Posts

Showing posts from June, 2020

Majalisar Mallam Jatau

0️⃣1️⃣ Sakamakon kowa yana zaman gida, hakan yasa majalisar kullum take cike da mutane tare da cewa ba wani yawan kirki ne dasu ba. Domin a unguwar akwai wayanda suka yarda dasu killace kawunansu kamar yadda gwabnati ta bukata, wasu kuma suna fita don yin harkokinsu. Amma shi mallam jatau da wasu tsirarun mutane sai suka zabi cewa zasu rinqa zaman majalisa da tattauna matsalolin rayuwa na yau da kullum. Ranar farko abinda aka fara tattaunawa shine matsalar gidan aure.  Inda a karshe matsayar da suka samu shine; ana samun matsala bayan aurene saboda irin soyayyar da ake nunawa a waje kafin aure ba a nuna koda makamanciyarta a gidajen aure. Don haka sai mallam jatau yayi musu huduba a ciki yake cewa _Kamata yayi ku rinqa taya matanku ayyukan gida da rainon yara da girki........_ yayi musu bayani sosai suka gamsu. Bayan majalisa ta tashi. Mutum na farko ya koma gida, shigarsa keda wuya ya iske matarsa tana harhada kayan shan ruwa. Yana ganinta yayi murmushi yace “Zee baby” Ta dago cikin m

INGANTACCIYAR MAGANA AKAN SIFFOFIN DA AKE SIFFANTA ALLAH (S.W.A) DA SU.

INGANTACCIYAR MAGANA GAME DA SUNAYE DA SIFFOFIN ALLAH. Babu wanda yasan hakikanin siffofin Allah da sunayensa sai shi ubangijin daya barwa kansa sani...... To in kuwa hakane babu wata siffa wadda zamu yarda da cewar ta Allah ce sai wadda muka san cewa daga gareshi take.  Mun kuwa san cewa babu wani abu daga Allah wanda ya wuce Qur'an da hadisi. In mun yarda da hakan to a Quran da hadisi kawai zamu dauko siffofi da sinayen Allah.... Wanda kuma yayi da'awar cewa shima yasan wasu wayanda babu su a Qur'an ko sunnah to saiya zo da hujja bayyananniya...... Dangane da maganar sunaye da siffofi gaba dayansu zamu iya rabasu zuwa kamar gida hudu. 1. Abinda Allah ya tabbatarwa da kansa, kamar ji, gani, ilmi da izzah. 2. Abinda Allah ya korewa kansa kamar rauni, nakasa da bacci. 3. Abinda Allah bai magana akansa ba amma saboda abin yana nuni da rauni dole a koreshi ga Allah. Kamar bakin ciki da kuka. Akwai bambanchi tsakanin fushi da baĆ™in ciki. Shi fushi anayinsa ne akan abin da ake d