayin cefanen gobe.” saurayin ya fada yana mai zurfafa tunani akan mafita. Duk da wasu daga yan'uwansa masu zana jarrabawa suna ta iface-iface domin kuwa yaune ranar kammala jarrabawar, yayinda wasu masu adadin shekaru basa wannan iface-iface, wasunsu ma tuni sun bar harabar makarantar... Tabbas wayanda suke baki a wajen zana wannan jarrabawar sunfi kowa murna da hauka gami da wauta. “Gaskiya ka burgeni da naga ka ware gefe ba'a wannan shirmen da kai,” wani mutum wanda yake da kimanin shekara 35 ya fada lokacin da yake mikowa matashi Umar hannu. Murmushi kawai umar yayi gami da amsa sallamar wannan mutumin. “Nifa wannan shine zana jarrabawata ta shida, kuma abu daya kawai nake nema. "Maths...

SHUGABANCHI 1

                          SHUGABANCHI .... Sabuwar hanya na bi , don wayar da kan al'umma akan halin da suke ciki a rayuwar yau . Na tsara bayanin nawa ta sigar labari ta yadda yan'uwa zasu karantashi cikin nishadi da kuma walwala . Ina fatan hakan bazaisa yan'uwa su kasa gane darussan da yake dauke da su ba .                           **         **          ** Farko Duk da iskar da take kadawa mai karfi hakan bai hana mutane fuskantar inda suka saka gaba ba. Mafi yawansu zaka iske cewa matasa ne kuma an zana kalmar FUSHI a fuskokinsu.... Suna tafe wasu basa ko magana yayinda zakaga wasu suna musayar magananganu a tsakaninsu.....

RAMADAN SERIES

RAMADAN SERIES 01. "Mai gida ka tashi lokacin sahur fa yayi.... Ragowar abinda ya rage bai wuce minti 15 ba...." Maryam ta fada lokacin da kokarin ficewa dauke da abinci. Umar ya mike zaune, yana mai furta addu'ar tashi daga bacci. Bayan nan yayi maza ya fice daga daga dakin. A gaggauce ya wanke bakinsa gami da daura alwala dama kuma fitowarsa daga wanke kenan bacci ya dauke shi. Yana gamawa ya nufo dakin da suke ya zauna don cin abincin sahur tare dasu. "Hanan, Humaira da Aliyu ina yaya Usman?" Mai gida umar ya fada lokacin dayayi turus a bakin kofar dakin. "Yace shi bazai sahur ba yau", Hanan ta bada amsa. Wadda dama ita take biyewa Usman wanda yake da kimanin shekaru 20, sai ita da take da 17 sai kuma Humaira kanwarta mai shekaru 12 biye da ita kuma dan autansu ne Aliyu mai shekaru 8. Tana gama furta hakan dattijo Umar ya juya ya nufi dakin Usman ya taso shi. Bayan sun hallara dukkansu, sai Dattijon arziki umar ya fara da cewa.... "An...