Matan Aure a Musulunci: Hakki, Daraja da Kyakkyawar Mu’amala.
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. Kowanne abu ba cikakke ba ne, duk halittar da Allah ya yi babu kamar mutum, amma shi kansa mutum tara yake bai cika goma ba, a dabi'ance, lafiyance da addinance. To haka idan ka duba abubuwan da suke kewaye da mu, masu rai da marasa rai za ka iske kowanne yana da bangaren da ya cika yana da kuma bangaren da ya ke da tawaya. ALLAH Buwayi Gagara Misali shi kadai ne cikakke, kuma gwargwardon kusancin bawa zuwa ga Allah gwargwadon cikarsa, kimarsa da darajarsa. Shi yasa Annabin Rahama ﷺ ya fi kowa zama cikakke domin ya fi kowa kyakykyawar alaka da Allah Mai Girma. Idan muka dauki ayyuka da kuma tsarin rayuwa za mu iske cewa cike take da kalu-bale mai yawa, kuma cike take da misalai ga masu hankali na irin hanyoyin da ta bi ta dilmiyyar game da hallakar da wayanda suka daukaka sha'aninta, kamar kuma za mu ga ba ta bar na kirkin ba, domin kuwa kowa akwai irin matsalolin da ya yi fama da su, kuma ya ke fama da su, kuma zai yi fama da su a nan gab...