Posts

Showing posts from December, 2017

GWAJIN HAUSA

Kana jin hausa ko kuwa har fahimtarta kanayi? Karanta don bawa kanka amsa. Daga Naseeb Auwal (Abu Umar) Tsananin tsantsar tsabagen tsayuwar tsayin daka da iyaye nagari suke wajen bada tarbiyya shine ya bambantasu da malalatan iyaye masu malalaciyar tsayuwa akan yayansu. Wawa da wawaso zuwa ga abinda turawan yamma sukai watsi-watsitsinsa yasa wasu suke kallon rayuwa da ido guda na bangaren hagu, yayinda jahilchi yayi bake-bake ya banke kishiyar idon hagun. Makarancin mutum wanda ya kammala karanta littafai dubu ko fiye da haka, zaka sameshi baida ilmin sisi bare ma ya bawa wani.... Yayinda zaka samu wanda ya karanta littafai cikin yatsun dake dauke a tafukan hannu na dama, zaka sameshi da ilmi harma yana iya gamsar da wani..... Tabbas tsakanin na farko dana biyu akwai banbanci tamkar tsakanin jirgin sama da kuma wanda ke kan laulawa a hanya mai gargada, kai bari madai zaka iya kamantashi da gajiyayyen yaron da yake rike da filfilwa yana rangaji da taga-taga kamar zai fadi. Sassa

FRUITFUL OR FRUITLESS ATTEMPT?

FRUITLESS OR FRUITFUL ATTEMPT? "Naseeb, That's a fruitless attempt" she said "... we are tired of your everlasting and never ending complaints about manyan yara"_. She smiled a little, her eyes and teeth gleamed in the dark. Sometimes silent is the best answer, that is why I kept silent, even though she said it jokingly, but I'm not tolerating this kind of mock in my business (Da'awa). Sometimes they used to say "We can't read your screed, but we like your thriller especially one of jatau's bag of magic". My long writing about religion is one I like most, and I could never convince them to read it all, and I knew they need it too much, but they didn't know. Their hubby and obsession always was watching films and reading useless hausa novels, like Hajjo gano of Aliyu kamal's hausa girl. Please brothers you must to keep an eyes on your sisters, but before you need to be a man of some knowledge and standing. "it's

Weighty Matters

WEIGHTY MATTER I am reluctant to write about weighty matters, which to write about you need to search thoroughly and think deeply. The weighty matter I am talking about is nothing more than relationship between people and internet. Internet; is a powerful means of spreading and getting information, it is also place to acquire more knowledge, it helps in learning many good as well as bad things, it is use for communication, sharing idea and connection, and contains maps, address and also plays a vital role in banking, buying, selling, entertainment and more. Unfortunately, most of our people deviate from the positive effects and rush to the other side, they're not benefiting their future which is begging them to do something good for theirselves, instead they normalize to use it negatively by sharing what is on their filthy mind just to problematized the societal situation and it give birth to social unrest, most of the time leading to gigantic uncontrollable problems... That's

Zuwa ga matasa

Zunzurutun tsananin tsantsar tsabagen tsagwaron rashin imani da wasu mazan suke nunawa a gidajen su na aure yana mutuqar bani mamaki. Matarka amana ce a wajenka, kuma za a tambayeka irin kiwon da kayi mata kamar yadda za a tambayeka irin yadda kayi sallah da azumi, kai bari madai tambaya akan hakkin mata yafi hatsari akan tambaya akan hakkin sallah da azumi da sauran bauta.... Sallah, azumi da zakkah duk Allah zai iya yafe maka idan baka yi yadda ya dace ba, amma ka sani hakkin wani Allah baya yafewa...... Ka daukota, ka rabata da iyayenta, ka rabata da gidansu ka kawo ta naka wulakantaccen gidan kuma a haka ka mayar da ita baiwarka, baiwar ma mara yanci mara kan gado duk a tutiyar cewa kaike shugabantarta.... Kuma Allah ya wajabta mata tayi maka biyayya..... Kaje waje kaci abinda kake so, nan kuma ka barta da wulakantaccen lamin abinci wanda bazai gina jiki ba, Dan karfin dayake dashi zai taimaka ne kawai wajen toshe wata bazawarar yunwa da take fama da ita. Ba ruwanka da lafiyart

Halin ko in kula.

Illar rashin kula da tarbiyya da ilmin yara. Iyaye da dama suna mutukar kokari wajen bawa yayansu tarbiyya, saidai kuma kash , suna nuna halin ko in kula ga rayuwar yara marasa galihu basa tunanin cewa yaransu da suke bawa karatu da kulawa da tarbiyya suna fuskantar kalu-bale da yawa anan gaba a rayuwarsu ... Tabbas wayannan yara da ba a bawa tarbiyya ba, indai suka girma tabbas zasu addabi wayannan yara da aka ilmantar domin kuwa dole dai tare zasu rayu , ba za'a raba musu duniya ba. Tamkar kashi ne idan aka yishi a cikin aji, sai wari ya dami mutanen cikin ajin, sai aka bukaci yan aji dasu kawar da wannan kazanta don a daina jin wannan warin ko za a sarara, sai kawai wasu sukace su iyakar kashin bangarensu zasu kwashe.... Alhalin kuwa akwai kashin bajaja a ko'ina. Shin kana tunanin in suka kwashe iyakar kashin bangarensu zasu daina jin kashin cikin aji? Ko kuwa sai an hada karfi da karfe an kwashe na ko'ina ? Sign Abu Umar A