RAMADAN SERIES

RAMADAN SERIES 01.

"Mai gida ka tashi lokacin sahur fa yayi.... Ragowar abinda ya rage bai wuce minti 15 ba...."
Maryam ta fada lokacin da kokarin ficewa dauke da abinci.

Umar ya mike zaune, yana mai furta addu'ar tashi daga bacci. Bayan nan yayi maza ya fice daga daga dakin.
A gaggauce ya wanke bakinsa gami da daura alwala dama kuma fitowarsa daga wanke kenan bacci ya dauke shi. Yana gamawa ya nufo dakin da suke ya zauna don cin abincin sahur tare dasu.

"Hanan, Humaira da Aliyu ina yaya Usman?"
Mai gida umar ya fada lokacin dayayi turus a bakin kofar dakin.

"Yace shi bazai sahur ba yau", Hanan ta bada amsa.
Wadda dama ita take biyewa Usman wanda yake da kimanin shekaru 20, sai ita da take da 17 sai kuma Humaira kanwarta mai shekaru 12 biye da ita kuma dan autansu ne Aliyu mai shekaru 8.

Tana gama furta hakan dattijo Umar ya juya ya nufi dakin Usman ya taso shi. Bayan sun hallara dukkansu, sai Dattijon arziki umar ya fara da cewa....
"Annabin rahama yana cewa: Bambancin da yake tsakanin azuminmu dana Ahlil kitabi shine cin abincin sahur". Nasa'i da Abu dawoud sun rawaito hadisin.
Yaci gaba da cewa "A wani hadisin na Bukhari, Muslim da Abu dawoud kuma cewa ma'aiki (S.A.W) yayi: Kuyi sahur hakika a cikinsa akwai albarka".
Ya juyar da kallonsa zuwa ga Yaya Usman daga bisani yace "Kaida kake gudun sahur to kaji albarka kake gujewa".

Bayan sun kammala sahur sunyi shirin sallah sai suka fice masallachi inda suka bar matan a gida.

Masallacin ya cika makil, sabanin yadda suka saba gani, domin ko rabin masallacin ba'a cikawa, amma abin mamaki suda suke samun sahun gaba yau sune a sahu na biyun karshe.

Bayan anyi sallah an idar liman ya danyi tunatarwa akan ayyukan da ake son aiwatarwa a azumin ramadana na daga karatun kur'ani, sallolin nafila, tsayuwar dare, istigfari da kuma ciyarwa musamman ga wayanda basu da karfi.

Bayan sun saurara sun kuma yi abinda ya samu na daga azkar sai suka fito daga masallacin lokacin kuwa gari ya fara haske.

"Baba wai mutane sunfi tsoron Allah ne da azumi? Dubi fa yadda masallacin nan ya cika...."
Aliyu ya tambaya yana mai karyar da kansa yana kallon mahaifin nasa tare da rike kugunsa da hannayensa biyu yana mai tsayawa a gaban baban nasa.

Dattijo umar ya sunkuyo kasa ya daidaita kansa dana dan nasa, sannan yace: "Tabbas da watan ramadan mutane sunfi zagewa su bautawa Allah, domin neman kusanci ga Allah da kuma marmarin ibada a wannan wata...."

Aliyu yayi jigum daga bisani yace: "Tab di jam, to tunda sun san Allah wanda ake bautawa a ramadan shine a sauran watan nin meyasa bazasu nemi kusanchi ga Allah a kowane wata ba? Sannan idan har suna son Allah da gaske ai a kowane wata zasu rinqa marmarin munajaati da Allah abin sonsu ko? Basa tsoron kuma Allah ya kamasu da laifin cewa suna sane suke kin zuwa sallar asuba a sauran watannin? Ko kuma suna tunani......"
Yaya Usman ya katse kaninsa Aliyu ta hanyar harararsa....

Aliyu yayi tsit daga baya yace "Baba idan babu yan sa ido a wajen ma tattauna ko?".

Dattijo umar ya kyalkyale da dariya yace "Karamin dana ka fiye surutu...

Daga nan suka wuce gida.

RAMADAN SERIES 02

Gaf da lokacin buda baki dattijo umar ya fito daga gidansa hankalinsa a tashe, yanata faman waige waige......

"lafiya?" wasu matasa suka fadi hakan lokacin da suke sassarfa don zuwa wajen dattijo umar.

"Aliyu nake nema, tun azahar ya fito kaga yanzu ana shirye-shiryen shan ruwa bai dawo ba..... Babban abin tashin hankalin ba'asan inda ya tafi ba, mun kuma tura hanan ta nemo mana shi itama kajita shiru kamar an aiki bawa garinsu....."
Dattito umar yayi shiru lokacin da yake yake faman leke-leke ko zai hango dansa a wani wajen.... Yaje ya durkusa ya leka karkashin motarsa baiga komai ba, ya tafi bakin kwata ya leka karkashin silaf nan ma baiga komai ba, ya nufi wata nannadaddiyar tabarma ya warwareta namma dai ba Aliyu...

"Haba dai ya haj, ya za'ai ya shiga cikin kwata ko tabarma?"
Wani cikin matasan ya fada lokacin da yake yiwa mallam gajeriyar dariya.

Mallam ya tsaya kikam yace "Na firgice ne wallahi, kaga kuwa idan na ganshi yau jikinsa ya gaya masa don ya bata min rai wallahi... Kuma baima tambaya ba ya fice fa...."

"Amma mallam ko mu zamu shaidi yaron cewa baya yawo, koma yana ina, to tabbas yana amintaccen waje insha Allah".
Wani cikin matasan ya fada.

Kamar daga sama sai sukaji muryar Aliyu yayi musu sallama yana murmushi.

Kafin su ankara tuni dattijo umar ya daga hannunsa sama rankwashi kan Aliyu.... Ji kake Qussss...

Aliyu saboda karfin rankwashin saida ya durkusa bisa gwiwoyinsa, amma bayan wannan baiyi ko gezau ba sai kawai ya sunkuwar  da kansa kasa  yayinda hawaye yake zubowa daga idanunsa....

Shi kansa mallam baiji dadi ba, domin yayi hannun riga da koyarwar Annabi na cewa "kada dayanku yayi lokacin da yake cikin fushi". Amma sai yayi ta maza yace "Mallam ina ka tafi tun dazu aketa nemanka?, duk ka tayarwa da mutane hankali...."

Aliyu ya fara magana cikin murya mai ban tausayi da shashshekar kuka yace "Naje masallaci nayi sallar azahar saina zauna karatu nufina idan na kamo yaya hanan sai in dawo..... To..to...to shine fa har akai la'asar ban kamo taba, sai kuma aka fara tafsiri shine na tsaya na saurara... Tofa ma shine malamin yake fadar falalar ciyarwa da kyautatawa mabuqata ni kuma sainayi maka kwadayin wannan ladan, shine mafa na tashi naje gidansu abokina hafizu don inga ko sun chanchanta.........."
Daga nan karfin kukan ya hanashi qarasawa.

Dattijo umar ya sunkoyo da kansa ya rungume dansa, yace "Aliyuna kayi hakuri idan zaka wani waje ka rinqa sanar dani, shima mallam sai hawaye ya biyo kumatunsa yana mai gangarowa zuwa gemunsa.........

Wani a cikin matasan da suke tsaye yace "Allahu Akbar, kunga dansa yayi mishi laifi ya fusata shi, amma kuma da kansa ya yafewa dan nasa, hasalima laifin saiya zamo kamar karin dakon soyayya a tsakaninsu... Tofa wannan shine misalin Allah da bayinsa, koda yaushe yana maraba da masu kaifin da suka tuba.

"Aliyuna, Meka gani a gidansu hafizu?"
"Babu komai".
Aliyu ya bada amsa gami da jan hannun mahaifinsa yana mai cewa cikin kasa-kasa da murya "Baba, bana son fadar sirrinsu ne a gaban jama'a, amma suna buqatar taimako, domin kuwa babu kayan abinci sai dai naga babansu ya shigo da wani abu a leda...."

"Ya isa haka" dattijo umar ya fada. Yaci gaba da cewa "Nace maka ka daina yawan surutu, idan aka tambayeka abu ka fadi iyakar abinda ake bukatar ji...."

"To ai baba kaine ka tambayeni, kuma ma aiban gaya maka abin cikin bakar ledar ba, sannan ban gaya maka hayaniya ta shiga tsakanin iyayen ba akan rashin kawo abin shan ruwan da wuri ba...shine fa na faki ido na fito... Inaji suna ce......"

Dattijo umar ya toshe bakin Aliyu yana mai dan dukansa a hankali a baya yace "My pikin ka ciki surutu kamar mallam jatau....."

Suka nufi gida suna masu gaggawa don gaggauta shan ruwa.

RAMADAN SERIES 03

Bayan dattijo umar da dan karamin dansa Aliyu sun shiga gida sai suka zauna suka ci dabino gami da korawa da abinnan mai dan dumi, bayan nan sai suka je masallachi suka gabatar da sallar magriba.

Kamar yadda muka sani shi agogo koda yaushe juyawa yake baya tsayawa, koda kuwa wani ya tsaya saboda matsalar rashin abincinsa to zaka iske wani dabam yana juyawa. Cikin lokaci kadan sai gashi har anyi sallar isha'i anyi taraweeh.

"Muje ka rakani gidansu hafizu".
Dattijo umar yake bawa dansa umarni, lokacin da suke fitowa daga masallachi.

Ba musu kuwa suka nufi hanyar gidansu hafizu.

**     **      **       **

Mahaifin hafizu wato gambo ya dawo daga sallah yana tafe amma zuciyarsa tana ta tunanin  abinda zai tarar a gida, shikam bai da abinda zasu ci shida iyalansa yau....

Bayan ya shiga yayi sallama sai matarsa Asabe tazo ta tsaya a kansa kikam tace "Kai mallam nifa na gaji da wannan azabtarwa da kake mana... Ka tashi ka nemo mana abincin sahur..... Ya za'ayi ace jiya kace babu yauma kace babu? Ai Allah yana tare da mai nema... Amma kullum saika zo gida ka wani mike kafa kana baza hanci kana jiran a kawo na sadaka tsabar mutuwar zuciya....."

"Haba umma", wata yarta yayar hafizu ta katse mahaifiyartata sannan taci gaba da cewa "Wallahi baba yana kokari, kinsan dai kawai kowa akwai jarrabawar da Allah yake masa......"

"Rufe min baki" Asabe ta fada cikin fada, "ai nasan shi kike so dama bani ba mara kunya kawai shashasha...."

Yar tata kawai saita daga hannu tana mai rokon Allah "Ya Allah kaine gatanmu, gareka muke kai kukanmu, ya ubangiji mai azirtawa ka azirtamu, ya Allah ka yaye mana wannan kunci da muke ciki....." kuka ya sarketa amma sai taci gaba da cewa; "Ya Allah saboda tsoronka muka kaucewa sata da alfasha, ya ubangiji yadda muka rufe rashin samunmu ya Allah ka wadatamu, ya Allah kada kasa zuciyarmu ta kekashi ta yadda zamu bijire maka...."

Sai kawai asabe mahaifiyarta tazo ta rungumeta tana cewa "Ameen 'yata, hakika nima fushi ne yasa nake furta wayannan kalamai akan mahaifinki, ya Allah ka dubemu duban rahama.... Allah ka yafe min...."

"Assalam Alaikum wai ana sallama da mallam gambo".
Wani Almajiri ya shigo yana furta hakan.

"jeka kace bana nan", mallam gambo ya fada a tunaninsa wayanda suke binsa bashi ne.

"Kananan kuma wallahi saika je", matar ta fada tana mai rike kugunta.

"To babata", gambo ya fada lokacin da yake kokarin fita don amsa kiran.

Jim kadan bayan fitarsa sai gashi ya shigo gidan da yan dako dauke da buhun shinkafa, katan din taliya da macaroni, dankali, da wasu kwalaye da ledoji dauke da kaya shadda kala biyu da atamfa kala biyu....

"Allah..... Allah.... Ni mema zance maka ne?.."
Ya fada yana mai fashewa da kuka.

Matarsa cikin mamaki ta tambaya "Mai gida wannan daga ina?"

"wallahi wani bayan Allah ne tare da wani karamin yaro suka kawo min banma gane suba don basu bari sun shigo haske yadda zan gane suba....... Dana rasa mai zan basu tukuici sai kawai na cire takalmina ina mikawa yaron.... Amma basu karba ba....."
Ya sake fashewa da kuka.

Yayar hafizu ta dago daga sujjadar godiya da tayi daga nan tace "Wayannan bayi ne a cikin bayin Allah, suka tausaya mana akan halin da muke cike anan duniya kuma suka taimaka mana, shin yaya taimakon Allah zai kasance a garemu ranar gobe kiyama na sakamakon hakuri, juriya da tsayawa akan hanyarsa da mukai? Tabbas Allah yafi wayannan bayin nasa tausayi da kuma jinkai..."

Daga nan mallam gambo ya fito da wata bakar leda a aljihunsa yace "Sannan ga wannan suka bani sukace in kara jari".
Matarsa tace "Nawa ne?

