TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (1)



Waiwaye Adon Tafiya 

Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W).


SHIMFIDA

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaba (S.A.W), tare da Ahalinsa tsarkaka, da Sahabbansa masu girma. Tabbas al'ummarmu tana bukatar tarihin Annabinta, tarihi wanda zai zo mata da wani salo na haska mata abin da ta rasa, tarihi da zai zo da wata rariya ta tankade dukkanin wani abu wanda bai tabbata ba a cikin tarihin Annabinmu, tarihi wanda zai zo da wani salo na fito mata da darussan da suke cikin wannan rayuwa mai albarka... Zan iya cewa babu zamanin da musulmai suke bukatar sanin Annabinsu irin wannan zamani, sakamakon yawaitar suka ga janibinsa da kuma kokarin kore ayyukansa har a cikin musulmai ka samu wasu sune zaton cewa sukar tabbatattun abubuwa daga Annabin rahama shi ne ba shi kariya.

Sakamakon bukatuwar yan uwa ga sanin tarihin, na ga ya kamata in gabatar musu da ita tun daga abin da ya samu na lokacin Jahiliyya har zuwa inda Allah ya nufe mu da tikewa.

Tabbas jama'a suna bukatar sanin tarihi, domin kuwa da tarihi ne za su san asalinsu, da manufarsu, da kuma hanyar da yafi kamata su bi.


  •  Tarihin musulunchi yana bukatar inganci don tabbatar da abin da ya tabbata da kuma abin da a ka farar da shi.
  • Tabbas akwai canje-chanje a tarihi da wasu masu son zuciya su ka yi, duk don cimma wata manufa ta su. Wasun su cikin kungiyoyin musulmi wasunsu kuma cikin wayanda ba musulmi ba.
  •  Akwai labarai da kafirai ne suka kagosu su ka sanyasu cikin musulunci, daga baya kuma suke amfani da su wajen suka ga musuluncin.
  • Akwai labarai da ake jingina su da musulunci masu mutukar jan hankali, sai dai kash zunzurutun karya ce mara fa'ida, sai dai ma asamu batanchi ga musulunci a cikin wasu daga cikin labaran. Ko a tsara labarin ta hanyar da mai karatu zai ji haushin wani daga salihan magabata na kwarai.

Bisa wayannan dalilai Ni Abu Umar Alkanawy na ga dacewar dauko muku labaran sirah wadanda suka tabbata gwargwadon iko.

Na daga cikin dalilan daya sanya ni wannan rubutu...

Rubutun zai zo a mako (sati) sau daya. InShaa Allah.


Allah nake roko da ya inganta niyyata ya kuma karfafeni hakika shi mai karfafawa ne.



Tabbas Allah (S.W.A) ya aiko Annabawa zuwa ga al'ummatai kamar yadda Qur'ani ya ba mu labari.

Kowane Annabi idan muka kula akwai irin wahalar da ya yi ta fama da ita... Wannan kuwa jarrabawa ce daga Allah. Acikin Annabwa mafiya girma akwai Annabi Nuhu, Annabi Ibrahim, Annabi Musa da Annabi Isah (A.S) sun sha gwagwarmaya da mutanensu mutuka... Wasu Annabawan suka rasa rayuwarsu, wasu suka rasa iyalansu da duk abin da suka mallaka, wasu aka azabtar da su, wasu a kan idanuwansu zuri'arsu ta hallaka ba su da ikon shiryar da su ko taimakonsu. Ita shirya dama a hannun Allah ta ke.

Duk namijin kokarin da wani Annabi zai yi don kawar da shirka da kafurci amma bayan wucewarsa zuwa ga mahalicconsu sai labari ya sha bam bam, domin da an debi wasu shekaru ma su yawa sai mutane su sake sauka daga kan shiriyar da Annabin da ya wuce ya barsu a kai. Musamman ta hanyar kirkiro bidi'o'i na shirka, tare da mayar da addinin ya zama yana tafiya kafada da kafada da al'adunsu na maguzanci. Idan tafiya tayi nisa a karshe sai su cakuda littafan da Allah ya saukar da soye soyen zukatansu. A karshe sai ya zamana ba za ka sami ingantaccen littafi saukakke daga sama ba sai dai na karya ko wanda aka cakuda da son zuciya, da karairayi.
(Muhammad Rasulullah page 13, by Abul Hasan Ali Nadwi (English)).

