JAN HANKALI GA ƊALIBAN KIMIYYA

Sai yanzu na gane...

Na riski maganganun malamai da yawa da suke cewa "Qur'anin ba littafin kimiyya ba ne, littafin shari'a ne. Sai dai ana samun ilmin kimiyya a cikinsa a matsayin mu'ujiza..."

A lokutan baya sai in rasa menene hikimar yin wannan togaciya cewa Qur'ani ba littafin kimiyya ba ne. Yanzu kam alhamdulillah na gano wasu daga cikin dalilan da yasa malamai suke wannan maganar.


Ga kaɗan daga ciki.
★ Dalilin saukar da Qur'ani shi ne shari'a, don haka duk wani abu da za a samu a cikinsa koma bayan shari'a ne. Don haka, idan aka ɗauki ayar Qur'ani mizanin da za a fassarata da shi, shi ne mizanin mutanen da Qur'anin ya sauka a cikinsu (Sahabbai). Su kuwa Sahabbai ana samun bayanai akansu ne a cikin littafan sunnah ingantattu.
To ashe idan muka samu aya magabata sun fassarata da wata ma'ana, to ɗaukar abin da suka fassarata da shi, shi ne dai-dai. Maganar wasunsu daga ɓangaren malamai ko masana kimiyya tana iya biyo baya mutuƙar bata sauka daga kan abin da suka faɗa ba.

★ Wasu daga cikin masana kimiyya a ƙoƙarin su na fito da wasu ayoyin kimiyya daga Qur'ani sai su rinƙa sauya ma'anar wasu ayoyin zuwa yanda zai dace da binciken masana kimiyya. Sun manta cewa Qur'ani bai sauka don marawa kimiyya baya ba, ita kimiyyar sai dai ta mara masa baya don tabbatar da abin da ya zo da shi.

★ Masana kimiyya ko yaushe a cikin bincike suke, don haka biyewa bincikensu da ƙoƙarin lallai sai an mayar da Qur'ani ya tafi dai dai da kimiyyarsu kamar wani babban taku ne da zai jagoranci al'ummar musulmi wajen sassauya ma'anar littafin Allah kamar yanda waƴanda suka gabacesu suka aikata.

★ Waƴannan kaɗan kenan daga dalilan da yasa ake waccan maganar da na kawo a farko. Wanda yake karanta littafan kimiyya masu alaƙa da addini kuma yake cin karo da rubuce-rubuce a kafofin sadarwa na zamani masu magana akan alaƙar Qur'ani da kimiyya zai riski irin wannan da yawa.

Idan Allah ya ara mana dama da lokaci Insha Allah zamu buga misalai.

Abu Umar Alkanawy

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.