"Dubu saba'in ne".

"Yawwa mai gida akwai ankon wata yar aminiyar kanwar babata za'ai bikinta a lagos ankon dubu hamsin ne sai kudin mota dubu ashirin kaga shikenan sun samu".
Matarsa Asabe ta fada cikin zolaya....

Tare suka kyalkyale da dariya suka tafa.

RAMADAN SERIES 04

Gaf da shan ruwa dattijo umar yana sassarfa don karasawa gida akan lokaci don shan ruwa tare da iyalansa yana tafe yana godewa Allah bisa ni'imomin da yayi masa a duniya.

Yazo giftawa ta wani lungu kenan sai yaji ana hayaniya alamar ba lafiya ba.

Ai kuwa saiya leka don ganin abinda yake faruwa.

Wata mata ya gani ta shake wuyan wani mai markade da nika tana wujijjigashi tana cewa duk inda yasan yakai mata garin masararta toya dauko mata shi...

"So kake in koma haka? Idan naje me zan cewa yarana? Dame zasuyi buda baki? Miyar zallah zasuci ba tuwo?.....
Matar tana ta furta kalamai kamar wadda ta zauce.

"Wallahi, tallahi, kinji dai na ran.. rantse, ni bansan inda yake ba inaga fa an dauke shi ko kuma wani cikin yaran naki yazo yayi gaba dashi..."
Mai injin nikan ya fada cikin wani sauti mai ban tausayi.

"Nasan wanda ya dauka", wata murya daga baya ta fadi haka.
Wata yar matashiyar budurwace ta fadi hakan lokacin da idanuwan mutane suka koma kanta... "kwarai kuwa nasan wadda ta dauka, wata matace anan gaba kadan gidanta yake...."

"Kinsan gidan?" dattijo umar ya tambaya lokacin da yake kutsowa ta cikin mutane.

"Eh nasan gidan makotanmu ne", ta bashi amsa da sauti mai cike da kwarin gwiwa.

"Da kai mai injin, da ke wadda aka daukewa nikan kuzo muje..."
Dattijo umar ya fadi hakan yana mai nuni dasu.

Ai kuwa suka dunguma wannan budurwa tana yi musu rakiya, basa tsaya ba sai a kofar gidan wannan mata wadda ake zargi da daukar nikan garin masara.

"To barau......"
Matar da aka sacewa zata fara maganganu cikin daga murya tun a kofar gidan dai dattijo umar yayi mata nuni da tayi shiru.

Ya tsaya a kofar gidan ya kwankwasa gami da yin sallama, cikin gaggawa aka amsa. Daga bisani saiga wata mata ta fito sanye da wasu kaya marasa kyau duk sun yayyage idan ba don kamalar da take fuskarta bama, zata zasuyi mahaukaciya ce.

Kafin suce komai sai tayi murmushi gami da gaishesu, sannan tace "Tunda naga mai injin nika, ba sai kunce komai ba nasan meke tafe daku amma ku shigo ciki...."

Ba tare data jira abinda zasu ceba sai kawai ta koma cikin gida.

Dattijo umar, mai inji da matar da aka sacewa garin masara sai wannan ya kalli wannan, wannan ya kalli wannan. Daga nan sai suka kutsa kai cikin gidan suna tafiya cikin bugun zuciya da tsoron abinda zasu tarar, tuni ansha ruwa amma saboda abinda ke gabansu bama su ankara ba.

Shigarsu keda wuya suka iske yara guda hudu zaune sun sanya garin masarar nan a gaba suna hambudawa a baki suna korawa da ruwa, biyu daga cikin yaran bazasu wuce shekara biyu da rabi ba, yayinda na sama dasu zai zamo mai shekara hudu sai babbar da take mace mai kimanin shekaru bakwai....

"Umma gayin (garin) yau yafi na gobe (jiya) dadi ko? Shaboda (saboda) kin shaka (saka) maci (mashi) shukali (sukari)"
Wani a cikin yaran ya fada cikin gwaranci.

Wannan matar idonta ya ciko da kwallah daga bisani ta fara da cewa "Wayannan 'yayana ne, mahaifinsu ya tafi lagos ya barni dasu, ba ruwansa da cinsu ko shansu baya bani komai saidai a karshen wata yazo ko kuma ya turo min da dubu goma, wannan karon kuwa watansa uku bai zo ba baiyi aike ba, sannan wayarsa ta daina shiga. A haka nake samu in dan je inyi aikatau abinda na samu dashi zamuci abinci ni da 'yayana. Shekaran jiya ban samu komai ba, don haka muka kwana da yunwa ba don ma makota sun taimako mana da ragowar abincin shan ruwansu ba da tazarcen azumi zamuyi....."
Kuka ya sarketa daga bisani taci gaba da cewa "jiya kuma sai aka turo min da garin masara, nayita neman abinda zan samu in girka amma abu ya gagara, ni kuma ba iya tambaya zanyi ba.... Sai muka hambuda shi haka muka kora da ruwa. Yau kuma dana rasa abinci sai zuciyata ta kasa jurewa......" ta sake fashewa da kuka... "shine naje injin nika kawai na sunkuto wannan na taho dashi, daga nan naje kanti nace abani suga gwangwani shima ban bada kudin ba nayi tahowata, da nazo shine na hada musu shi don suci... Abinda suka rage nima sai inci......."

Mai injin nika, matar da aka sacewa garin masarar da dattijo umar gaba dayansu kwalla ke kwaranya daga idanunsu.

"Saiki dauki garinki", dattijo umar ya fada lokacin da yake yiwa mai nikan nuni da taje ta dauko.

"a'a wallahi na yafe mata...."
Mai nika ta fada cikin kuka.

Koyaya zata kasance?

RAMADAN SERIES 05

Dattijo umar, mai injin nika, matar da aka sacewa gari da kuma matar da tayi satar duk suka tsaya tsawon yan dakiku babu wanda yace uffan.

"Zamu wuce...."
Dattijo umar ya katse shirun da furucinsa.

Wannan mata mai satar gari cikin fara'a tamkar ba itace a cikin damuwa ba tace "Tohm, Nagode Allah ya saka da alheri..."

Ba tare da wani a cikinsu yace wani abuba suka juya suka nufi gidajensu.

**    **     **      **

Duk da an jima da shan ruwa, amma zaka iske cikin gidan dattijo umar yayi tsit, dukkaninsu sun ajiye kayan buda bakin a gabansu sunyi jigum, an rasa wanda zai fara ci.....

Dole su shiga damuwa domin sun saba shan ruwa da mahaifinsu amma kuma yau babu shi.

"Gaskiya inaga wani aikin ne ya tsare baba, kuma babu abinda zai sameshi sai alkairi domin Allah bazai wulakanta shi ba...."
Yaya usman ne yake furta haka, yayinda yake cusa dabino cikin bakinsa.

Humaira ta bishi da kallo, daga bisani itama ta dauki dabinon zataci amma sai abu ya faskara.

Mahaifiyarsu (Maryam) kuwa tagumi ta rafka....

"Assalaam Alaikum..."
Sallamar dattijo umar ta katse shirun nasu, lokacin da yake kutsowa cikin gidan.

Da gudu Aliyu ya mike ya tarbeshi yana yi masa sannu da zuwa.

Daga nan ya basu labarin abinda ya tsare shi.

Matarsa maryam tun kafin ya kammala labarin take kuka, daga bisani yana kammalawa tace masa "Abban humaira, Tabbas wannan watane da Allah yake ninninka kyawawan ayyuka, kuma wata ne wanda Allah yake 'yanta bayinsa... Shin mezai hana ka zuba naka jarin a wannan wata mai alfarma, me zai hana ka bawa Allah rance, tunda aka bashi anan duniya ninninkawa yake a gobe kiyama.... Tabbas mafi girman ibadar da zakayi yau itace taimakon wannan mata da yayanta..."

"Baba tunda baku bar musu wani abinci ba a maimakon garin masarar da suke ci, ni na basu abincina na shan ruwa...."
Yaro Aliyu ya fada.

"Ni kuma kudin da muke ajiyewa a asusu nida hanan mun basu sa rage wani abin...."
Humaira ta furta hakan tana mai sunkuyar da kanta.

"Ni kuma zanyi dakon kayan naku duka zuwa gidan".
Yaya usman ya fada.

Dattijo umar ya juyo ya harare shi.

Haka suka tattara abinda zasu iya usman ya dauka Aliyu yana biye dashi, su biyun duka suna bayan mallam.

Bayan sun nemi izini sun shiga sai dattijo umar ya gabatar mata da abubuwan daya halarto dasu.

Tayi godiya, daganan yayanta suka kewaye abincin da aka kawo sunaci.

"Baba irin abincin Aljanna da kike bamu labari ko?
Babbar yarta yar kimanin shekara bakwai ta tambaya.

"Tabb kaji yarinya, aina Aljanna yafi wannan sau malala gashin tinkiya..."
Aliyu yayi tsalle ya dira cikin maganar.

Yarinyar ta dago ta kalleshi ta kebe baki tace "Dan shishshigi kawai".

Aliyu yayi dariya baidai tanka mata ba.

Yaran suna walwala amma ita kuwa matar babu walwala a fuskarta.

Dattijo umar yayi sallama da ita har sun juya zasu tafi sai matar tayi masa inkiyi ya tsaya.

Tazo daf dashi tasa hannunta ta share hawaye, sannan tace masa "Bayan fitarku aka zo aka sanar dani mahaifin yaran nan danace muku ya tafi lagos ya rasu, wata hudu kenan da suka wuce..... Ya mutu sakamakon taresu da yan fashi sukai, suka bukaci ya basu kudin dake dauke dashi kiminin dubu tamanin, shikuma yayi gardama a cewarsa wannan na iyalansa ne, kuma inba iyalansa ba bazai bawa wasu ba, saidai su kasheshi.... A karshe yayita kokawa dasu, ganin haka yasa abokan tafiyarsa da suke mota guda suka samu kwarin giwar rufarwa yan fashin inda suka kashesu baki daya, shi kuma saboda raunika bayan yan awanni dayin artabun ya mutu..... Kafin ya mutu ya bawa wani amintacce a motar kudinsa yace don Allah duk kokarin da zaiyi kada kudin su wuce sati basuzo gareni ba....."

Ta fashe da kuka.

Sannan taci gaba da cewa "Bayan wancan sun tahone suka qara samun matsalar yan fashi a hanyar inda suka kwace dubu tamanin din, shima yaso yayi gardama sai suka jijji masa ciwuka sannan suka karbe kudin ta karfin tsiya.... Amma don isar da amanar amininsa a haka da ciwukan basu gama warkewa ba ya shiga aikin karfi kala-kala burinsa shine ya hada dubu tamanin din nan ya kawo min, amma sai abu ya faskara. Shine ya yanke shawarar zuwa da abinda ya samu don bani su sannan ya bani hakurin jinkiri da yayi...... Yanzu haka dubu hamsin ya bani...., yanzun nan ma yace min zai dawo ya bani wani sakon...."

Ai kuwa bata gama rufe baki ba, saisuka ji an rangada sallama, sai gashi ya shigo, kansa daure da bandeji, sannan yana dogara sanda.

Yana shigowa ya hada ido da dattijo umar sai kawai ya saki sandarsa kasa ya zazzaro ido yace "Umar Muhammad class captain!"
Ya dafe kirjinsa.

"Tanimu Tijjani bushasha!"
Mallam ya amsa masa lokacin da suka rumgume juna suna kukan farin ciki.

RAMADAN SERIES 06

Cikin farin ciki Dattijo Umar ya kalli abokinsa Tanimu gami da share kwallar dake idanunsa sannan ya dora da cewa "Duniya kenan, duk tare mukayi yarinta kamar bazamu taba rabuwa dai-dai da minti biyar ba, amma gashi yau munyi shekaru aru-aru bamu haduba sai yau cikin ikon Allah, tabbas Allah shine abin godiya".
Bayan sun dan tattauna kamar yadda tsoffin dalibai sukeyi sai suka fice suka nufi gidan dattijo umar tare da Aliyu da kuma yaya usman.

**      **       **        **

Samari ne jere a zaune cikin duhu, tun daga nesa idan ka hangosu zaka san cewa wayannan ba mutanen kirki bane, zaman da sukai a duhu shi zai kara tabbatar maka da hakan, nesa dasu kadan masallachi ne, wanda ake sallar tarawih a ciki.

Kaico a wata mai alfarma, a watan da ake neman kusanci ga Allah amma su suna neman nisanci da Allah....

Dattijo umar ne yake tafiya tare da yayansa yaya Usman da kuma Aliyu.

Tun daga nesa yake jin warin wiwi, don haka saiya umarci Usman da Aliyu dasu jira shi.

"Baba don Allah ka rabu dasu, yi musu magana fa babu abinda zai jawo maka sai danasani, kodai ka gama babatu suki jinka, ko kuma ma su dauki wani matakin, wannan gangancine fa...."
Yaya Usman ya fada yana mai kawar da kansa daga kallon dattijo umar.

