Majalisar Mallam Jatau


0️⃣1️⃣

Sakamakon kowa yana zaman gida, hakan yasa majalisar kullum take cike da mutane tare da cewa ba wani yawan kirki ne dasu ba. Domin a unguwar akwai wayanda suka yarda dasu killace kawunansu kamar yadda gwabnati ta bukata, wasu kuma suna fita don yin harkokinsu. Amma shi mallam jatau da wasu tsirarun mutane sai suka zabi cewa zasu rinqa zaman majalisa da tattauna matsalolin rayuwa na yau da kullum.

Ranar farko abinda aka fara tattaunawa shine matsalar gidan aure. 

Inda a karshe matsayar da suka samu shine; ana samun matsala bayan aurene saboda irin soyayyar da ake nunawa a waje kafin aure ba a nuna koda makamanciyarta a gidajen aure.

Don haka sai mallam jatau yayi musu huduba a ciki yake cewa _Kamata yayi ku rinqa taya matanku ayyukan gida da rainon yara da girki........_ yayi musu bayani sosai suka gamsu. Bayan majalisa ta tashi.

Mutum na farko ya koma gida, shigarsa keda wuya ya iske matarsa tana harhada kayan shan ruwa.

Yana ganinta yayi murmushi yace “Zee baby”
Ta dago cikin mamaki ta kalleshi sai kawai ta kebe baki taci gaba da aikinta.

Yaji babu dadi amma sai kawai ya basar ya zauna. Yana nazarin yadda take aikin tare da tunanin ta ina zai tayata.

“Baban mukhtar, kasan dai bana son kallo, kuma kazo ka kafeni da ido kamar wata telebijin.....”
Mai gida yayi shiru yana jinjina abin a ransa. 

Bayan ansha ruwa ta zubo masa abinci kai tsaye yaje wajenta ya zauna ya debo abincin zai bata a baki.

Tayi maza taja da baya tana rafka salati.... “Wai Baban mukhtar menene haka? Babba dani zaka wani bani abinci kamar wata karamar yarinya... Kaga babu takura bari na koma dakina."

Ai kuwa saita kwashi kwanonta ta barshi anan yana mamaki.


0️⃣2️⃣

Mutum na biyu shima ya nufi gidansa yanata sake-saken abin da zaiyi don farantawa matarsa, don haka a hanya ya tsaya ya sayi kayan marmari ya tafi dasu.

Matarsa tana dakin girki tana girki tare da kallon wani video a wayarta tana dariya... Sai kawai taji sallamarsa, ai kuwa tayi tsaki ta katse video din game da murtuke fuska...

Tana jinsa yana tambayar yaransu "Ina maman taku?"

"Tana kitchen" babbar yarsa ta amsa yar kimanin shekaru shida.

Kai tsaye ya nufi dakin girkin, ai kuwa yana shiga suka hada ido ya saki wani tattausan murmushi yace "Yammata sannu da aiki"

"Uhm, yawwa" ta amsa masa a ciki-ciki.

"Miko min wukar nan ta kusa dake" mijin ya fada cikin saurin baki.

Matar ta zazzaro ido tace "lafiya?"
"Babu komai, kawai zan tayaki aikin ne yau"
Ta kebe baki ta kalli shi sannan tace "Yau kuma? Kaga mallam don Allah ka tafi daki idan na gama girkin zansaka yara su kawo maka, ni nace kaje waje ka dade har yunwa ta koro ka? Zaka wani zo ka azalzaleni"

Kalmomin sun masa daci amma sai ya danne, kawai ya tsira mata ido lokacin da take kyasta ashana, a zuciyarsa kuma yana tunanin abin da zai mata ya rama.... Ai kuwa sai akaci sa'a ashanar nan ta karye ba tare data kyastu ba..... 

