Posts

Showing posts from February, 2022

ƘARYA

Image
ƘARYA. DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA ANNABIN RAHAMA SHUGABA JA GABA DA AHALINSA TARE DA SAHABBANSA DA WAYANDA SUKA BIYO BAYANSU DA KYAUTATAWA. NA SHAIDA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH KUMA ANNABI MUHAMMAD BAWANSA MANZONSA NE.  HAKIKA MAFI GASKIYAR ZANCE SHINE LITTAFIN ALLAH, KUMA MAFI ALHERIN SHIRIYA ITACE SHIRIYAR ANNABI MUHAMMAD (S.A.W), MAFI SHARRIN AL'AMURA KUWA SUNE WAYANDA AKA FARAR, KUMA DUKKANIN FARARREN ABU BIDI'A NE, KUMA DUKKANIN BIDI'A ƁATA CE. BAYAN HAKA, WANNAN WANI TAƘAITACCEN RUBUTU NE DA NAKE SO IN BIJIROWA YAN UWA SHI DON TUNATARWA DA KUMA FAƊAKARWA AKAN WANI MUHIMMIN ABU MAI GIRMA WANDA SABO DA SHI YA SANYA DA YAWANMU MUN DAINA GANIN GIRMANSA. BA WANI ABU BANE WANNAN FACE ƘARYA.  INA ROƘON ALLAH DA YA SANYA WANNAN AIKI YA ZAMO DON SHI AKAYI, YA KUMA KARƁI AIKIN, HAƘIƘA SHI MAI IKO NE MAI KUMA KARAMCHI NE. ƘARYA Ƙarya dai sananniyar aba ce, domin kuwa koda yaushe tana kaikawo a cikin mutane,

LALLAI AKWAI TAMBAYA DANGANE DA NI'IMOMIN RAYUWA

“Sa'annan kuma haƙiƙa lallai sai an tambayeku game da ni'imomi.”  Duk wata ni'ima ta shiga cikin wannan, don haka idan Allah ya yiwa bawa wata ni'ima to tabbas ya shirya amsa tambayoyi ranar alƙiyama akan wannan ni'imar. Cikin hadisi ingantacce riwayar muslim, Annabi Muhammad (S.A.W) da manyan sahabbansa da kuma mafi kusancin abokanansa (Abubakar da Umar) (R.A) yunwa ta fito da su, a ƙarshe suka samu abinci a gidan ɗaya daga cikin sahabbai mawadata, suka ci suka ƙoshi kuma Annabi ya basu tabbacin cewa sai an tambayesu dangane da wannan ni'imar. Idan har abincin da ba kai ka nemo da guminka ba za'a tambayeka to ni'imomin da akai maka na lafiya da ƙwarewa a wani fanni na rayuwa sune mafi aula da'a tambaya. Idan kanada ƙarfin tunani da hangen nesa to tabbas za'a tambaye ka akan wannan ni'imar. Idan kana da fasahar tsara rubutu to tabbas za'a tambaye ka akan hakan. Idan kana da balagar magana, ka iya yin magana wadda za'a fahimta kuma ka