GWAJIN HAUSA

Kana jin hausa ko kuwa har fahimtarta kanayi?
Karanta don bawa kanka amsa.

Daga
Naseeb Auwal (Abu Umar)

Tsananin tsantsar tsabagen tsayuwar tsayin daka da iyaye nagari suke wajen bada tarbiyya shine ya bambantasu da malalatan iyaye masu malalaciyar tsayuwa akan yayansu.

Wawa da wawaso zuwa ga abinda turawan yamma sukai watsi-watsitsinsa yasa wasu suke kallon rayuwa da ido guda na bangaren hagu, yayinda jahilchi yayi bake-bake ya banke kishiyar idon hagun.

Makarancin mutum wanda ya kammala karanta littafai dubu ko fiye da haka, zaka sameshi baida ilmin sisi bare ma ya bawa wani.... Yayinda zaka samu wanda ya karanta littafai cikin yatsun dake dauke a tafukan hannu na dama, zaka sameshi da ilmi harma yana iya gamsar da wani.....

Tabbas tsakanin na farko dana biyu akwai banbanci tamkar tsakanin jirgin sama da kuma wanda ke kan laulawa a hanya mai gargada, kai bari madai zaka iya kamantashi da gajiyayyen yaron da yake rike da filfilwa yana rangaji da taga-taga kamar zai fadi.

Sassaukar sanayya tsakanin ido da haruffa yana shigar da bayanai zuwa ga kwakwalwa da zuciya, wayannan bayanai kuwa zasu haskaka rayuwa da bata hanya wadda ta dace.

Meka fahimta ga wannan rubutu?

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.