WAIWAYE ADON TAFIYA. (1 - 5)

Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)

Waiwaye Adon tafiya (1)

Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W).

Sakamakon buqatuwar yan uwa ga sirah, naga ya kamata in gabatar musu da ita tun lokacin jahiliyyah har zuwa inda Allah ya nufe mu da tiqewa.

Tabbas jama'a suna buqatar sanin tarihi, domin kuwa da tarihine zasu san asalinsu, da manufarsu, da kuma hanyar dayafi kamata subi.

Tabbas babu wani zamani da ake buqatar tataccan tarihi kamar wannan zamani.

Saboda dalilai kamar hka.

* Tarihin musulunchi yanà buqatar inganchi don tabbatar da abinda ya tabbata da kuma abinda aka farar dashi.

* Tabbas akwai chanje chanje a tarihi da wasu masu son zuciya sukayi, duk Dan cimma wata manufa tasu. Kamar Yan Shi'ah, yan haqeeqah wahdatul wujudi, dadai sauransu.

* Akwai labarai da kafirai ne suka qagosu suka sanyasu cikin musulunchi, daga baya kuma suke amfani dasu wajen suka ga musulunchi.

* Akwai labarai da ake jingina su da musulunchi masu mutuqar jan hankali, saidai kash zunzurutun karyace mara fa'ida, saidai ma asamu batanchi ga musulunchi a chikin wasu daga cikin labaran. Ko a tsara labarin ta hanyar damai karatu zai ji haushin wani daga salihan magabata na kwarai.

Bisa wayannan dalilai Ni Abu Umar Alkanawy naga dacewar dauko muku labaran sirah wadanda suka tabbata gwargwadon iko.

Na daga cikin dalilan daya sanya ni wannan rubutu.

* Mutane sun karkata zuwa ga ji da karanta qagaggun labarai marasa tushe da asali, wanda zunzurutun labari ne kawai da bai faru ba.

Idan jarumta mutum yakeso tabbas Annabi gawurtaccen namijin maza ne.

Idan Hikima da Dabara mutum yakeso, to tabbas Annabi madakatar hikima ne da iya dabara.

Idan iya zaman duniya mutum yakeso to masu iya zaman duniyar a gurin ma'aiki (S.A.W) suka koya.

Idan nutsuwa mutum yakeso, to nutsuwar bata zama nutsuwa sai an kwaikwayi Annabi.
..........
........

Rubutun zai zamo a mako(sati) sau biyu.

Ranar Litinin
Da ranar Alhamis.

Allah nake roqo daya inganta niyyata ya kuma karfafeni haqiqah shi mai qarfafawa ne.

Abu umar Alkanawy!

WAIWAYE ADON TAFIYA (2).

Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W).

Tabbas Allah (S.W.A) ya aiko Annabawa zuwaga al'ummatai kamar yadda Qur'ani ya bamu labari.

Kowane Annabi zakaga akwai irin wahalar dayayi fama da ita.......... Wannan kuwa jarrabawa ce daga Allah. Acikin Annabwa mafiya girma akwai Annabi Musa, Isah da Ibrahim (A.S) sun sha gwagwarmaya da mutanensu mutuqa...........

Duk namijin kokarin da sukayi amma bayan wucewarsu zuwaga mahalicconsu sai labari yasha bam bam.
Inda mabiya addinansu suka dara qirqiro bidi'o'i na shirka, tare da maida addinin ya zama yana tafiya kafada da kafada da al'adunsu na maguzanchi. Tafiya tayi nisa a qarshe ma sai suka chakuda littafan da Allah ya saukar da soye soyen zuqatansu. Harsaida ya zamana bazaka sami ingantacce littafi saukakke daga sama ba saidai na qarya ko wanda aka chakuda da son zuciya, da karairayi.
(Muhammad Rasulullah page 13, by Abul hasan Ali nadwi (English)).