"Haba yaya usman, babane fa, amma kana yi masa magana kamar kana yiwa kaninka magana, baka san in ana yiwa babba magana tattaudan lafazi ne yake fita ba?"
Dan Karamin kaninsa Aliyu yayi masa gyara.

Yaya Usman murmushi kawai yayi ya shafi kan Aliyu sannan yace "Nagode aku".

"Umarni na baku ku jirani".
Dattijo Umar ya ambata lokacin dayake karasawa gurin matasan.

"An gaida mazzaje", ya fada da murya ba irin tasa ba.
"Allah yabar mana mai gida", wani a cikin masu shaye-shayen ya fada.

Dattijo umar yace "miko min kara daya nan", lokacin da yake mika hannunsa.
Aikuwa suka miko masa ya kunna mata wuta sai kuma kawai ya tsaya yayi jigum.

"Yadai baaba lafiya?"
Wani cikin matasan ya fada.

"Ina so ku nuna min duhun da zan shiga inda Allah bazai ganni ba, domin kuwa inajin kunyar Allah in saba masa a wannan wata mai alfarma, lokacin da wasu suke neman gafara da nemarwa al'umma aminci, ni kuma lokacin nake karawa kaina zunubi da kuma kirawowa Al'umma fushin Allah tsinuwarsa......."
Kawai sai ya fashe da kuka ya durkusa bisa gwiwoyinsa yana neman gafara.

Kawai suma matasan nan masu shaye-shaye sai duk suka zubar kayan shaye-shayen suna zubarda hawaye kamar yadda sukaga yanayi suma suna neman gafara.

Basu aune ba sai gani sukai babu mutum babu dalilinsa.

Wanda ya fara ankara sai yace "Kai babaye ku duba min mana wannan mutumin fa ya bace".

Wani yace "To wallahi Aljanine".
Wani ya dora da cewa "Ai an kulle Aljanu saidai mala'ika"

Ai kuwa sai suka tashi suka ruga suna guje-guje.

Wani a cikinsu rigarsa ta makale a jikin wani ice shi kuma sai kicin-kicin yake amma ina an rikeshi tamau....

Ai kuwa saiya fara magiya "Mala'ika don girman Allah kayi hakuri, wallahi ni zaman taya hira nazo yi...."

Yaci gaba da kici-kicin guduwa yana ta faman magiya, zuwa can da rigar ta fita daga jikin icen nan fa shima ya tsere.

Daga ranar basu kara zama a wajen ba.

Shi kuwa mallam da yayansa sai suka tafi masallaci suna dariyar abinda suka gani.

RAMADAN SERIES 07

Kamar kullum, yauma an tashi da kwalleliyar rana mai tsananin zafi, don haka zaka iske da dama daga masu zirga-zirga yau sun samu inuwa sun zauna, duk da cewa inuwar ma huci take fitarwa saidai kuma tafi cikin ranar dadin zama nesa ba kusa ba....

"Ana shan rana kwanakin nan, mudai rokon da muke Allah yasa ibadarmu karbabbiya ce".
Wani dattijo ya fada lokacin da yake damkawa dattijo umar kayan da ya siya a wajensa.

Dattijo umar ya amsa da ameen.
Sannan yayi jigum idonsa ya ciko da kwallah.

"Baba me kake tunani ne?"
Dansa Aliyu ya fada lokacin dayake jan rigar mahaifin nasa don ya kula dashi.

"Babu wanda yake da tabbas din an karbi bautarsa, wallahi da ace zan samu tabbacin cewa Allah ya karbi raka'a guda daga sallolin da nayi a duniya tabbas da zanyi murna mutuka saboda nasan cewa Allah baya karbar abu sai daga masu tsarki, ita kuwa wutar jahannama bata kona masu tsarki saidai idan suna tare da dattin shirka da zunubai to a sannan ne za'aje a kone wannan dattin da suke dauke dashi....."
Dattijo umar ya furta a matsayin amsa zuwaga dansa.

Aliyu ya kalli mahaifinsa umar, daga bisani ya fara jero tambayoyi kamar haka...
"Shin Allah ba mai jinkai bane?
Shin Allah ba mai gafara da yafiya bane?
Shin Allah ba yana sane da bayinsa bane?"

Duk sanda yayi tambayar sai mutanen kewayen su amsa da cewa "Haka ne", a zukatansu kuwa suna cike da mamakin wannan yaron

"To don haka ni banga abin jin tsoro ba, Allah yana mutunta wayanda suke mutunta abin daya shar'anta."
Aliyu ya furta hakan

Usman dayake kusa dashi sai yayi murmushi yace "Ai kuma idan ka tuna Allah din dai shine mai azabtar da bijirarru, shine wanda komai kankantar mummunan aikin daka aikata saika gani a mizaninka, hakanan kyakkyawan aiki ma."

**          **          **         **

Bayan dawowarsu gida ne sai kawai Aliyu  ya shiga daki jim kadan sai gashi ya fito, yana muzurai.

"Lafiya?"
Dattijo umar ya tambayeshi.

Aliyu ya bude baki zai magana sai kawai gyatsa ta kwace masa.

Yaya usman da yake gefe har faduwa yayi saboda dariya....

Aliyu yayi tsuru-tsuru kamar mai jin kashi.

"Karya azumin kayi?"
Mallam ya tambaya yana mai sakin bakinsa gami da duba agogo. Sannan yaci gaba da cewa "Da kayi hakuri saura awa daya da minti talatin ma a kira sallah..... Shikenan ka rasa ladan azumin yau......"

Sai kuwa Aliyu ya zabura yace "Subhanallah, yanzu baba duk kishirwar danayi a farko ta zama ta banza kenan...."
Ya tambaya idonsa ya cicciko.

Mahaifiyarsa maryam tayi maza ta sako baki tana mai cewa "Sannu dana ai kayi kokari, kafi wayansu."

"Ainasan dani kike" yaya usman ya fada yana mai kawai da kai gefe.

Aliyu yasa hannunsa a habarsa yace "Ohh lallai yaya    usman ba kunya".

Kaga kaima kayi asarar naka azumin, tunda Allah yana karbar aikin mutanen da ya yarda dasu ne. Kai kuwa yanzu kayiwa umma rashin kunya kuma kasan Annabi yace " Yardar Allah tana daga yardar iyaye, hakanan fushin Allah yana daga fushin iyaye".

Usman yaje gaban mamansa (maryam) ya sunkuyar da kansa yace "Yake mahaifiyata ki yafe min domin yardar Allah tana tare da taki yardar".

"Magajin mallam kenan ba komai, amma ina so kaje ka sauya askin kanka, kai yanzu baka jin kunyar yin sallah alhalin kayi aski irin wanda Allah ya haramta?"

RAMADAN SERIES 08

Mallam daya shige daki ya fito da sauri yana mai kallon kan yaya usman daga bisani ya rafka salati.

"Baba wai babu kyau ne?", Yaya usman ya tambaya da alama dai yana cike da jin mamaki.

Humaira da take sakin danwake a tukunwa ta cafe maganar tana mai cewa "Annabi ya hana aske wani sashin kai abar wani sashen. Hadisin Bukhari da Muslim ne suka rawaitoshi.

Hanan ta kara da cewa " Hakanan a musnad na imam Ahmad ma ya rawaito cewa Annabi yaga an yiwa wani yaro aski, an aske wani wajen an bar wani wajen, sai Annabi ya umarci cewa kodai a askeshi duka ko kuma a kyaleshi duka......" 

Yaya usman yayi jigum sannan yace "To babu wata yar fatawa mai dan sauki?"

Kafin kowa ya bada amsa  Aliyu yayi caraf ya tsomo baki yana mai cewa "Yanzu har akwai wani malami wanda yafi Annabi Muhammad (S.A.W) iya bada fatawa da jin kan al'umma?

Dattijo umar ya gyada kai sa'annan yace "Usman, shin da son zuciyarka da kuma abinda ya tabbata a sunnah wanne zaka bi?

Usman ya sunkuyar da kansa kasa sa'annan yace "abinda ya tabbata a sunnah".

"To kaje ka aske gashin kanka".
"An gama Babana."

**         **          **          **
Kasancewar lokacin shan ruwa ya kusa, wannan ne yasa zakaga kowa hankalinsa ya karkata zuwaga gida, masu ababen hawa suna sassarfa don karasawa gidajensu don shan ruwa tare da iyalansu, wasu kuma zaka iske suna tafe ne akan kafafuwansu, suna tafiyar kama basaso, sakamakon gajiya da sukai.

Wasu kuma zaka iske su akan kafar tasu suke tafiya amma sunata kazar-kazar kamar basa jin azumin.

Dattijo umar da dansa usman zaka iya cewa suna tsaka-tsaki.

Wani mai ayaba suka gani suka tsayar dashi, zasu siya sai kawai dattijo umar yace masa "Yi hakuri".

Suka kuma tarar wani mai mangoro, shima sai mallam yayi masa umarnin ya wuce.

"Baba me yasa baka siya ba?"
Usman ya tambaya.

"Usman wayannan kayan nasu ba nunar gaske sukai ba, tabbas akwai wani sinadari da suke saka musu, wanda zaisa su nuna da wurwuri. Kuma wannan sinadarin yana saka kansa (cancer). Don haka kaima ka gayawa duk wanda ka sani cewa ya kula da kyau....."

"Baba mezai hana mu sayi ko kadan ne?"
Usman ya kuma tambaya.

"Abinda yasa bazamu siya ba shine fadin Allah; kada ku jefa kawunanku zuwa ga hallaka...."

RAMADAN SERIES 09

A gajiye yaya usman da mallam suka karaso gida.

Bayan sun sha ruwa sun zauna sun tattauna kamar kowane lokaci sai mallam yake musu wata gajeriyar nasiha, bayan kammalawarsa ne kuma ya mike suka tafi masallaci tare da Aliyu da kuma yaya usman.

Bayan fitarsu sai Hanan ta kalli humaira tace "Nifa gobe saina tambayi baba wai meyasa baya tafiya damu masallaci sallah, alhalin ya halatta, kuma musammam ma sallar taraweh wadda mutum zaifi sakin jiki yayi idan yana binta a jam'i.....”

Humaira tayi murmushi sannan tace "Ai bakisan yadda akai ba, kwanaki umma ta tambayeshi tace zata masallachi, mai makon ya bata amsa saiya kawar da kai..... Ita kuwa saita dauki hijabinta tayi ficewarta... Tana fita sainaga ya bita waje... Danake tambayarta bayan ta dawo saitace min wai ai baya son mata su rinka zuwa ne... Ita kuma bataga dalilinsa nayin hakan ba..."

"Idan ya dawo zan ji ta bakinsa"
Hanan ta fada lokacin da take gyara kashin kanta.

Jim kadan saiga dattijo umar ya dawo tare da Aliyu da yaya usman.

"Ku bakuyi sallar bane?"
Dattijo umar ya tambayi su humaira.

Kafin su bada amsa yayi usman yayi caraf yace "Wayannan ai in baka nan ma bayin sallar suke sosai ba, ta farillar ma ya aka kare ballantana ta nafila."

Mallam ya juya ya harareshi daga bisani ya juyar da kansa bangaren su hanan yace "Tambayarku nake yi ko?"

"Baba munyi niyyar zuwa masallacin tare da kai..." Hanan ta fada sannan taci gaba da cewa "Sai mukaga ka tafi, munyi niyyar biyoka kuma sai muka shagaltu da yin gyaran gida".

"Ai gwara ma da baku biyomu ba, domin yanzu mata da yawa ba sallah take kaisu masallachi ba, sauda yawa zaka iske maza ne suke taresu a hanyar, masu dama-dama sune wayanda suke samun rakiyar damarinsu zuwa masallaci da kuma rakiyar dawowa gida...." Mallam ya ambata sannan ya cigaba da cewa "Da ace da yawan iyaye sun san me yake wakana ga yayansu a wannan wata mai alfarma da basu turasu sallah ba tare da kyakkyawan tsaro ba".

"A tunani kenan, amma a addinance me addini ya nuna akan zuwan mata masallachi?
Maryam matar mallam ta tambaya.

"Zan baku amsa gobe idan Allah yasa mun gani"
Dattijo umar ya ambata.

RAMADAN SERIES 10

Tun bayan kwanciyarsa bacci shidai bai tuna komai ba, yadaiji yana yin jikinsa ya sauya domin jikin yayi nauyi.

Hayaniyar da yake jiyowa itace tasakashi ya yunkura domin mikewa zaune, amma sai yaji ya kasa ko motsawa...

Yayi yunkurin bude bakinsa, namma dai inaaa sai abu ya faskara. A sannan ne kuma hankalinsa ya fara tashi, domin yana ganin abubuwanda baya ganinsu a rayuwarsa.

"Anya kuwa ba mutuwa nayi ba", ya fada a cikin zuciyarsa lokacin yayi dai-dai da lokacin zuwan wasu manyan abokansa su biyu. Sukaje kansa suka tsaya daga bisani saiga wani likita ya shigo dauke da kayan gwaji, bayan ya kammala gwajin saiya dago yana mai kallonsu yace "Saidai kuyi hakuri, amma dattijo umar ya cika".