"Yanzu fisabilillahi wanne irin almubazzaranchi ne wannan? Ace ashana bazaki iya tattalata ba? Yanzu wannan data karye shikenan anyi asara kenan, zanyi maganinki aure zan qaro in yaso yarinya qarama sai tazo ta koya miki kyasta ashana"

Matar ta saki baki tana kallonsa, idonta ya dan kada kadan, daga bisani tace "Tunda na ganka a kitchen nasan cewa shirme zakai min wallahi.... Kuma aure ai kofa a bude take qarewa inka tashi ka auro dubu, saidai ina tayasu jimamin samun miji irinka.......

Mai gida zaiyi magana saiya tuno wa'azin mallam jatau sai kawai yayi shiru, ya danne zuciyarsa. Daga bisani ya dauki ashanar ya kyasta mata sannan ya dauki tukunya ya dora, duk akan idonta, ita kuwa tana cike da mamaki, a zuciyarta kuwa tana tunanin ko ba'a hayyacinsa yake ba, domin ita dai tasan bai taba shigowa kitchen ba tunda suke da ita, amma yau gashi harda dora tukunya........

"Mai gida nifa ban gane ba" 
"Menene baki gane ba"
"Wani abin zaka girka ne"
"Ko kadan, kawai tayaki aikin nake yi, kuma duk sanda nake available ma zan rinka tayaki"
"Wai da gaske kake ko kuwa gadar zaren daka saba shirya min zaka shirya?"
"Addu'arki ce Allah ya karba yau"
"Wacce kenan, mai gida?"
"Addu'ar miji nagari mana"

Matar tayi dariya tace "Allah yasa.


0️⃣3️⃣

Mutum na uku.

Cikin gaggawa ya shiga gidansa, ko cikakkiyar sallama bai yiba yana zuwa ya ajiye kujera a gaban kayan wanke-wanke ya zauna ya janyo ruwa kusa da shi...

"Talatu..." Ya kwalawa matarsa kira. 
Ta amsa tana mai fitowa daga daki, ta saki baki tana kallon ikon Allah.

"Miko min omo" ya gaya mata cikin tsawa-tsawa.
Jiki na rawa ta dauka ta mika masa. Ta koma bakin kofa ta tsaya tana jiran taga yayi wani yunkuri ta gudu, don dai tasan ba kalau yake ba da alama.

Ya daka mata tsawa yace ta matso inda yake.

Jikinta na rawa ta matso, zumbur ya mike daga kan kujerar daya zauna ya kamata da karfi ya zaunar shi kuma yayi zaman dirshan a kasa.

"Baban salele, wai lafiya kuwa?"
"Lafiya kalau, wanke wanke zamuyi" ya fada yana dariya.

Ta danyi murmushin karfin hali tace masa "Tohm".

A fakaice kuma tana neman hanyar guduwa ta fice daga gidan ta kira makota suzo suyi gaba dashi.

Suka fara wanke-wanke, yanayi mata wake-wake...

Ai kuwa data faki idonsa saita mike ta fice da gudu daga cikin gidan.

Shi kuwa ya tsaya yana mamaki. 

Jimawa kadan sai gata tare da liman da manyan unguwa. 

Suna shigowa suka ganshi zaune kasa zaman dirshan yana cuda kwanuka da ganin haka sai liman yace "lallai mallam garba babu lafiya" liman ya fada yana mai jinjina kansa.

Mallam garba ya mike tsaye ya kalle su, yace "Haba liman, mallam jatau ne yayi mana nasiha akan kyautatawa mata....."

Wani cikin yan rakiyar liman yace ai yanaga ayiwa mallam garba rukiyya kawai.

Mallam garba ya saki baki yace "Bafa hauka bane, ba kuma aljanu bane, soyayya ce wallahi"

Liman ya kuma gyada kai, yace lallai mallam garba an tabu.

Katti suka rirrike mallam garba, shi kuwa yanata kicin kicin yana ta maimaitawa "Soyayya ce liman, wallahi soyayya ce"

Su kuwa tsammaninsu salon haukan nasa ne yazo da haka......


