Posts

Showing posts from April, 2018

AUREN DOLE.

Wannan takaitaccen fadakarwa ce akan auren dole, hukuncinsa a addini da kuma shawarwari.... Mun tattara bayanan ne don amfanuwar Malamai, Dalibai, Iyaye, matasa da wasunsu. Aikin da mukai na dai-dai daga Allah ne, wanda mukayi na kuskure kuma dama mu yan Adam ne, muna rokon Allah daya gafarta mana. Ya kuma sanya littafin ya zama mai amfamarwa ne ga daukacin yan'uwa musulmi. Tare da mu Dan uwanku. Naseeb Abu Umar Alkanawiy. Da yar'uwarku. Shifaa khamis Adam. AUREN DOLE 0⃣1⃣ Tabbas soyayya jigo ce mai girma a zamantakewar auratayya. Shiyasa Allah da kansa yake cewa... "Yana daga cikin ayoyinSa ne, ya halitta muku matan aure daga rayukanku, domin ku nutsu zuwa gareta, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani." Rum:21 Hakanan Annabin rahama yake fada cewa "Banga abinda yafi dacewa da masoya biyu ba sama da suyi aure". Anan zamu gane cewa soyayya jigo ce a cikin aure kuma da itane aure