Bidi'a tana nufin shar'anta wani abu a addini wanda Allah da Manzonsa ba su bada umarnin a yi ba, sannan a aikata abin ana da nufin neman lada a wajen Allah... Don haka bayan shudewar kowane Annabi sai mabiya su fara yin kari a kan abin da Annabin ya zo da shi, har ma su rinka nuna cewa ai suna aikata wannan aikin ne don neman kusanci ga Allah, daga nan zai zamana malamansu suna shar'anta musu wasu abubuwa wayanda Allah bai yi umarni da su ba, wannan shi ne mafarin kowace fitina. Dalilin haka sai shirka ta yawaita a koma bautawa malamai  ko an sani ko ba a sani ba, daga nan sai shirka ta ci gaba da yaduwa har ta gauraye ko ina. Wannan shi ne mafarin lalacewar kowace al'umma domin lalaci ya na farawa ne idan aka ki sallamawa Allah da manzonsa akai kokarin cewa bayan hanyar Annabawa akwai wata hanyar ta saduwa da Allah... Hakan kuma shi ya ke bayuwa zuwa ga bauta kala kala.


Kafin aiko Annabin Rahama lallai duniya tana cikin tashin hankali da tsananin duhu wasu suna bautar Gumaka, wasu rana, wasu wata, wasu wuta, wasu ruwa da sauransu. Addinai marasa asali da tushe sun  danno kai cikin duniya. Misali addinin Buddhism ya mamaye garuruwa tundaga India har zuwa central-asia. (Discovery of India P. 201-203, Muhammad Rasulullah P. 18)

Haka nan addinin Hindu ya mamaye nahiyarsu gaba daya (Hindu da Buddhist duk ma'abota bautar gumaka ne) a wannan nahiya (India) a sixth century [A.D. / C.E] sai da ya zamana akwai ababen bauta miliyan 33 (33 million) wayanda mabiya addinin Hindu suke bautawa.... (Muhammad Rasulullah p. 18)

A makkah a wannan lokaci a Dakin Ka'aba akwai gumaka guda 360. (Sahihul Bukhari)

Kowacce kabila ta nada gunkin da take bautawa. (Kitabul Asnam Ibn kalabi)

Sakamakon nisa da akai daga sakon annabta da kuma yawaitar shirka sai duhun zalunci ya mamaye duniya kwacen gida da mata da yaya ba wani bakon abu ba ne. In ba ka da karfi wanda ya fi ka karfi zai mayar da kai bawansa kuma duk abin da ka mallaka ya zama nasa, wulakanta mata da binne jarirai mata da muzguna musu shi ne abin da ya zama ruwan dare a wannan lokaci.

Mutane a wannan lokaci hankalinsu ya gushe basa bambamche mai kyau da mara kyau, sun bar bautar Allah sun koma bautawa zuciyoyinsu. Manyan dauloli suka rinka murkushe kananu cikin salon zalunci na musamman.


Duka wannan ina magana ne akan rayuwa kafin haihuwar Annabin Rahama, duk da dai akwai wasu tsirarun mutane da wasu daga malamai suke lissafosu da sunan cewa suna kan addinin hanifs kamar Warakat Bn Naufal, Usman Bn Huwan, Ziyad Bn Amr da Abu Anas.

Duk wannan abu da yake faruwa a duniya, Allah yana kallo kuma yana sane da kauce hanya da bayinsa su kai. Tabbas duniya tana bukatar agajin gaggawa. Don samuwar zaman lafiya a cikinta. Musamman a irin wannan lokaci da kowane sashe na duniya yake cikin duhun Jahiliyya

Shin kuwa akwai wanda zai iya dawowa da mutane hankalinsu su tuba su koma ga mahaliccinsu?

Kasance da mu sati mai zuwa don jin amsar a rubutu na gaba.

Comments

Popular posts from this blog

KNOWLEDGE AND ITS NEGATIVE EFFECT...

JAN HANKALI GA ƊALIBAN KIMIYYA

PUBLIC DANCE!!!