0️⃣4️⃣

Mutum na hudu cikin daliban mallam jatau, bayan tashinsa daga majalisa saiya nufi gidansa a zuciyarsa yanata sake-saken abinda zai aikata a gidansa, tabbas yasan cewa kai tsaye yajewa matarsa da wani bakon al'amari da bai saba ba, bai zama lallai ta gane kota fuskanta ba.......

Yana shiga gidansa, yayi sallama yana mai kutsa kai, matar ta kalleshi daga sama zuwa kasa ta amsa tana mai ci gaba da tsintar shinkafar da take. 

Ya zauna ya fuskanceta lokacin da itama ta dago kai ta kalleshi tadan dakata da tsintar da take.

Yayi murmushi ya kalleta yace "Tabbas a lokacin da nake neman aurenki mun sha gagarumar soyayya, ban taba zaton aurenmu zai zamo haka ba, ace bama wuce sati guda sai mun samu sabani kuma abu kankani zai iya hadamu....." Matar kawai ta kafeshi da ido tana kallonsa. Yaci gaba da cewa "Duba kiga yau abin kunya, akan burodi kike jin haushina har yanzu....."

"Kaga mallam, nasan bukatar kanka ce ta kawoka.... "
"Ashsha, ai kinji matsalata dake, baki tsaya kin fahimchi inda na saka gaba ba, so nake zaman aurenmu ya zamo zama mai inganchi maimakon mu rinqa baqantawa juna rai me zai hana mu rinka farantawa juna rai? Shin idan mukai hakan mu kanmu ba zamu fi jin dadi ba....."
Matar ta kalli cikin kwayar idonsa, taga cewa tabbas da gaske yake, ta kuma sake tabbatarwa da cewa idan harshe yana furuci to tabbas idanu ma sunayi, kuma idanu basa iya bayyana abinda yake na qarya.

"Mai gida ka tuna nasihar da shehin malami yayi mana kafin muyi aure mana, wallahi daka bibiyeta da babu abinda zamu samu na daga matsala....."
"Uwargida kenan, na tuno da wata maganarsa da yake cewa *Ita mace ko matar mutum kamar farar takarda take babu rubutun komai a jikinta, sai abinda mijin ya rubuta...* Abin nufi duk wani abu data aikata to wannan mijin shine ya bada hanya ga aikatawarta....." Mai gidan ya danyi murmushin karfin hali sannan yaci gaba da cewa "...Idan zakiyi adalchi, nikam ban bada dama kiyi irin wayannan abubuwan da kike yimin ba, yanzu gashi shekara biyu amma mun zama fadanmu yafi shirinmu yawa...."

Matar tayi shewa, sannan ta kawar da shinkafar da take gyarawa gefe guda sannan tace "Laifinka na farko kenan, kai bazaka taba yarda kayi laifi ba, kullum kaine akan dai dai. Sannan tunda ka aureni ka daina bani kulawar da kake bani lokacin da muke matsayin saurayi da budurwa, to don me nima zanci gaba da baka irin waccan kulawar? Nayi tsammanin idan mukai aure soyayyarmu karuwa zatai, amma kalmomin soyayyar da kake min sai suka juye zuwa kalmomin hantara da habaici..... Sannan idan yan'uwana suka zo bayan gaisuwa baka damu da basu kulawa ba... Idan zaka sakani aiki baka sakani da tattausan lafazi, ni kuwa tunda ba baiwarka bace dole in maka aikin yanda naga dama....  Kuma baka jin nauyin fadar laifin iyayena a gabana, koda sunyi laifin ai kunyar zama dani saika ki ambatar laifin a gabana, amma zakai musu haka kayi tunanin nima zan saurara maka?"
Ta dan bata rai saboda ganin yana daga mata hannu alamar tayi shiru.

