Posts

Showing posts with the label Tunatarwa

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

Image
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Hadisi yazo daga Mu'adh bn Anas, wanda imam Ahmad ya rawaitoshi da kuma Imam Tirmidhi (514) cewa "Annabi ya hana zaman Ihtiba'i (zaman hade gwiwa da hannu kamar yadda yake a hoton sama) yayinda liman yake huduba." Zaman ihtiba'i shi ne mutum ya haɗe ƙaurinsa da cinyarsa a zaune sannan ya kewaye su da hannayensa.  Wannan hadisi Imam Albaniy da wasu daga masu tahƙiƙin musnad sun ingantashi. Imam Nawawiy kuma da Ibnul Arabi sun da'ifanta hadisin tare da wasu malamai. (Tahzeeb Attahzeeb 4/258) Sai dai an samu cewa wasu daga cikin sahabbai sun yi irin wannan zama, yayin da liman yake tsaka da huɗuba, cikinsu akwai Abdullahi Bn Umar da Anas Bn Malik Allah ya ƙara yarda da su. Ibn Qudama cikin littafin Mugniy na sa, ya nuna babu laifi idan anyi wannan zama, harma ya nuna wannan itace fahimtar Ibn Musayyib, Hasanul Basariy, Ibn Sirin, Imam Malik da kuma Shafi'i da sauransu. Allah yayi musu rahama baki ɗaya. Ibn Qud...