Akan idonsa yaga sun fashe da kuka, yana yunkurin bude bakinsa amma ina abu ya gagara.

A wannan lokaci ne matarsa ta shigo tana mai kuka mai ban tausayi. Yayi wani namijin yunkuri da zummar daga hannunsa don yayi musu inkiya suyi shiru. Amma inaaa sai abu ya faskara.

Akan idonsa aka rinka daukarsa daga nan zuwa can,  yana kuma jin magangaun mutane, sannan yana kallonsu amma babu damar basu amsa.......

Babban tashin hankalinsa shine, shin me zai tarar a lahira, domin kawo i yanzu baisan makomarsa ba, shin Allah zai duba abinda mutane suke fada ne a kansa, ko kuwa za'a hukuntashi da laifukan da yake aikatawa?

A sannan ne kuma yayansa suka shigo, Yaya usman, halifa, hanan da humaira. Dukkaninsu suna zubda hawaye. Nan fa hankalinsa ya sake tashi. Shin idan ya mutu wanene zai kula dasu?

Yana ji yana gani aka ciccibeshi aka kaishi inda za'ai masa wanka, bayan an kammala an shirya shi.....

Sai aka nufi makabarta, to wai shin gaggawa zaiso suyi ko kuwa lakai-lakai? Domin kuwa shi kam baisan me zai tarar ba a kabarinsa.

Lokacinda aka kaishi tuni an kammala hakar kabarin. Don haka sai suka ciccibeshi suna kokarin saka shi a kabarin.

Shikam fargabar abinda zai tarar aciki yake kawai, zuciyarsa tana cike da wasu-wasi.

Bai dawo hayyacinsa ba sai ji yayi an rufe kabarin ruf.

Yana jiyo karar sawayen ko takun wayanda suka kawoshi.

Daga can kuma sai kabarin yayi masa wata matsa wadda babu abin misaltata anan duniya domin ji yayi kamar kasusuwansa sun harhade saboda tsananin karfin matsar.

Daga can kuma ya fara jiyo wata tsawa da rugugi mai tsananin karfi, daga can saiga wasu halittu biyu mafi ban tsoro a abubuwan daya taba gani a duniya, suna kartar kabarin nasa yana tartsatsin wuta.....

"Tabbas abinda ka shuka shi zaka girba......."
Daya daga cikin halittun guda biyu ya fada.

Mallam ya bude bakinsa bisa ga mamaki saiyaga bakin ya budu.

Kafin yace wani abu saiyaji muryar matarsa maryam tana cewa...
"Mai gida ka tashi kayi sahur, don ka kusa makara yau...."

Firgigit ya farka a razane.

"Tabbas abinda na shuka shi zan girba". Ya fadi hakan lokacin da yake jinjina abin a kwakwalwarsa.
Yaci gaba da cewa "Ashe mafarki nake...... Tabbas duniya abar tsoro ce."

Zamu dakata anan
Sai kuma a shiri na gaba.

Muna bin dattijo umar bashin bayani akan fita sallar mata.

RAMADAN SERIES 11

Bayan mallam ya kammala sahur yaje masallachi ya dawo ya kuma gabatar da azkar kamar yadda ya saba gabatarwa sai hanan da humaira suka matso kusa dashi. Ba tare da jinkirtawa ba sai humaira ta fara da cewa "Baba meyasa baka so mu fita sallar tarawehi masallachi, kuma meyasa baka hanamu fitar saidai mu gane kin hakan a fuskarka?"

Dattijo umar yayi murmushi yana mai kallon gefe guda a dakin da alama wani sakalallen agogo yake dubawa. Lokaci guda kuma ya mike ya fice daga dakin ba tare dayace musu uffan ba.

Humaira ta kalli hanan, daga bidani tayi ajiyar zuciya tace "Mu tashi mu tafi, naga kamar baba baya son irin wannan tambayar".

"Ina so mana, me zai hanani inso abinda ya fito daga masoyana guda biyu?" Ya fada musu yana murmushi a daidai lokacin da yake takowa zuwa cikin dakin.

Bazaka iya banbancewa ba, shin karar tik-tik-tik da agogon yake da karar takun kafarsa wannene yafi kara  ba. Hakan kuwa ya faru ne domin a nutse yake tafiyar cikin dakin wadda da kadan ta zarce irin tafiyar da yake yi a waje.

Bayan yazo ya zauna yana mai fuskantar yayan nasa sannan saiya fara da cewa; "Na'am, hakika fitar mata sallah sanannen abune a zamanin Annabi Muhammad S.A.W domin hadisai sun nuna haka.... Akwai hadisi da Annabi yayi bada umarnin cewa kada a hana mata zuwa masallachi, wannan in sukace zasuje kenan"

Yaci gaba da cewa "Tare da cewa an samu sauye-sauye tsakanin zuwan matan zamanin Annabi da matan yanzu din. Domin a wancan lokacin in baku manta ba, matan ma ba'a gane su saboda shigarda sukeyi da kuma tsayawa tsayin daka don yin taka tsan-tsan....."

Yayi shiru lokacin da yake saka maballin hannun rigarsa a bigirensa tare da rarraba ido ko zai hango warin (dan'uwan) maballin na daya hannun.... Daga bisani saiya cigaba da magana; "Yanzu kuwa da dama daga mata da suke zuwa sallah zaku iske kadan ne masu tsayawa suyi sallar, sai wasu masu yawa da suke waya da samari, sai kuma wayanda suka dauki masallacin dandali, sai kuma wayanda suka dauki hanyar zuwa masallacin da dawowa a matsayin wani dandalin soyayya ta inda zaka iske suna tafiya ne da samarinsu maza hakanan suna dawowa da su ne....."

Mallam ya mike sakamakon ganin maballin daya rasa da yayi, sa'annan ya sanya shi a bigirensa kafin daga bisani ya  cigaba da cewa "Wasu lalatattun kuma bama masallacin suke zuwa ba... To don gujewa wayannan matsaloli musamman a wannan zamani da muke ciki shiyasa ni nake ganin yin sallarku a cikin gida tafi, domin samarin yanzu suna da karfi wajen juyar da tunanin mata cikin kankanin lokaci tamkar sunyi musu asiri.... Tabbas a cikin dadin baki da iya jera magana ma akwai nau'i na sihiri... Don haka nake ganin daka tura yarka wani katon banzan yaje ya saka mata guba (poison) a cikin kwakwalwarta, gwara ka barta a tare da kai.... Zakafi samun nutsuwa....".

Mallam ya sake mikewa gami da dauko wata hula daga nesa kadan dashi yana kallonsu yana murmushi.

"Baba wannan hular batai matching ba sosai gaskiya..."
Humaira ta ambata.

Ta mike ta nufi inda ya dauko hular tasa sannan ta dauko wata daban saita miko masa da hannu biyu tana mai cewa "Wannan zatafi yi maka kyau".

Mallam ya harareta sannan ya karbi hular yana mai cewa "Wannan hular ta sallah ta ce".

Amma sai ya cire waccan yasa mai kyan wadda humaira ta bashi.

"Gashi ba mudubi amma ga camera din wayarmu nan ka duba"
Hanan ta fada lokacin da take mika masa wayar.

Ya duba yaga eh tabbas yayi kyau.
Saiya shafa screen din wayar saiga hoton wata wadda bai sani ba cikin uniform tare da humaira da hanan din.

"Wannan wacece haka naga ta fiku yin kyau"
Mallam dattijo umar  ya fada cikin zolaya.

Kafin su bada amsa tuni mahaifiyarsu shigo dakin ta kalli dattijo umar daga bisani tace "Wacece kake cewa tayi kyau a hoto?"

Dattijo umar yayi maza ya amsa da cewa "Kece mana ai hoton da kuka dauka kwanaki a wayar na gani".

Maryam mahaifiyarsu ta danyi murmushi tace "Auhoo.." Sannan ta juya ta fice.

Humaira da hanan suka kalli juna suna murmushin ganin yadda ummansu tayi.

"Baba nifa ban gamsu da wannan bayanin naka ba".

Humaira ta ambata.

"Ba damuwa idan na dawo zaki fahimta."

Mallam ya fada lokacin daya fice daga dakin don tafiya unguwa.

Zamu dakata anan.

RAMADAN SERIES 12

Titi ne cike da ababeb hawa, wasu suna tafiya wasu kuma suna dawowa, hayaniya da zafin rana sun yawaita a ilahirin filin wajen.

Daga gefen titi wani mutum ne da alama ya manyanta yake tafe yana tura kekansa, kaida ganinsa kasan a gajiye yake.

Nesa dashi kadan kuwa dattijo umar ne yake binsa a baya ba tare da sanayyar mutumin ba.

Haka suka wanzu suna tafiya ga zafin rana nan wanda ya mamaye hanyar da suke tafiya akai.

Wannan mutum bai tsaya ba saida yazo kofar wani gida sannan ya tsaya ya kafe kekensa a kofar gidan kana ya shige cikin gidan.

Dattijo umar dake biye dashi saiya rakabe a jikin wata bishiya don kada mutumin ya ganshi.

Jim kadan bayan shigar mutumin saiya fito cikin gaggawa da sauri da zummar hawa kekensa.

Cikin hanzari dattijo umar ya bayyanar da kansa ga wannan mutumin suka kalli juna daga bisani suka rungume juna.

"Umar dama kana nan?"
Wannann mutum ya fada lokacin da yake kokarin share kwallar da take idonsa.

"Ina nan, Mallam Goje", dattijo umar ya ambata.

"Tabbas rayuwa abar tsoroce," mallam goje ya fada  ya kuma cigaba da cewa; "Duk matsalolin da kake hasashensu saida na hadu dasu... Wai ni anya kuwa kaiba waliyyi bane? Inba haka ba ya za'ai hasashenka ya rinqa fita dai-dai?"

Dattijo umar yayi murmushi "Ai ana kallon yau ne domin sanin abinda gobe zata haifa, yau tana da ciki kuma itace mai haifar gobe, babu wanda yasan abinda yau zata haifa gobe sai masu hankali da auna abubuwa. Inbaka manta ba nasha gaya maka cewa mutukar zaka rinqa shaye-shaye tofa rayiwarka ta gaba kake batawa.... Ita rayuwa kamar noma ce, idan ka bada himma kayi noma mai kyau to hakika zaka girbi abu mai kyau, sannan zakayi farin ciki".....

"Fito kayi min magana da hausa sosai don Allah".
Mallam goje ya fadi hakan.

"Eheem..." Dattijo umar yayi gyaran murya "Mutanen duniya kakaf tamkar manoma suke", dattijo umar ya ambata lokacin da yake jan hannun mallam umar yana mai zaunar dashi akan wani benchi.

Dattijo umar yaci gaba da cewa "Nau'in mutane na farko sune wayanda basa aikin komai a gonarsu saidai kewaye kawai, amma bazasu shuka komai ba, wani lokacin zakaga sun taya wasu aiki amma su nasu aikin ya gagara..... Wannan sune wayanda suke rayuwa ba tare da tsara rayuwarsu ta gaba ba, kuma zaka tarar don shirme irin nasu suna taimakawa wasu don cikar abinda suka tsara..."

Dattijo umar ya kalli goje ya tabbatar da cewa yana ganewa sannan yaci gaba da cewa; "Wasu kuma sai sun gyara gonar sosai sai su fara shuka gishiri, dusa, awara da sauran kaya marasa tsiro. Kuma suyita faman jigilar ban ruwa da gyaran gona, wani lokacin ma har kashe kudade zakaga sunayi don gyaran gona, su a tunaninsu noma suke.... Wayannan sune masu rayuwa bisa tsari mara kyau da planning wanda bazai taba cika ba, domin hanyar da suka biyo bata bullewa."

Mallam ya yunqura yana mai kokarin tashi lokacin da yake cewa "Kaso na uku kuma sume masu gayara gona sannan su shuka, shuka ingantacciya. Suna mata kuma duk abinda ya dace. Wayannan sune masu tsara rayuwarsu bisa tsararren tsari..... A tunaninka a cikin wayannan ukun wanene zai samu sakamako mai kyau!"  

Mallam goje yayi murmushi yace "Banda hauka inada gona in kyaleta ban shuka komai ba, kuma har inje gonar wani in tayashi aiki.... Ko kuma haka kawai in rinka shuka gishiri a cikin kasa ai hauka ne wannan kawai... Kuma ko karamin yaro ai yasan cewa na ukun sune masu hankali kuma manoma na gaskiya..."

Dattijo umar yayi murmushi sannan yace "To ai kai goje bayan rashin shuka da kayi a gonar rayuwarka, har zuwa kayi gonar wasu ka tayasu kuka rinka shuka dusa da maggi.... Don bayan ka bata yarintarka a Shaye-shaye daga baya kuma komawa kayi karen yan siyasa kaci karenka babu babbaka...."

"Daina tuno min da wannan lokacin" daganan goje ya fashe da kuka sannan yace "Anya Allah zai yafe min kuwa?"

"Me kayi kai kuwa har kake fadin haka?"
Dattijo umar ya tambaya.

"Zauna in gaya maka"
Mallam goje ya ambaci hakan.