"Kema kulawarki gareni kafin aure tafi yawa ai, ko kuwa kin taba kirana bayan na fita aiki kince min kin kirani ne kawai kiji lafiyata, muryata ko wanin haka? Sannan babu abinda zan miki in burgeki, idan na kawo miki abu koda kinyi murna to tabbas kina gamawa saikin aibata abin, kodai kice yayi tsada in daina siyowa in rinqa baki kudin ki siyo da kanki, ko kice kalarsa bai miki ba, ko kice ke bkya son saka abinda ake yayinsa ko wani abu makamancin wannan. Sannan kema har yanzu kina daukar yan'uwana a matsayin kishiyoyinki ba yan'uwanki ba...." Ya danyi shiru yana tunani daga bisani yace "kai idan zan zayyano miki laifukanki ai sai a shekara ban gama ba".

Ta kebe baki tace "Ba zaka chanja hali ba wallahi, ni dai yanzu tunda kazo da gyara na yafe maka kuma da fatan nan gaba zamu cigaba da tattauna irin wayannan matsalolin don fahimtar juna".

Yayi mamakin yadda yaji da wuri tayi abinda yake so, da kansa ya tuno wasu abubuwa da yayi mata don ramuwar wasu laifuka da tayi masa, ya kuma tuna duk girman wayannan abubuwa da yayi mata yanzu gashi ta yafe masa a kasa da minti biyu... *Tabbas da gaske ne tsakanin ma'aurata akwai soyayya da jin kai*..... Zuciyarsa ta gaya masa bai san lokacin da kwalla ta fara kwararowa daga idanuwansa ba.


0️⃣5️⃣

Mutum na biyar cikin jerin daliban hamshakin malami jatau nufar gidansa yayi yana tafe da radio a hannunsa ya ware labarai yana ji, jefi-jefi kuma idan yaga wayanda ya sani yana tsayawa ya gaishesu cikin hayaniya, raha, kakaci da shewa.....

Da shigarsa gidan saiya iske matarsa tana shara, nan take tunanin shawarar mallam jatau ta taya mata aiki tazo masa aikuwa saiya dubi sharar da take, a zuciyarsa kuma ya rasa ta wacce hanya zaibi ya tayata..... Can sai kawai wani tunanin yazo masa ai kuwa saiya fara magana, wanda dama maganarsa kamar hargowa take.

"Wannan wacce irin shara ce?"
"Allah ya kyauta, ka dawo za'a fara kenan."
"Daga abin kirki sai kuma takalar mutum da fada..."

Bata bashi amsa ba kawai taci gaba da shararta tana rera waka _Allah sarki duniya wata rana komai na wucewa, dadine ko wuya duk wata rana suna wucewa, muyi amfani da dama in ta wuce ba zata dawo ba....._ 
Wuf taji an dagata an ajiyeta a gefe, mai gidan nata ne, yana ajiyeta ya kwace tsintsiyar daga hannunta ya fara shara, yana tafiya yana barin baya da kura........

Bayan ya tattara, sai kawai ya kalleta duk yabi ya hada gumi, yayi murmushin karfin hali yace "Dauko min zani"

"Mai gida? Zani fa kace"
"Kefa dadina dake gardama, nace ki dauko min zani mana"

Ta shige daki tana tunanin abu biyu, kodai mai gida ya zama dan daudu ko kuma wulakanci zai mata ya kwashe sharar a cikin zaninta. Don haka saita tsaya tana yanke shawarar meya kamata tayi..... Tana cikin sake-sake taji ya sake kwalla mata kira "Kande wai bazaki dauko min zanin bane?"
"Baban nalami ina zuwa" ta ambata lokacinnda take tahowa da zani a hannunta.

"Kinsan me zanyi da zanin nan?" Ya tambayeta.
"A'a" ta bashi amsa.
Yayi dariya yace "Goyaki zanyi yau, kuma duk inda kike son zuwa a fadin unguwarnan saina kaiki, tunda mallam yace su mata kulawa suke so, to ni kuwa nasan babu kulawar data wuce a goya mutum saboda tsananin gatansa a yawata dashi...." Ya kara sakin wata dariya lokacin da yake baje zanin a gadon bayansa.

