Posts

Showing posts from July, 2018

ABOKIYAR ZAMA

"Kafin in kara aure ban fuskanchi wata matsala da uwargida ba, asalima ita take min kwalliya ko kuma ta zabo min kayan da zan saka idan ta fuskanchi zanje zance." Matashin mutaumin mai kimanin shekaru 35 yake fada a dai-dai lokacin da nake gab da shi a cikin keke napep. "Ranar daurin aure ma ita tayi min kwalliya, mukayi hotuna daga bisani na tafi wajen daurin auren, da safiyar washe garin daurin auren ita tazo har bangaren amaryar ta shirya mana kayan breakfast gamida wasu lemuka data ajiyewa amarya wanda ni banma san ta tanade suba...." Ya dan dakata yana mai lalubo hotunansa da matan nasa gamida da nuna mini. Yaci gaba da cewa; "lokacin da nakuda ta zowa amaryar, uwargidan ita ta kaita asibiti a motarta, bananan lokacin sai kawai waya tayo min tace amarya ta sauka suna asibiti kaza, dana je asibitin abinda na gani ya burgeni domin hatta yan'uwan amaryar duk yan kallo suka zama duk abinda ake bukata kafin suyi uwargida tayi... Hatta kayan da aka sanyawa