RAMADAN SERIES 13

Bayan dattijo umar ya sake zaunawa ya fuskanci goje, sai goje ya share kwallar da take gudana a idanuwansa sannan daga bisani ya fara da cewa...

"Tsawon shekaru bana sallah, idan kaga nayi to kawai nayita ne, wani lokacin ma tun tayarda kabbara bansan me zance ba, saidai inyita dungurawa har in kammala. Hakanan watan azumi idan yazo bana yinsa, wani lokacin tsabar takama da cewa babu wanda ya isa dani, tsakar rana zan fito ina karya azumin nawa, kasan  idan kana shaye-shaye ji zakai kaf duniya babu wanda ya isa dakai... Hakanan na kasance mai yawaita sabon Allah da gwabawa Allah magana ....", goje ya fashe da kukan bakin ciki.

"Allah mai karbar tuban bayi ne, tabbas idan ka tuba zai yafe maka", Dattijo Umar ya fada yana mai shafa kan goje tamkar wani karamin yaro.

Goje yana shashshekar kuka ya kara da cewa "Ai idan iyakar wannan ne to da sauki, to amma lokacin dana shiga bangaren siyasa da rigimar daba, akwai wayanda na jiwa ciwuka babu gaira babu dalili, akwai wayanda laifi kankani yasa na yanke musu hukunci mafi muni, na daga kisa ko yanke wani sashe na jikinsu...  Abinda yafi tayar min da hankali shine lokacin da muka taba kama wani matashi ya saci kwanan masara, bayan zaneshi da mukai sai muka kwantar dashi muka sare masa hannunsa na dama, tun daga hammata har karshe....." Kuka ya sarke goje, daga bisani ya share majina ya goge hawaye sannan yaci gaba da cewa... "Wannan matashin yana kuka yake cewa dani, yadda na aikata haka a gareshi insha Allahu nima haka za'aimin, kuma insha Allah sai Allah yayi mini hisabi dana dashi, tunda dai wannan garin ba sata yayiba...... Jin haka yasa yarana suka rufeshi da duka har suka kaishi lahira....." Kuka ya kara sarke goje lokacin daya fado daga kan bencin da suke kai yana mai rirrike kafafuwan dattijo umar, daga bisani yaci gaba da cewa "Sai bayan ya rasu saiga mai saida garin kwakin ya iso garemu a firgice, anan yake bamu labarin cewa wannan matashi ba satar garin yayi ba, siya yayi, wasu daga yan shaye-shaye ne suka tare shi suka bukaci ya basu garin shi kuma yaki basu.... Shine sukai masa sharrin sata..... A wannan lokaci duk da ina cikin mutanen banza banji dadin hakan ba, don haka suma yaran nawa da sukai haka sai nasa aka yayyenke musu hannaye dai-dai dama su biyu ne masu laifin.... Gwabnati kuwa tunda tana bukatar mu a wannan lokaci saboda zabe saita kawai share abinda muka aikata bata dauki wani mataki ba.....".

"Ya'isa haka", dattijo umar ya fada lokacin da yake daga hannu yana mai yi masa inkiyar yayi shiru, zazzafan hawaye ne yake satatowa daga idanunsa...... Daga bisani ya daga hannu sama ya durkusa bisa gwiwowinsa yana mai fashewa da kuka yana cewa "Ya Allah kada ka kamamu da abinda shashashan cikinmu suke aikatawa..., Ya Allah ka yafe mana kura-kuranmu, ya Allah ka shiryi matasanmu...."

Ya sunkuyar da kansa kasa sannan yace "Lallai shaye-shaye yafi komai illa, domin yana sanya mutum yafi dabba dabbanci......"

Bayan sun dauki lokaci mallam yana bawa goje shawarwari saiyace "Sannan akwai shagon da zan doraka akai zan kuma saka maka yara masu kula dashi...."

"Shagon lemuka da ababen ci ne?
Goje ya katse dattijo umar.

"A'a", dattijo umar ya fada cikin murmushi, " Shagon kayan masarufi ne.

Goje da yake tsugune yayi zumbur ya mike ya zaro addarsa daga kugu.

Dattijo umar yayi gaggawar tashi don tserewa. Sai caraf goje ya damkoshi gami dayin jifa da addar tasa, sannan ya rungume dattijo umar yana mai cewa; "kar kaji tsoro, ai na tuba, kaima ka zama mai aminchi anan, burina dai kawai Allah ya azirtani da shahada domin gani nake kamar itace kawai hanyar tsira....."

"Hanyoyin Allah suna da yawa", dattijo umar ya bashi amsa.

A dai-dai lokacin dayake masa inkiya dasuje suga shagon da aka budewa gojen.

RAMADAN SERIES 14

Bayan dattijo umar yaje yakai goje kantin daya mallaka masa don samar masa da aikin yi, daga nan saiya dauki hanya ya nufi gida inda a zuciyarsa kuma yake tunanin illa da matsalar da shaye-shaye yake kawowa....

_Shaye-shaye yafi yaki hatsari, domin kuwa yaki kana yinsa ne da wanda kasan abokin gabarka ne, amma shaye-shaye wanda kuke tare dasu ne zasu zama masu bahagon tunani da *bahaguwar fahimta* sannan su rinka kokarin hallakar daku. Babu wani abin cigaba dazai tabbata a al'ummar da mashaya suka yawaita a cikinta......._

_Saina tuno wani littafi dana karanta *limathaa harramal lahu hazi'il ashya'a* tabbas illar shaye-shaye daga kan giya har zuwa kwayoyi da tabar wiwi, sholisho suna mutuqar cutarwa......._

_Binciken da akai a baya-bayan nan ya nuna cewa mafi yawan kayan shaye-shaye sunfi giya yin illa ga jikin dan'adam... Amma a haka matasa suka rungumi shaye-shayen...._

_Abinda yafi bani mamaki shine yadda matasa suke ganin rayuwar magabatansu da sukai shaye-shaye a wulakance, a tsiyace amma tare da hakan suke sha'awar zamowa cikin yan shaye-shaye......._

Dattijo umar ya dakatar da tunaninsa gami da nazarin hanyar, tabbas taro yayi taro yayinda aketa hayaniya.....

"Kome yake faruwa?" Dattijo umar ya tambayi zuciyarsa.
"Kaida kake fili aikai zaka fini sanin abinda ke faruwa."
Zuciyar ta bashi amsa.

A hankali dattijo umar ya kusanci inda ake wannan hayaniyar yayinda yana kara kusantar wajen zuciyarsa kuma tana bugawa, bugun daya tsoratar dashi.

Anya kuwa ba wani abune yake shirin faruwa ba? Ya tambayi zuciyarsa amma inaaaa ba wata amsa da yake da tabbacin zata iya zama dai-dai.

Kamar daga sama yaji an cafki kugunsa.

Yana waigawa yaga wani matashi mai jajayen idanuwa, leben nan yayi bakikkirin. Yayinda hasken rana yake dallare kansa wanda yayi kwal-kwal yana ta sheki....

"Uban waye ya kawoka wajen nan? Bakasan yan unguwar tsallake basa shigo mana hurumi ba.....?
Matashin saurayin ya tambaya cikin kumbura murya da nuna isa da gadara.

"Haba dai bawan Allah, shin nayi maka kama da masu shirme irin naku? Ko kuwa nayi maka kama da masu gurbataccen tunani irin naka?....."
Kafin dattijo umar ya rufe bakinsa wannan matashi ya kawo masa sara da addar hannunsa....

Saran ya taho yana keta iska ya tunkari kafadar dattijo umar ta hagu.... Da gudu da karar takobin lokacin da take ratsa iska shine ya sanya Dattijo umar rufe idonsa yana jiran yaji saukar saran a jikinsa.

"Kalllll" yaji karar haduwar karfe da karfe, hakan ya sakashi bude idonsa.

Abinda ya gani ya mutukar bashi mamaki, domin gani goje yayi a tsaye rike da adda  a saman kafadar dattijo umar. Da alama dai shine ya kare saran.

Matashin nan ya kalli goje suka wanzu suna kallon kallo, yayinda suka sanya  dattijo umar a tsakiya.

RAMADAN SERIES 15

Dattijo umar ya kalli goje ya kuma juyar da kansa ya kalli wannan fandararren matashin, a zuciyarsa kuwa tunani ne yayi cunkoso inda wani tunanin yake hana wani wucewa....

Caraf yaji an rike kugunsa, zumbur yayi ya duba saiyaga ashe yan sanda ne suka halarci wajen, ba tare da tsayawa sauraron wani abuba sai kawai yaga an azasu a motar yan sanda tare da sauran jama'ar da akayi nasarar kamawa.

Babu wanda yace uffan balle kyakkyawan motsi musamman saboda ganin irin shirin da jami'an tsaron suke cikinsa, fuskokinsu murtuk, wasu daga cikinsu ma sai huci suke...

Bayan sun danyi tafiya mai nisa sai aka tsayar da motar, daga can wani zabgegen kato ya fito yana muzurai yana kallonsu daya bayan daya gamida wata dariyar yake...

"Tabbas babu wanda zai tsira a cikinku, sai wanda ya tseratar da kansa" ya fadi sannan yaja bakinsa gum kamar bashi yayi maganar ba.

"Kamar yaya mu zamu tseratar da kawunanmu?" Goje ya ambata lokacin da yake kallon mutumin ido da ido.

"Kuyi wani abu sai a taimakeku".
Wani tsigi-tsila daga cikin motar ya leko yana mai ambatar hakan.

Shiru shine abinda ya biyo baya.

Dattijo umar ya nisa yace "Bamu gane bafa."

Mai maganar farko cikin jami'an ya daka masa tsawa "Kaiii! Dubu goma-goma zaku bayar".

Duk da mutanen nan suna cikin fargaba amma sai hayaniya ta balle inda suka rinka Allah wadai da wannan salo na ci hanci.

Shi kuwa dattijo umar saiya daga hannunsa sama yana mai cewa "Ya Allah ga talakawanka an kamasu, cikinsu akwai wanda babu ruwansu, kuma an bukaci su fanshi kansu da kudade masu yawa.... Ya Allah wayannan bayin kai kadaine gatansu, da kai suka dogara, gareka suke mika lamuransu..."

Dattijo umar bai kammala addu'ar ba sai sukaji an kira shugaban jami'an a waya.

Ai kuwa cikin gaggawa ya amsa, inda kuma anan take aka umarceshi daya saki mutanen daya kama domin cikinsu akwai yan daba kuma yaran manyan yan siyasa ne.

Da kansa ya karbi tukin motar ya kaisu inda ya debo su sannan ya juya don cigaba da ayyukansu.

Ana ajiyesu ba tare da anci gaba da fada ba sai kowa ya kama gabansa musaman lokacin dare ya fara.

Dattijo umar ne sukai sallama da goje a gaggauce sannan mallam ya nufi gida cikin gaggawa.

_Yanzu wanene yafi laifi cikin wayannan mutane? Su yan sandan da suka dora musu wannan kudi tun kafin aje station ko kuwa shi dan siyasar dayayi umarni da a saki har masu lefin? *Mai laifi ya kama mai laifi, mai laifi yayi waya yace a cika masu laifi don mutanen masu laifi ne*.

"Sannu don Allah".
Wata katuwar murya ta katse dattijo umar.

Juyawar da zaiyi sai yayi arba da wannan matashin da aka kamasu tare.

"Zuwa nayi in bada hakuri, nasan nayi laifi da fatan za'a yafe min".
Matashin ya fada.

"Babu damuwa na yafe maka, amma ka tabbata bazaka taba daina irin wannan laifin ba".
Dattijo umar ya gaya masa.

"Saboda me kace haka?"

"Saboda mutukar kana shaye-shaye a koda yaushe hankalinka bazai taba zama dai-dai ba, sa'annan tunaninka zaiyita tauyewa yana zama mara amfani, harsai a karshe ka koma tunani irin na dabba...."
Dattijo umar yayi shiru sakamakon ganin kwalla da yayi a idon wannan matashin.

Matashin ya risina gaban dattijo umar yana mai fashewa da kuka yana ta faman nadama.

Daga nan dattijo umar ya rarrasheshi ya kuma dauki dubu biyu ya bashi.

Yana bawa matashin nan, sai matashin ya daure fuska ya hankade dattijo umar sannan yazo ya tsaya a dai-dai kan dattijo umar wanda yake kwance sakamakon hankadawar da matashin yayi masa.

"Bazamu taba daina shaye-shaye ba, wannan kudin naka ma, kayan shaye-shayen zamu siya  dasu."
Matashin ya kama hanya ya wuce.

Yabar dattijo umar nan kwance yana jinjina al'amarin wannan matashi.

RAMADAN SERIES 16

_Akwai abin tausayi a rayuwar matasanmu sosai, shin yanzu wayannan matasan wayanda tunaninsu ya gama jirkicewa sune zasu rike al'ummarmu? Shin yanzu wayannan matasa da suka bata kansu da shaye-shaye sune zasu zama iyayen jikokinmu?_

Dattijo umar ya yunkura ya tashi ya karkade jikinsa ya nufi hanyar gida yaci gaba da tunani.