Matarsa ta saki baki tana ganin ikon Allah, daga bisani ta samu bakin magana "Ni dai na gode, amma ba za'ai wannan shirmen da ni ba."
"Matsalar yar kauye kenan wallahi, ke dai banga sanda zaki waye ba, to ina gaya miki a turai, mutum saiya dauki matarsa ya goyata ya zagaye gidan yan'uwa da abokan arziki kuma babu abinda ke jawo hakan sai so da kauna...."
"Mu kuma hausawa ne ai, idan soyayyar zaka nuna saika nuna min ta fuskar yanda hausawa suke nunawa, kamar wadata gida, sutura mai kyau, kula da nuna kishi a kaina, kokarin gyara tsakanina da mahaliccina, biyamin bukatuna wayanda basu ci karo da koyarwar addini ba, tsayawa don bani kariya, nuna cewa kana alfahari dani, gyara min kura-kuraina ta hanyar hikima da tattausan lafazi, rashin hantara da cin zarafi da kuma karbar laifinka idan kayi laifi.... Kasan wani abu ma kuwa?"
"A'a sai kin fada"
"Da yawan maza bakwa karbar laifinku idan kunyi laifi, wannan yake sanya zuciyar wasu matan kekashewa da rashin karbar laifi koda kuwa su sukai laifin domin basu ga abin koyi mai kyau daga gareku ba. Shi kuwa zaman aure idan akace babu wanda zai karbi laifi to bazai taba zama mai inganchi ba. Amma da ace idan namiji yayi laifi zai bawa matar hakuri koda ta fuskar wasa ne to da ina tabbatar maka da cewa ita kanta duk sanda tayi laifi baza taji nauyi ko girman kan bashi hakuri ba."

Mai gida ya saki baki yana kallonta yace "Shegiya, wallahi kinfi mallam jatau hankali"
Cikin wasa ta daga hannu kamar zata dakeshi tace "Wacece shegiyar?"

Mai gida ya rufe fuska da hannayensa yadan risina cikin barkwanchi yace "Yayata ayi hakuri" 

Yayansu da suke gefe suka bazamo suka rungume iyayensu......

★.      ★.       ★.    

Washe gari daliban mallam jatau suka hallara a majalisa don bada labarin abinda ya wakana a gidajensu.

0️⃣6️⃣

Daliban mallam jatau sunyi jugum a majalisar mallam suna jiran fitowarsa daga gida. Jim kadan sai mallam ya fito sannan ya samu waje ya zauna bayan gaisawa da yayi da su daya bayan daya.

"Ina garba?" Mallam ya tambaya lokacin da yake kokarin zama akan kujerarsa.

Dalibai wannan ya kalli wannan, wancan ya kalli wannan. Daga bisani cikin karfin hali daya daga cikinsu yace "Allah ya gafarta mallam, ai garba babu lafiya don yanzu haka yana gidan liman a daure..."

"Subhanallah, amma kuka zauna anan? Ku tashi muje muga abin da yake damunsa."
Mallam jatau ya furta yana mai kokarin tashi daga kan kujera, garin sauri ya zame ya fadi amma sai yayi ta maza ya mike yana mai tattare babbar rigarsa. 

Yayi gaba dalibai suna binsa a baya. Haka sukaita tafiya har gidan liman. Da zuwa suka turawa liman sako cewa sun zo, kuma ga abin da ya kawo su. Ba a dauki wani lokaci ba sai ga liman ya fito tare da mallam garba daure hannu da kafa......

"Yawwa mallam, ka gaya musu wallahi lafiyata kalau soyayya ce, daga ka taya mata aiki sai ace ka haukace?"
Garba ya ambata yana fada.

