Posts

Showing posts from November, 2020

TSARABAR JUMA'A DAGA ABU UMAR ALKANAWY

Image
*Tsarabar Abu Umar Alkanawy*. (3) Lokacin Khalifancin Sahabi Abubakar (R.A) ya shugabantar da Khalid bn Walid, bayan Sayyadi Abubakar shi kuma sahabi Umar bn Khaddab (R.A) saiya cire Khalid (R.A) ya maye gurbinsa da Abu Ubaida bn Jarrah (R.A)... Ko menene dalili? Shaikhul Islam Ibn Taymiyya (R) yace “Shi Abubakar (R.A) mutum  ne mai sanyi mai sauki, saboda haka saiya shugabantar da Khalid (R.A) wanda mun sani cewa shi mutum ne mai tsanani. Shi kuma lokacin da Sahabi Umar ya hau Khalifanci, mutumne mai tsanani don haka saiya sauya Khalid ya shugabantar da Abu Ubaida (R.A) wanda shi kuma mutum ne mai sanyi... A tsari na shugabanchi haka akafi bukata a hada zafi da sanyi, kada a hada zafafa biyu sai tsaurin yayi yawa, hakanan kada a hada sanyaya biyu sai sanyi ko sakaci yayi yawa. Nace: Ka duba lokacin da Allah ya turo Annabi musa mana, saboda yasan yanada tsanani sai ya sanya masa dan'uwa mai sanyi wato Haruna (A.S). 

TSARABA DAGA SHEHU USMAN DAN FODIO

Image
*Tsarabar Abu Umar Alkanawy* Shehu Usman Dan Fodio yana cewa... “... Daga cikin bidi'o'i akwai addu'a bayan idar da kowace sallah ta wata fuska abar sani, itace liman ya rinka addu'a su kuma mamu su rinka amsawa da ameen, wannan bidi'a ce makruhiya a mazhabar imam malik, wasu malaman kuma sukace bidi'a ce mustahsana, wasu sukace bidi'a ce abar so.  Shehu Usman Dan Fodio yaci gaba da cewa... “...Sai dai abin da yake na asali shi ne kowane mutum yayi addu'arsa, sai dai fa ba a yi saɓani ba cewa ba a rawaito daga Annabi (S.A.W) yayi sallama daga sallah sannan ya ɗaga hannunsa yayi addu'a mamu kuma sukace ameen ga addu'arsa ba, hakanan ba a rawaito wani daga halifofinsa shiryayyu yayi haka ba, Gaba ɗayansu.  Shehu Usman ɗan Fodio bai tsaya haka ba sai ya ci gaba da cewa... “...Shi kuwa duk abin da Annabi (S.A.W) bai taɓa aikata shi ba, haka nan ko ɗaya daga cikin sahabbai. Babu shakka barin wannan abin shi yafi akan aikatashi... كتاب بيان...