_Shin wacce irin tarbiyya 'ya'yan wayannan matasa zasu samu nan gaba?..... Mutanen da suka gabacemu duk da nagarta irin tasu, amma basu kadai suke tarbiyyantar da yayansu ba, harda makwabtansu da yan'uwa da masu unguwanni, hakan yasa yayansu suka kasance masu tarbiyya da ganin girman na gaba... Amma kayi tunanin me zai faru idan akace mutumin daya lalata rayuwarsa tun yana saurayi shine zai bawa dansa tarbiyya shi kadai, babban abokin adawarsa shine wanda yayi kokarin tayashi tarbiyyar yayansa.... Anya kuwa za'a ga dai-dai...._

Yaci gaba da tafiyarsa yana mai kara sassarfa domin yasan cewa iyalansa suna can hankalinsu a tashe domin kusan karfe goma na dare yanzun amma bai dawo ba. Ga kuma wayarsa a kashe.

Ya laluba aljihunsa da nufin dauko ta yaga ko zata kunnu, amma saiya tarar da aljihun babu komai inka dauke yadin da aka dinka aljihun dashi.

_Babu makawa wannan matashin shine ya sace wayar nan, ina jinsa lokacin da yake taba min aljihu..._
Ya fada a zuciyarsa.

Yaci gaba da tafiyar yana tuno abubuwa da dama...

_Lokacin da muke yara akwai Baban saude, wanda duk yan layinmu suke shayinsa... Idan magriba tayi daya biyo layi ya daka tsawa zakaga yara sun tarwatse sun shige gidajensu... Hakanan ko laifi yaro yayi a gidansu tofa indai akace za'a gayawa baban saude shikenan yaro bazai sake ba. Saidai yaran yanzu sun rasa irin mutanen nan a rayuwarsu......_

Ya karya kwanar gidansa yana tunanin kuma alheran da baban saude yake musu...

_Idan ya dawo daga kasuwa gida-gida yake aikawa yara da alewa, idan kuma anci sa'a yaran suna waje lokacin dayake dawowa da wuri toda kansu zasu je wajansa su karba yana daga su sama yana cafewa suna annushuwa da murna.... Allah sarki baban saude, akwai wata rana daya dawo babu alewa muka kewayeshi zamu karba sai kawai mukaga ya fashe da kuka... Ko menene ya sashi kuka? Tabbas muma bamu san menene ya sakashi kuka ba... Saidai kawo i yanzu zan iya cewa ko ranar bai samu kudin siyar alawar bane? Wannan dai shine ganina dashi na karshe._

"Assalaam Alaikum"
Dattijo umar ya fada lokacin da yake kokarin shiga gidansa.

"Sai yanzu kaga damar dawowa? Duk ka tayarwa da mutane hankali".
Matarsa maryam ta fada cikin fada.

"Wa'alaikum salam", yaya usman ya amsa sallamar.

"Baba ina fatan lafiya dai ka dade haka yau a waje".
Hanan ta fada lokacin datake nufoshi.

"Alhamdulillah, wallahi sai yanzu naji nutsuwa".
Humaira ta fada tana mai bayyana murnar dawowar Abbanta.

"Baba yau kasha yawo", Aliyu ya fada lokacin da yake rike hannun baban nasa yana kokarin yin lilo.

"Masu yimin sannu da zuwa nagode, masu yimin fada suma na gode", Dattijo umar ya fada.

Matarsa maryam ta tako tazo inda yake tayi masa rada a kunnensa sai kawai su biyun suka tuntsire da dariya.

RAMADAN SERIES 17

Bayan mallam ya kwashe labarin abinda ya wakana tsakaninsa da goje da kuma irin abubuwan daya hadu dasu, sai iyalansa sukai godiya ga Allah daya dawo musu da mahaifinsu lafiya.

Cikin dare yaya usman ya farka ya nemi buta yayi alwala don gabatar da tsayuwar dare kamar yadda ya saba jefi-jefi...

Bayan ya kammala yaje ya tayar da sallah, saiyake jiyo hayaniya a tsakar gidansu, don haka sai yayi sallama ya lallaba ya leka, amma bisa ga mamakinsa sai baiga kowa ba.

Saiya koma don yaci gaba da sallarsa abinka da mara tsoro, nan kuma saiyaji wata kara kamar an buga langa a kasa, karar ta cika masa kunne, amma bisa ga mamakinsa baiga kowa a gidan ya farka ba, duk da karar da yaji.

Zuwa can kuma sai yaji an kunna famfo yana ta zuba.

A wannan karon kuma saiyayi tunanin ko Aliyu ne. Don haka saiya leka waje saiya hango Aliyu a bakin famfo yana wasa da ruwa.

"Kai baka da hankali ne, tsakar dare me kake anan? Kashe famfon nan ka dawo daki.

Aliyu ya kashe famfon amma saiya shige bandaki.

Yaya usman ya juyo da kansa zuwa shimfidar Aliyu, abinda ya gani yasa gabansa ya fadi, domin kuwa Aliyu ya gani kwance yana ta sharar bacci.

Yaya usman ya tsaya yayi jugum daga bisani saiya tuno lallai yau sun tsaya jin labari basuyi azkar din da suka saba yiba....

Don haka sai yayi addu'o'in daya iya tunowa daga nan saiya tayar da sallah. Ya kuma kunna kwai don zaifi samun nutsuwa.

Da yasan abinda zai gani da bai kunna kwan ba. Domin kuwa yayi nisa a sallar tasa sai yaga inuwar wani mutum a kusa dashi da yara guda biyu suna bisa sallah.

Cikin dakiya ya dake, yaci gaba da yin sallah.

Lokacin daya kammala fatiha saiyaji an amsa masa da "Ameeen",

Ba shiri ya sallame ya koma kusa da Aliyu ya kwanta. A zuciyarsa kuma yana tunanin _ai idanma wani abin cutarwar ne ba abinda Aliyu zai iya tsinanawa_.

Yana cikin wannan yanayi ne yaga wata halitta a jikin bango tana masa dariyar yake.

Bai samu nutsuwa ba sai lokacin da yaji an turo kofar, maryam ce mahaifiyarsa, tace "Ku tashi lokacin sahur yayi".

Jikin yaya usman a mace ya mike, yana mai kallon wannan halittar ta bango, sai a lokacin kuma abin yaso ya bashi dariya domin kuwa wata rigarsace ya sakaleta a wajen.

Bayan sun kammala sahur, saiyake bawa babansa dattijo umar labarin abinda ya gani.

Dattijo umar yayi murmushi sannan yace "Tabbas ana gane-gane a gidan nan, musamman kafin muyi yawa, ina nufin lokacin da muke mu biyu nida mahaifiyarku.... Kuma abinda yasa kayi wannan gane-gane shine rashin azkar da bamuyiba, sannan kai din akankin kanka bakayi azkar ba yau....."

Yaya usman ya gyada kai alamar hakane.
"To amma baba ko don gaba idan naga irin wannan me zanyi?"
Yaya usman ya tambaya.

Dattijo umar ya kurbi ragowar ruwan dake ajiye a gabansa, sannan yace "Irin wannan kiran sallah zakayi, domin shaidanune shi kuma shaidan duk lokacinda yaji kiran sallah yana guduwa".

"Nagode baba", yaya usman ya ambata.

Daganan suka ci gaba da tattaunawa inda dattijo umar yake bashi labarin gane-gane wayanda suka fi wannan muni wayanda Annabi, sahabbai da manyan bayin Allah sukai.

Daga nan suka tashi gandai Aliyu suka dunguma sai masallachi.

RAMADAN SERIES 18

Zaune suke sunyi jigum babu wanda yake koda kyakktawan motsi a cikinsu, ga dukkan alamu dai wani mummunan labari ne ya riskesu, gabansu kuma wata matace wadda kana ganinta zaka gane cewa ba'a hayyacinta take ba domin banda kuka babu abinda take.

Dattijo umar ya numfasa sannan ya sanya hankici ya share kwallar da take kokarin taradda gemunsa. Yayi hakan ne cikin sauri domin baya so kowa a wajen ya fahimchi cewa kuka yake yi.

"To wai bayan sun hauro gidan naku sun dauke mai gidan naki basu gaya miki inda suke ba?"
Dattijo umar ya tambaya.

Matar ta danyi shiru jim kadan daga bisani tace "Eh basuyi magana ba, saidai lokacin da suke kokawa suka kifar dashi kasa ya samu nasarar cire mayafin da dayansu ya rufe fuskarsa dashi... Kamar nasan fuskar, don tayi min kama data babban yaronsa a tafiyar daba wato ci-zali, kuma abinda ya kara tabbatar min da shine, shine naji mai gidana ya kira sunansa...."

Dattijo umar ya sunkuyar da kansa kasa daga bisani tunani ya shigo cikin kwakwalwarsa...

_Rayuwar shaye-shaye bata yiba, hakanan harkar daba bata yi ba, yanzu dubi bawan Allah nan goje, ya tuba yabar harkar dabar amma har yanzu yan'uwansa na dabar bibiyarsa suke....._

"Mai gida abin nan bafa na zama bane", matarsa maryam ta katse masa tunani, "kamata yayi a tashi a tafi gurin jami'an yan sanda a sanar dasu".

Matar goje da take gefe guda ta zaro ido ta kalli maryam matar dattijo umar gami da dafe kirjinta tace "Kinsan kuwa ci-zali? Babban yaron yan siyasa ne, don haka duk abinda yaga damar yi shi yake yi babu wanda ya isa ya tanka masa".

"Ba damuwa zan san yadda za'ai, yanzu dai inane wajen zamansa?"
Yaya usman ya tambaya.

"Yana can gidan shagala a bayan filin wasa".
Matar goje ta fada.

Tana fadar haka sai yaya usman ya mike zai fice. Dattijo umar ya kalleshi yace Allah yana cewa "Kada ku jefa kawunanku izuwa ga hallaka...., don haka ka dawo ka zauna, mubi abin a sannu".

Usman yayi murmushi yace "Sai kuma Allah yaci gaba da cewa; Ku kyautata domin Allah yana son masu kyautatawa......, sannan yakai babana kayi sani cewa ceto rayuwar baba goje kyautatawa ce mai girma."
Ya juya ya fice.

Mallam yana kwalla masa kira amma ko waigowa baiyi ba.

Mallam ya bishi da sassarfa, amma inaa ko sama ko kasa bai ganshi ba.

**          **          **            **

Zunzurutun matasa ne suke tafi cikin wani yanayi na rashin tsoron abinda zai afko musu koma menene.

Akan gaba yaya usman ne dauke da wani kwali mai dauke da rubutu *Bama goyon bayan zulunchi*, tafe suke suna tunkarar gidan shagala inda ake zaton ci-zali yana can shida tawagarsa.

Babu jimawa sai gasu a kofar gidan suka tarar katotuwar kofar gidan mai kama data gareji a garkame da kwado. Amma abinka da matasa sai kawai suka jijjigeta suka kutsa kai cikin gidan nan take fa yan daban gidan sukayo musu caa suna zage-zage amma da sukaga alamar yawannan gayyar matasan babu tsoro a tattare dasu sai suka fara jaa da baya.

Ganin haka yasa matasan suka kakkama su, suka kukkulkesu da igiya wanda kuma yayi gardama to sai ayi masa ta dole.

Haka wayannan matasa suka shiga bincike, suka shiga wani daki saiga wayoyin jama'a birjik da aka kwace nan fa yaya usman ya bawa wasu matasa umarni suka zuba wayoyin a buhu sukai waje dasu.

Daga nan suka je wata haraba sai suka tarar da ababen hawan mutane da aka sace ana caccanja musu fasali misali tayar wannan babur din a sakata a wancan, tayar wancan ma a sakata a wannan haka dai zaka tarar an sauyawa abin hawa kira ta yadda ko maishi bazai gane shiba.

Nanma yaya Usman yayi umarni aka fitar dasu waje.

Daga nan suka wuce wani dakin suna shiga sukai arba da goje an sare masa hannu guda daya. Yana kwance cikin jini. Nan take suka dauke shi sukai waje dashi, wasu daga cikin matasan suka nufi asibiti dashi.....

Haka dai sukaita ganin abubuwa kala-kala a wannan gida, harma da makamai.

Suna gama aikinsu basu wuce ko inaba da wayannan kayan da kuma yan daban sai ofishin yan sanda.

Suna shiga suka gabatar da kansu da kayan da suka gani a gidan shagala da irin kwayoyin da suka dauko da kuma yan daban gidan shagalar da suka kamo, sai wanda suka tarar ya jinjina musu. Gami da yi musu godiya.

Yana cikin magana sai wayarsa ta dauki qara alamar ana kiransa. Bayan ya amsa kiran sai ya ajiye wayar yayi shiru ya sunkuyar da kansa, daga bisani kuma yace "Kuyi hakuri, gwabnati tace batai amanna da aikin da kukai ba, don haka ana zarginku da zama yan ta'adda, sannan abin da kukai dai-dai yake da fashi da makami, kun balle kofa, sannan a cikin gidan kun saci miliyan goma sha biyar, don haka yanzu za'a tsareku har sai an kammala bincike".