Dalilin haka sai shirka ta yawaita suka koma bautawa malamansu, daganan sai shirka taci gaba da yaduwa harta gauraye ko ina. Bauta kala kala wasu suna bautar Gumaka, rana, wata, wuta, ruwa da sauransu. Addinai marasa asali da tushe suka Danno kai cikin duniya.

Daganan sai addinin Buddhism ya mamaye garuruwa tundaga India har zuwa central-asia.

(Discovery of India P. 201-203, Muhammad Rasulullah P. 18)

Ana tsaka da haka sai addinin hindu ya mamaye nahiyar gaba daya (Hindu da Buddhist duk ma'abota bautar gumaka ne) a wannan nahiya (india) a sixth century A.D saida ya zamana akwai ababen bauta miliyan 33 (33 millions) wayanda mabiya addinin Hindu suke bautawa........

(Muhammad Rasulullah p. 18)

A makkah a wannan lokaci a dakin ka'aba akwai gumaka guda 360.
(Bukhari babu fathu makkah)

Kowacce kabila tanada nata gunkin da take bautawa.

(Kitabul Asnam ibn kalabi)

Sakamakon haka sai duhun zalunchi ya mamaye duniya kwacen gida da mata da Yaya ba wani baqon abu bane. In baka da karfi wanda ya fika karfi zai mayar dakai bawansa kuma duk abinda ka mallaka ya zama nasa, wulakanta mata da binne jarirai mata da muzguna musu.

Mutane a wannan lokaci hankalinsu ya gushe basa bambamche mai kyau da Mara kyau, sun bar bautar Allah sun koma bautawa zuciyoyinsu.

Tabbas dubiya tana buqatar agaji.

Akwai wasu tsirarun mutane da wasu daga malamai suke lissafosu da sunan cewa suna kan addinin hanifs kamar waraqat bn naufal, usman bn huwan, ziyad bn amr da Abu anas.

Duk wannan abu dayake faruwa a duniya, Allah yana kallo kuma yana sane da kauche hanya da bayinsa sukai.tabbas duniya tana buqatar agajin gaggawa. Don samuwar zaman lafiya a cikinta.

Shin kuwa akwai wanda zai iya dawowa da mutane hankalinsu?

Shin daga ina duniya zata samu agaji?

WAIWAYE ADON TAFIYA (3).
Tatacciyar sirar Ma'aiki S.A.W.....

................
................
Kamar yadda bayanai suka gabata akan yadda duniya take kafin Annabtar Annabi Muhammad (S.A.W).

.......
Tabbas Allah mai hikima ne, don haka kafin ya aiko Annabin rahama, saiya zabar masa wajen dayafi dacewa dashi. Wato cikin larabawa.

Duk da irin halinda larabawa suke ciki na jahiliyyah, hakan bai hanasu riqo da wasu halayen kirki ba, kamar gaskiya, karamchi, amana, izza, rashin daukar raini da kuma taurin kai akan abinda suke kai. Sannan suna gujewa yaudara da ha'inchi.
(Rahiq Maktum)

Sannan ta fuskar al'adunsu, sunada riqo da al'ada ta inda zasu iya mutuwa akan kiyaye al'adarsu.
(The life of mahomet vol. 1 & Muhammad rasulullah P. 45)

Don haka a irin wannan yanayi ma'abota addinin hanifiyyah basu da damar yiwa larabawa wa'azi ba. Domin larabawan a shirye suke dasu mutu akan abinda suke kai.
(Muhammad rasullullah 45).

Allah daya zabarwa Annabi Qabila mafi girma saiya zabar masa dangi mafi girma wato quraishawa, babu wani waje da Annabi zai kasanche face Allah ya zabar masa mafi girma da falala. Kamar yadda ya bayyana hakan (Annabi) a hadisai wayanda Muslim da tirmidhi da wasun su suka rawaitosu.

Kuma bawai zamowar Annabi ne a cikin larabawan ya sanyasu suka zamo mafiya girma ba, dama Chan a cikin Qabilu sune mafiya girma da falala a wajen Allah, kamar yadda ibn taymiyyah ya fadada bayani a littafinsa Istiqaama!

