Posts

Showing posts from January, 2019

IYAYEN KO MALAMAN?

ƊALIBAN, MALAMAN KO IYAYEN? Rubutawar Naseeb Auwal (Abu Umar Alkanawy)                     Da Shifaa Khamis Adam    ★      ★       ★     ★       ★ Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin rahama, shugaban farare da baƙaƙe. Bayan haka. Taɓarɓarewar ilmin addinin musulunchi da kuma rashin ganin girmansa abune daya samo asali daga wasu abubuwa da zamu tattaunasu a wannan rubutu, kafin nan yanada kyau muyi waiwaye wanda ake cewa adon tafiya. WAIWAYE ADON TAFIYA Lokacin zuwan turawan mulkin mallaka, sun tarar da sarakuna na wancan lokaci suna kula da alarammomi da sauran dalibai masu neman ilmin addini, sa'annan masu ilmin ababen girmamawa ne da kuma girma da kima a idon mutane. Da dama daga cikin dalibai na wancan lokacin suna barin garuruwansu a kafafuwansu bisa jagoranchi ko goyon bayan mahaifansu zuwa wani garin don kwankwaɗar ilmi daga wani hamshakin malamin. Wayannan ɗalibai ana kiransu da Almuhajirun mutum daya kuma sai a kir