Matasan nan suka yunkuro don aiwatar da wani abu, amma sai yaya usman yayi musu inkiya suka dakata.

RAMADAN SERIES 19

Chanjawar wannan dan sanda ta lokaci guda ya bawa yaya usman mamaki, don haka kawai saiya saki baki yana kallonsa.....

Laifukan da ake zarginsu da aiwatarwa sune abubuwan da suka fi razana shi, akan komai, zuciyarsa ta rinka bugawa da karfi, kai kace kogunan duniya ne suke ambaliya a zuciyar tasa saboda tsananin razana.

Firgita, razana, dimuwa, kaduwa, tsorata da dimauta sune abubuwan da suke ta rige-rige a zuciyarsa zuwa kwakwalwarsa.

"Kai yaro ba tunani nace ka tsaya yiba, tun muna shaida juna ka kawo miliyan Ashirin dinnan kafin fushin hukuma ya hau kanka".
Dan sandan nan ya katse masa tunaninsa.

"Haba mai gida dazu kuma miliyan sha biyar fa kace."
Wani a cikin matasan da suke tare da usman ya furta hakan.

"Da ni kake musu? Ko kuwa karyatani zakayi? Ko kuma nufinki nima macuci ne irinku?", Dan sandan ya fada cikin tsawa. Sannan ya juya ya kalli yan sandan kananu yace; "a tsare min su, sannan a koya musu hankali".

**        **         **        **         **

Kwance goje yake akan gadon asibiti inda akaqi karbarsa, sai anzo da jami'in tsaro kamar yadda doka ta tanadar.

Kasancewar gojen a wannan lokaci ya farfado ya kuma ga abinda ya faru dashi saiyaji gaba daya duniyar ma ta isheshi.

"A kwanakin da nake matashi ina ganin babu wani sai ni, ina ganin babu wanda ya isa ya sakani, koya hanani, ina aski irin wanda nake so domin in nunawa duniya cewa ni na gagara, ina saka kaya a yadda nake so, domin in nunawa duniya cewa babu wanda nake jin kunya, ina kuma furta kowace irin magana agaban kowaye, koma waye don in nuna cewa bana shayin kowa da komai..."
Goje ne yake furta hakan lokacin da yake kuka.... Yaci gaba da cewa...
"Ashe dama haka duniya take cike da bakin cikin da gurbatattun mutane? Nayi dana sanin bata shekaruna danayi a abinda bazai taba amfanar dani ba, yanzu gashi girma yazo inata kokarin barin hakan amma shi abin yaki ya barni.... Na janyowa ya'yana masifu, domin abin bazai tsaya iyakar kaina ba.... Shin idan Allah ya yafe min laifina tsakanina dashi, ya zanyi da laifukan al'umma..."
Goje ya sake fashewa da kuka.

Yaci gaba da cewa; "Hakkin yayana kuma me zan cewa Allah akai? Alhalin na shiririta da gurbataccen tunani yasa na kasa basu tarbiyya. Shin idan sun girma zasuyi alfahari dani a matsayin babansu tsohon dan daba ne ko kuma tsohon mashayi? Ko kuwa bakin ciki zasuyi da rashin sa'ar uba da sukayi?

Ya sake fashewa da kuka yana son yin magana amma ya kasa saboda karfin kukan.

Daya daga cikin 'ya'yansa ta qaraso kusa dashi itama tana hawaye sannan tace "Baba insha Allah babu abinda zai hana Allah ya gafarta maka, ni abinda nafi jiye mana shine, yadda wayannan mutane suka illataka haka suke kokarin illata zuri'arka domin fushin da suke dakai ya shafe mu..... Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un....".
Itama kuka ya sarketa ta damke hannun baban nasu wanda ba'a sare shiba.

A dai-dai lokacin ne kuma dattijo umar ya shigo dakin asibitin ya kalli goje yaga yanayin da yake ciki daga bisani yace "Ya banga an fara dubashi ba?
Ya kawar da kansa ga barin kallon gojen don hawaye ne suke zubo masa kawai.

"Sunce sai anzo da dan sanda"
Wani a wajen ya bawa dattijo umar amsa.

Cikin gaggawa dattijo ya fice.

Jim kadan saiya dawo tare da dan sanda.

Amma kash, sun makara domin goje rai yayi halinsa.

Kowa a dakin yayi tsit, inka dauke mata da suke koke-koke.

Dattijo umar yana tsaye ya rasa meke masa dadi. Sai kawai ga wasu matasa sun shigo a birkice.

"Lafiya?"
Dattijo umar ya tambaya.

"Su... Su... Usman ne an kamasu ana... ana... ta..ta du..dukansu"
Daya daga cikin matasan ya fada cikin kinkina.

"A ina?"
Dattijo umar ya tambaya.

Suka hada baki sukace "a ofishin yan sanda".

Dattijo umar ya tsaya kikam yana tunanin mafita, shidai yasan yanayin kasarnan waka-sanine-waya-sanka....

"Mai gida muje wajen kawata zainab".
Matarsa maryam ta fada cikin gaggawa. Sannan taci gaba da cewa "Mijinta babban dan sanda ne a kasar nan, kuma yana cikin masu gaskiya".

Ai kuwa ba shiri suka bar wakilai akan gawar goje, inda aka nufi gida da ita. Shi kuma dattijo umar da matarsa suka shiga motarsa sai gidan hajiya zainab.

RAMADAN SERIES 20

Dattijo umar ya wanzu yana sharara gudu a mota don zuwa gidan hajiya zainab, a kwakwalwarsa kuma yanata tunanin abubuwan da suke ta faruwa a gareshi a wannan yan kwanakin.

_Gashi anci biyu bisa ukun azumi, lokacin daya kamata ya koma ga Allah sosai, ya kara zage damtse akan ibada, amma lokacin ne yake ta faman gamuwa da matsaloli na rayuwa. Koma dai menene yasan Allah yana sane dashi...._

Ya katse tunanin nasa sakamakon karasowa da yayi kofar gidan hajiya zainab.

Cikin gaggawa matarsa maryam taje ta buga kofar gidan. Ba jimawa kuwa mai gadi yazo ya bude kasancewar ya santa bai tsaya yin wani bincike ba sai yayiwa dattijo umar inkiyar ya shigo da motar. Dattijo umar ya shiga da motar ya bude shima ya fito. Bisa ga mamakinsa saiyaga an bude kofar baya an fito....

Dattijo umar ya saki baki sannan yace "Aliyu dama kana cikin motar?"

Aliyu wanda idonsa yayi jajur saboda kuka ya gyada kai kawai, yana kebe baki kamar zai fashe da kuka.

Dattijo umar ya durkusa a gabansa sannan ya shafi kan dan nasa, ya sumbaceshi a goshi yace "Aliyuna kar kayi kuka kaji".

Aliyu ya gyada kai alamar ya karbi umarnin.

Kai tsaye maryam ta shige cikin gidan kafin jim kadan ta fito tacewa su dattijo umar suma su shigo.

Tun kafin su shiga dama maryam ta gayawa hajiya zainab abinda yake gudana. 

Don haka suna shiga bayan gaisuwa da kuma yi musu ta'aziyyar goje, da kuma jajen abinda ya faru gasu usman sai hajiya zainab ta umarci dattijo umar daya hau sama wajen mijinta don gaya masa abinda ke tafe dasu.

Ba musu dattijo umar ya hau sama zuwa dakin mijin nata mai suna Sanda.

Cikin fara'a suka gaisa, daga nan dattijo ya zayyano masa matsalar da take tafe dasu na neman a saki wayannan matasa da aka kama tare da hukunta ci-zali domin shine silar mutuwar goje.

Bayan dattijo umar ya gama jawabi sai Sanda yayi murmushi yace "Tabbas wannan mai sauki ne amma a baki, don kuwa a aikace yanada mutukar wahala, musamman ma tunda matsalar abin ya hadu da ci-zali, kasan kuwa saboda manya da yake tare dasu mu kanmu shayinsa muke....."

Dattijo umar yayi shiru yana nazarin maganar.

Sukayi dai yar doguwar muhawara kafin a karshe dattijo umar ya samu nasarar gano cewa tabbas abinda yake bukata ba zaiyiwu ba.

A sanyaye ya mike sukai sallama lokacinda Sanda yake ta bashi hakuri.

Yanayin yadda ya fito ne ya nunawa maryam da hajiya zainab cewa babu nasara.

Ba tare da hajiya zainab tace komai ba sai kawai ta taho har tana bangaje dattijo umar saboda sauri ta haye saman. Kasancewar jikinsa babu kwari ai kuwa tana bangaje shi saigashi yayi zaman dirshen akan matattakalar bene.

Aliyu da yake gefe guda ya kyalkyale da dariya.

Hajiya zainab kuwa tana shiga dakin mai gidanta sanda saita turo dankwali gaban goshi ta zauna ta bata rai.

_"Uwarhome_, lafiya naga kin bata rai?
Sanda ya tambayeta.
Ta turo baki sannan tace "Inafa lafiya zaku kashe min da".

"Subhanallah, a ina?"

"Ca nake yanzu ka gama yiwa babansa rashin mutunchi"

"Laaa ba haka bane wallahi kinsan abinne babu yadda zanyi saboda...."

"Kaga ni ba cewa nayi ka bani labari ba, so nake a sake su kawai idan kuma bani da wannan darajar a wajenka saika gaya min in san matsayina".

"Haba Zee baby,  kinsan kin wuce haka, kawai kinsan abubuwan ne bazasu yiwu ba"

"Ba wani na wuce haka a wajenka, kawai dai kace zakai min dadin baki".

"To ki bari zan kira ince a sake su, in yaso nasan abinda zan fada acan sama".

"Kaga mai gida babu inda zanje, sai dai kayi wayar nan a gaba na"

Sanda ya zazzaro ido, idanuwan sukai jajur daga bisani ya karya murya yace "To shikenan amma zaki sakani a matsala wallahi".

"Allah yana taimakon wanda ya taimaki wanda aka zalunta, don haka ruwanka yanzu kayi abinda Allah zai tamakeka ko kuma kakiyi ka gamu da fushina".

A sanyaye ya dauko wayar ya buga ya bada izinin a sake matasan.

Wanda ya daga wayar yace "kaii rufa min asiri, so kake ci-zali ya kashe ni?

Sanda cikin tsawa yace "Umarni na baka fa, bawai shawara nake nema ba".

"An gama oga".

Hajiya zainab ta tsaya jim kadan a dakin nasa sannan tayi murmushi tace "Yanzu ne nasan inada mai gida mara tsoro, an gaida jarumi".

Sanda yayi dariyar yake kawai ba tare dayace komai ba.
Amma a zuciyarsa kuka yake yi.

Bayan ya tabbatar ta fita, sai ya dauko wayar nan ya sake kiran wanda ya kira yace "Wayannan matasan kada a sake su".

"Tab oga ai an gama sakinsu, yanzu haka ma ci-zali ya taho zai sameka, don na gaya masa kaine kace a sake su".

Sanda sai kawai ya saki wayar kasa ya koma ya zauna yana mai dafe kansa.

**     **     **      **      **

Dattijo umar da maryam sukaiwa hajiya zainab godiya daga bisani dattijo yace "Wannan ci-zali baiji dadin halinsa ba, akwai hadisi daya tabbata cewa _mafi munin masauki a mutane ranar alqiyama shine wanda mutane suke gudunsa saboda alfasharsa_, ko kamar yadda Annabi yace.

Daga nan suka fito harabar gidan suna sallama.

Sai ji sukai an saka kafi an tura kofar daga bisani kuma wata mota ta sawo kai.

Mai gadi ya mike da sauri ya tari motar.

Sai kawai sukaga ci-zali ya fito daga motar yana muzurai.

RAMADAN SERIES 21

Ci-zali ya dakawa dattijo umar tsawa yace: "Kaii kamar ni insa a tsare mutane kaje kasa a sake su don kana takamar kana da wannan dan tsakon sanda?".

Dattijo umar zaiyi magana sai kawai jin sautin dan karamin yaronsa Aliyu yayi yana bada amsa yana cewa da karfinsa "Kai boss a gaban Actor kake wannan haukan? To ka gaggauta barin wajen nan tun kafin mamata ta dauko bulala wallahi..."

"Kai wanene?" Ci-zali ya tambaya.
"Ni yaro ne", Aliyu ya bada amsa.
"Dan gidan wanene kai?" Ci-zali ya sake tambaya.
"Dan gidan wani dattijo mara shaye-shaye" Aliyu ya sake bada amsar kai tsaye.
"Baka da kunya ko?" Ci-zali ya tambayi Aliyu.
"Kaima ai babana ya girkeka", Aliyu ya bashi amsa cikin sauri.
"Baka jin tsoro na?" Ci-zali ya tambaya cikin mamaki.
"Ai kai ba abin tsoro bane domin bakada ikon sauya abinda Allah ya rubuta", Aliyu ya sake bashi amsa.

Ci-zali yayi tsit, daga bisani ya juya ya kalli yaransa yace "Wai me kuke jira da shi ne? Karamin yaro sai ruwan rashin kunya yake min...."