Asalin larabawa kafin zuwan Annabi Muhammad (S.A.W) suna kan tafarkin Annabi Ibrahim, har zuwa lokacin da Amru bn luhayyi shugaban Qabilar khuza'at ya sauya musu tunani da Alqibla.

Amru bn luhayyi kuwa mutumin kirki ne asali, mai kokari wajen ciyarwa da bauta da sadaka ga karamchi. Don haka sai suke tsammanin shi wani babban makusanchine ga Allah. Kowani waliyyi.
(Rahiq maktum P.33)

Don haka wata rana yaje sham dayaga yadda ake bautawa gumaka sai abin ya burgeshi, saiya taho da gunki guda daga gumakan inda aka ajiyeshi a ka'aba. Sannan ya kira larabawa zuwa bautar gumaka kuma suka amsa masa.
(Kitabul Asnam ibn kalabi P. 28 & Rahiq maktum P.33 & Muhammad Rasulullah)

Da abin ya fadada saiya zamana kowace kabila tanada nata gunkin.

Bayan bata da larabawa sukai da kauche hanya.........

Sai Abrahata (wani shahararren sarki) yazo don ya rushe ka'aba, ya taho da gagarumar runduna cikinta harda wata giwa mai tsananin girma. Amma burinsa bai cikaba domin kuwa Allah ne ya saukar musu da tsuntsaye dauke da diwatsu na gidan wuta aka hallakasu.
(Sirah ibn Hisham)

Sanadiyyar faruwar hakan sai girman Quraishawa ya kuma Qaruwa a idon duniya.
(Muhammad Rasulullah P.75).

Al'amarin Abdulmuddalib kuwa wato kakan Annabi. Shine ya zabawa Abdullahi dansa matar data dace dashi wato Nana Ameenah bnt wahb, a wannan lokacin kuwa itace mafi girman mata ta bangaren nasaba da gurin zama.

Bayan ya auratane da wasu lokuta sai mahaifinsa ya aikeshi madina inda achan rai yayi halinsa.

A wata riwayar kuma akache ya tafi  sham ne don kasuwanchi. Inda ya dawo tare da tawagar quraishawa. A lokacin da sukazo madina bashida lafiya don haka saiya tsaya anan. Ashe lokacine yayi. Anan Allah ya karbi ransa aka kuma binneshi a madina.

Adai cikin wannan shekarar shekarar giwa sai Allah yayi nufin haska duniya daga duhu zuwa haske, daga zalunchi zuwa Adalchi, daga shirka zuwa tauhidi, daga bidi'a zuwa sunnah.

**To yan uwa yanzu ne zamu fara tarihin wato haihuwar ma'aiki abinda ya gabata duk shimfidache**

An haifi Annabi 9 ga watan rabi'ul Auwal(Rahiq maktum)

Saidai wasu dadama daga mutane suna cewa an haifeshi 12 ga watan rabi'ul Auwal.

Saidai binciken ma'abota ilmin Astronomy ya nuna cewa tara ga watan shine ranar Litinin din. Kamar yadda Mahmud Pasha na kasar misra ya bayyana hkan shi kuma masani ne a bangaren ilmin Astronomy.

Shin me zai faru a duniya, tundadai munji larabawa a shirye suke dasu bada rayuwarsu akan wanzuwar al'adarsu da ababen bautarsu?
Idan suka fuskanchi wanda aka haifa Annabine anya kuwa bazasu cutar dashi ba?

WAIWAYE ADON TAFIYA (4)
Tatacciyar sirar ma'aiki (S.a.w)

Allahu Akbar!!!

Tabbas an haifi gagara gasar masu gasa, Annabin karshe kuma cikamakin Annabawa.

