Posts

Showing posts from August, 2018

WAIWAYE ADON TAFIYA. (1 - 5)

Tatacciyar sirar Ma'aiki ( S.A.W ) Waiwaye Adon tafiya (1) Tatacciyar sirar Ma'aiki ( S.A.W ). Sakamakon buqatuwar yan uwa ga sirah , naga ya kamata in gabatar musu da ita tun lokacin jahiliyyah har zuwa inda Allah ya nufe mu da tiqewa . Tabbas jama'a suna buqatar sanin tarihi , domin kuwa da tarihine zasu san asalinsu , da manufarsu , da kuma hanyar dayafi kamata subi . Tabbas babu wani zamani da ake buqatar tataccan tarihi kamar wannan zamani . Saboda dalilai kamar hka . * Tarihin musulunchi yanà buqatar inganchi don tabbatar da abinda ya tabbata da kuma abinda aka farar dashi . * Tabbas akwai chanje chanje a tarihi da wasu masu son zuciya sukayi , duk Dan cimma wata manufa tasu . Kamar Yan Shi'ah , yan haqeeqah wahdatul wujudi , dadai sauransu . * Akwai labarai da kafirai ne suka qagosu suka sanyasu cikin musulunchi , daga baya kuma suke amfani dasu wajen suka