Kafin su yunkura tuni Aliyu ya tari numfashinsu......
"Shin yanzu akan bin umarnin wani katon banza kun yarda ku sabawa Allah mahalicci? Kun yarda akan binsa ku bata mu'amalarku da Allah, da Manzonsa, da iyaye da jama'ar gari? Shin akwai abinda zai baku wanda Allah bazai baku ba in kuka yi masa biyayya? Ko kuwa kun raina arzikin Allah ne shiyasa kuke neman na ci-zali? Kuna tunanin a gobe kiyama zai iya tseratar daku daga azabar Allah? Ko kuwa kuna tunanin shi kansa zai iya tseratar da kansa?

Yaran ci-zali sukai jigum, aka rasa wanda zai motsa, can sai daya daga cikinsu ya durkusa kasa yana mai ajiye makamansa. Ai kuwa take ragowar sukai irin yadda yayi.

Ci-zali yana ganin haka ya nufesu da sassarfa da zummar hukuntasu ai kuwa sai babbansu ya tareshi suka fara kokawa da kicin-kicin.

Dattijo umar a guje ya nufesu da zummar rabasu, sai matarsa maryam rikeshi, tace "lallai mai gida an gaisheka, ka tsira da kyar kuma yanzu kana kokarin sake saka kanka a wahala".

Basu ankara ba sai ganin yan sanda sukai sun shishshigo gidan inda sukai musu kawanya.

Nan aka umarci ci-zali da yaronsa dasu daina wannan rigima, ai kuwa ba musu suka rabu. Koda yaron ci-zali ya koma da zummar shiga cikin yan uwansa sai kawai ci-zali ya faki idon wani dan lukutin dan sanda ya fizge bindigarsa ya saita wannan yaron nasa zai harbe shi.

Kamar daga sama sai gani akai an harbi ci-zali a goshinsa take ya fadi ya margaya.

Kallo ya juya daga inda harbin ya fito sai kawai akaga Sanda ne da wannan aikin.

Yansanda suka dauke gawar sukai waje da ita.

**        **        **         **         **

Kafin dattijo umar ya koma gida saida ya fara biyawa ta gidan marigayi goje, inda yayi musu ta'aziyya daga nan aka rashi kabarin goje yayi masa addu'a.

Saboda akwai gajiya a jikinsa anan bakin kabarin kawai sai bacci ya saceshi.

A cikin baccin sai yayi mafarki gashi cikin makabartar amma bisa ga mamakinsa saiyaga matattun sunata harkokinsu, wasunsu sunata shawagi a sama.

Sai ya hango wani mutum matattun sun kewayeshi ana hira, saiya nufi inda suke yayi musu sallama. Duk suka juyo suka kalleshi.

"Kai dan duniya filin wasa, meke tafe da kai?"
Wani cikin matattun ya tambaya.
"Ina sone a bani shawara akan rayuwar duniya".

Sai babban ya nuna wani yace "Kaine baka dade da barin duniyar ba, bashi shawara".

Wannan sabon mamacin saiya mike sannan ya fara da cewa "Ka kiyaye sallah, amma ka tabbatar tsarki yana tare da kai, domin Allah baya karbar abu sai mai tsarki, ka yawaita istigfari domin a cikin bautarma da muke yi a duniya kuma muke tutiya akwai kura-kurai... Sannan kayiwa mutanen kirki gargadi, hakanan kayiwa mutanen banza bushara".

Sai wannan sabon mamaci ya koma ya zauna.

Abinka da baban Aliyu, bakinsa baya shiru sai yace ban gane jimlar karshe ba. Ta yaya zanyiwa mutanen kirki gargadi alhalin sune na kirki, ta yaya kuma zanyiwa mutanen banza bushara alhalin sune na banza.

Sai wannan sabon mamacin mai kama da larabawa ya sake mikewa yace: Mutumin kirki ayi masa gargadi kada ya rinqa ji a ransa cewa yana tsinanawa Allah wani abu, domin baida tabbacin an karbi aikinsa ko ba'a karba ba, hakanan shi kuma mutumin banza ayi masa bushara cewa Allah mai karbar tuba ne, kuma mai gafara ne.

Mamacin ya sake komawa ya zauna.

Mallam dattijon arziki umar ya sake cewa  "Meyasa naga bakwa yawaita surutu?"

Sai duka matattun suka hada bakinsu sukace "Babu abinda mukayi dana sanin aikatawa sama da magana barkatai, domin zaka furta magana ka rainata alhalin mai girmace a wajen Allah, tabbas muna shawartarka daka rage surutu ka yawaita ambaton Allah, kaga azumi kuwa da kuke ciki yanzu da kunsan abinda muka sani tattare dashi da tuni kun roke Allah ya karbi ranku koda kuwa azumi guda da kukai ne karbabbe".

Firgigit ya farka daga baccin daya daukeshi.

Daganin kuma ya nufi asibiti don duba yaya usman domin ance saboda dukan da yasha a ofishin yan sanda yanzu yana can kwance a asibiti.

RAMADAN SERIES 22

Bayan dattijo umar yaje asibiti saiya tarar tuni ma an sallami yaya usman, don haka saiya biya ta gidan marigayi goje inda bayan yayi musu ta'aziyya saiya nemi yana so yaga babban dan gidan goje.

Aikuwa aka kirawo masa shi, yaji matukar mamaki daya ganshi saurayi matashi mai haiba, da alama addini ya ratsashi inda anan yayi masa nasihohi gami da sake jaddada masa cewa wannan shagon daya bawa goje zai dawo karkashin kulawarsa, don haka yayi kokari wajen ganin ya tafiyar da komai dai-dai, sannan kuma yayi kokari wajen hadin kan yan'uwansa.

Daga nan dattijo umar ya nufo gida inda da kyar ya shiga, mutane masu yi musu jaje sun cika kofar gidan.... Kai harma da yan jarida.

Bai samu nutsuwa ba saida rana ta tafi gab da faduwa.

A lokacin ya shiga gidansa ya zauna inda matarsa maryam take hada kayan shan ruwa.

Humaira da hanan suna wasu ayyukan dabam inda shi kuma Aliyu yake zaune tare da yayansa yaya usman suna wasa da dariya, abin dai gwanin sha'awa.

Dattijo Umar ya daga hannu sama yana mai zubar da kwallah yace "Allah hakika ni bawa ne mai zaluntar kansa, zalunchi mai yawa, kuma babu wanda yake gafarta zunubai sai kai, Ya Allah kayi min gafara... Ya Allah kaine ka azirtani da wannan zuri'a, ya Allah hakika kasan ina iyakar kokarina wajen tarbiyyantar da ita, ya Allah ka tarbiyyantar min da ita, ya Allah idan baka taimaka mana ba tabbas zamu zamo daga cikin asararru...."

"Baba daina kuka", Aliyu ya fada lokacin da yake share tasa kwallar. Sannan yaci gaba da cewa "Allah yana tare da kai a kowane lokaci".

Yaya usman da yake gefe ya tako yana dingishi kawai ya fada kan babansa ya rungumeshi yana fadin "Bani da wanda ya wuceka Babana, insha Allah bazan kara ketare maganarka ba, kuma daga yau zan baka mamaki ina mai tabbatar maka da cewa duk abubuwan da kace in bari a baya na daina...."

Dattijo umar ya godewa Allah.

Daganan suka taya matan aiki anayi ana nishadi da dariya har suka kammala suka sha ruwa tare suka mike yaya usman ya jasu sallar magriba don yaukam basu fita masallachi ba.

Bayan sun idar sai hanan tace "Muna sallar nan fa naji hayaniya a waje Allah yasa lafiya".

"Nima naji" humaira ta fada.

Adai dai lokacin ne kuma hayaniyar ta nufo  gidan da suke cike.

RAMADAN SERIES 23

Jim kadan sai dattijo umar yaji ana rafka sallama a kofar gidansa, ba shiri ya fita don jin wannan hayaniya da kuma jin abinda yake wakana da kuma fita don ganin mai yin sallamar.

Yana fita kuwa ya iske mutane ne birjik anata faman raha da fitarsa suka taso yuuu suka yanyameshi kowa yana miko masa hannu. Bayan sun gama gaisawa da mutane ne sai ya buqaci yaji abinda ke tafe dasu.

"Ba komai wallahi, dama cewa mukai bari mu duba muga lafiya baka halarchi sallah a jam'i ba, domin da wayonmu da yawanmu bamu taba ganin kayi rashin sallah a jam'i ba".

Dattijo umar kuma sai jikinsa yayi sanyi ya sunkuyar da kansa kasa daga bisani ya dago yana mai dubansu daya bayan daya  daga bisani idonsa ya ciko da kwalla ya bude bakinsa da nufin cewa wani abu amma sai magana ta faskara.

Sai jama'ar nan suka fuskanchi cewa sun sakashi a wani yanayi.

Wani tsoho a cikin mutanen mai yawan zolaya ya dan daki dattijo umar a kafada yana cewa "Dattijo mai shagwaba, kai kenan komai kuka... Kodai rako maza kayi ne".

Dattijo umar ya kyalkyale da dariya, suma ragowar mutanen wajen sai suka taya shi, haka aka tsaya anata faman hirarraki har lokacin sallar isha'i yayi suka dunguma suka je masallachi akai sallah tare daga bisani wani a cikinsu yasa aka kawo musu lemuka suka sha sukai hani'an sannan kowace gayya ta nufi inda gurin kwananta yake.

**       **       **         **         **

Masallachine a cike da mutane ana sauraron khudbah daga liman, akan sahun gaba zaka iske dattijo umar ne da kuma yayansa da sauran dattijai, yayinda akan mumbarin kuma mai gabatar da hudubar matashin saurayin nan dan gidan goje ne.

Yana cikin hudubar ne wani mutum ya shigo yana kukkutsawa ta cikin mutane...

"Bawan Allah ka samu waje ka zauna mana"
Saurayin ya katse hudubar yana mai yiwa mai shigowar magana.

"A gaba nake zama, yau kuma sai aka samu akasi na makara, alwala ma kawai nayi na taho".
Mai kotsuwar ya fada lokacin da yake kokarin zaunawa.

"Alwala kadai? Alhalin kasan Annabi yana umarni da yin wanka a ranar juma'a"
Saurayin limamin ya maida masa da raddi, daga bisani yaci gaba da hudubarsa.

Bayan an kammala anyi sallah sai halifa yake tambayar yaya usman "Dama in ana huduba liman yana iya yiwa wani magana?"

"Eh mana, An samu Annabi yana aikata hakan idan da wata larura sannan akwai athar daya tabbata shima sayyadina umar ya aikata hakan".
Yaya usman ya bada amsa.

Suka dunguma suka koma gida.

Shigarsu gidan keda wahala, sai dattijo umar ya kirawo yayansa dukansu da mamansu.

"Na godewa Allah daya azirtani daku, sannan ina mai sake godewa Allah daya shiryar min da ku, tabbas babu abinda zanyi wanda ya wuce godiya ga Allah da kuma tsayawa tsayin daka wajen baku tarbiyyar".
Dattijo umar ne ke jawabi.

Yaci gaba da cewa "Kawo i yanzu nasan kowannenku ya fara fahimtar mecece rayuwa, kuma yasan dai-dai yasan ba dai-da ba, nidai burina ku taimaka ku tseratar dani a wajen Allah, kun dai gani nayi iyakar kokarina wajen tarbiyyarku domin nasan za'a tambayeni akanku ranar gobe kiyama.... Daga nan yayi shiru yana mai rike kwallar idanunsa.

"Samun uba tamkarka abune mai mutukar wahala, tabbas muna godiya ga Allah daya bamu kai a matsayin mahaifi, kuma bazamu baka kunya ba har a gurin Allah insha Allah."
Yaya usman ne yayi wannan furuchi.

"Baba, muna sonka don haka bazamu so Allah ya kamaka ba akanmu, zamuyi iyakar kokari wajen ganin mun kula da kanmu".
Humaira da hanan kamar hadin baki suka hada baki suka furta hakan.

"Baba mai shagwaba, dama ni ai kaga abokinka ne ko? Kasan kuma aboki baya son ganin abokinsa cikin damuwa".
Aliyu ya fada lokacin da yake hawa kan cinyar babansa.

"Abban Hanan, kana kokari, kayi kokari, kaci gaba da kokari, tabbas kayi namijin kokari wajen zabo uwa ta gari ga yayanka, shiyasa nake jiye maka kada kace zaka kara aure ka auro wadda bata dace ba".
Matarsa maryam ta fada tana murmushi.

Gaba dayansu suka kyalkyale da dariya suka fada kan mahaifinsu dattijo umar harma da babar tasu maryam.

Shi kuwa ya dauko waya ya daukesu a hoto, dukansu  sun fito kuma sunyi kyau sosai.

Zamu tsaya anan.

Wannan shine karshen wannan series, sai kuma  a wasu rubuce-rubucen na gaba.

Tare da ni Naseeb Abu umar Alkanawy.
Don samun rubuce-rubucenmu sai a tuntubemu ta email Nasibauwal@gmail.com

Assalaam Alaikum warahmatullah.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.