"Ya danganta da irin aikin daka tayata da kuma sigar da kabi ka tayata aikin." Liman ya fada yana mai kallon kwayar idon mallam jatau. Sannan yace "kai kaje kace musu su rinka hauka a gida suna shirme ko?

Mallam jatau yayi dariya sannan ya dubi liman duba mai cike da ilmi yace "Ko kusa alaramma, bance musu komai ba, face su kyautatawa matansu, su zamo masu kai zuciya nesa sannan idan da dama su rinka taya matansu aiki...."

"Nayi rantsuwa da ubangijin Annabi musan haruna, ba haka kace mana ba."
Mallam garba ya fada cikin fada yana kallon babban malami jatau. "Cewa fa kayi mu rinka taya mata aikin gida kuma baka ce mana idan da dama ba......."

Liman ya saki wani murmushi yace "Mallam jatau, kaima abin tuhuma ne."

"Amma da mamaki kamar kai liman ka dauki maganar mahaukachi a matsayin hujja."
Mallam jatau ya fada.

Mallam garba ya kara fusata, ya zaburo zai turmushe mallam jatau.... Liman ya rirrikeshi amma inaa yafi karfin liman, da kyar dai aka harhadu aka rirrikeshi yanata maganganu "kai ka koya mana soyayyar nan, kuma mun yita a aikace amma har kai za'a rinka ce mana mahaukata........"
Jama'a kuwa suka rinka dariya don ganin yadda ya hakikance. 

Ta karfi aka kamashi aka zaunar, cikin hikima mallam jatau ya karasa inda yake yayi masa rada "Ka nutsu kabar wannan surutai ko zamu samu damar tafiya da kai, mutukar kace zakaita fada to tabbas kowa zaici gaba da zaton cewa akwai matsala akanka"

Bayan yan tambayoyi da aka yiwa mallam garba da gwaje gwaje sai aka sakeshi aka damka shi a hannun mallam jatau.....


Da shi da sauran daliban mallam jatau suka garzaya majalisar mallam aka sake zama.

"Wasunku sun bi abinda nace ta hanyar hikima kuma sun dace" mallam jatau ya ambata "wasu kuma sunyi gaggawa don haka aka samu matsala."

"Abinda yake akwai shine, shi zaman aure zaman taimakekeniya ne, miji da mata tamkar tsuntsu ne mai fuka-fukai guda biyu. Don cikar lafiya da daidaituwar wannan tsuntsun dole ne kowane fuka-fuki ya motsa...... Mata tanada nata ayyukan da zata gudanar na daga ayyukan gida kula da tsaftar muhalli, da kuma rainon mai gidan kansa kamar yadda take rainon yayansa ko kusa da haka..... Bakuji mata suna kiran mazajensu da baby ba? To ai babyn ne shi.......... Su kuma maza su nemo abinci da kula da gurin zama, da lafiyar mata da yara da kuma lafiyar inda suke zama.... Hakanan idan akace abinci ana nufin abinci mai lafiya da gina jiki gwargwadon iko..... A sunnance an samu Annabi da sahabbai suna taya matansu ayyukan gida kuma taya aikin yana kara dankon soyayya tsakanin ma'auratan...."

Mallam garba a harzuke ya cafe maganar mallam yace "Wani lokacin a garin nan maimakon a samu qaruwar dankon soyayya dankon hauka ake samu....."

Yan majalisa suka bushe da dariya.

Mallam jatau yayi gyaran murya akai shiru sannan yaci gaba da cewa "Miji da mata kuma sunyi tarayya akan tarbiyyar yara, karku damu indai muna tare da sannu zan rinka nuna muku hanyoyin da zaku bi don gyara tsakaninku da matanku... gyara tsakaninku da matanku kuwa yana gyara tsakaninku da mahaliccinku........"


Anan muka kawo karshen takaitacciyar wannan nasihar mai suna majalisar mallam jatau..... Sai kuma Allah ya sadamu a rubutunmu na gaba.

✒️
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.