Mahaifin Annabi ya rasu tun kafin haihuwarsa, don haka Annabin tsira maraya ne.
(Rahiq maktum & Muhammad rasulullah & sirah ibn Abdulwahhab)

Lokacinda mahaifiyarsa ta haifeshi, saita aikawa kakansa da busharar haihuwar, aikuwa cikin farin ciki yabar abin da yakeyi, ya taho cikin sauri da gaggawa.

Ya dauki wannan abin haihuwa ya shigar dashi ka'aba yayi godiya ga Allah tare da rokon Allah.
(Ibn hisham & Rahiq maktum 55)

Tabbas an rawaito abubuwa da dama kafin haihuwar Annabi da bayan haihuwarsa saidai mun tsallakesu domin basu da isnadi.........

Abdulmuddalib kakan Annabi shine ya zabar masa suna Muhammad.

Mahaifiyar Annabi Aminatu bnt wahb itace ta fara shayar da Annabi kafin daga baya suwaibatul Aslamiyyah ta karbeshi. Ita kuwa suwaibah ta shayar da Hamza bn Abdulmuddalib kafin ta shayar da Annabi, bayan Annabi kuma ta shayar da Abu salamata bn Abdul'asd Almakzumiy.
(Sahih Bukhari 5101,5107,5100 & Rahiq maktum 55)

Bayan ita kuma sai halimatussadiya ta karbeshi, itama kuma ta shayar da sayyadi hamza kafin Annabi Muhammad.

(Zadl ma'ad)

Bayan ta karbeshi sai Albarka ta sauka agidanta. Lamarin Annabi kuwa ya kasanche yana girma fiye da sauran yara. Don haka daya cika shekara biyu saita mayar dashi. Amma saboda soyayya da shaquwa saita kasa haqura ta nemi abata shi ta koma dashi ya kuma zauna a wajenta....... Har daga karshe mahaifiyar Annabi Muhammad ta yarda da buqatar Halimatu.
(Muhammad Rasulullah 93)

Bayan komawarsa wajen Halimatu wata rana ya fita tare da yara guda biyu saiga wasu mutane da fararen kaya sun nufosu gadan gadan. Aikuwa suna zuwa suka kayar da Annabi Muhammad suka kwantar dashi. Suka farka masa kirjinsa suka ciro zuciyarsa suka cire wani gudan jini a cikinta sannan suka mayar da ita suka dinke kirjin nasa. Sukuwa wayannan yara yan uwansa sai suka ruga da gudu gida suna cewa an kashe Muhammad!
Cikin firgici halimatusadiya suka nufo inda wannan abu ya faru Ai kuwa suna zuwa suka tarar da Annabi amma launinsa ya sauya dalilin haka sai taji tsoro ta dawo dashi gida wajen mahaifiyarsa.
(Muhammad Rasulullah 93-94)

Wannan abu ya farune lokacin Annabi yanada shekara 4.
(Rahiq 57)

Wayannan mutanen kuwa mala'iku ne, awata riwayar  kuma mala'ika jibril. Sun wanke datti ne daga zuciyar Annabi don haka shaidan baida rabo akansa.

Bayan Annabi ya dawo wajen mahaifiyarsa sai ya kasance akwai shaquwa sosai a tsakaninsu. Uwa ce da babu irinta, ga danta shima dane da babu irinsa, Yaya kake tunanin wannan soyayya da shaquwa??

Wata rana sai mahaifiyar Annabi tayi nufin kai ziyara kabarin mahaifinsa tare da yan'uwanta da suke madina, don haka suka shirya suka dauki hanya, tare dasu harda Ummu aimana daya daga cikin abubuwan da mahaifinsa ya rasu yabar masa kenan (ragowar abubuwan da mahaifinsa yavar masa sun hada da Rakuma guda biyar, awaki da wannan baiwa Ummu aiman).........
Bayan sunje a hanyarsu ta dawowa sai sai rashin lafiya ta kama mahaifiyar Annabi Muhammad. Koyaya zaiji saboda shaquwar da sukai??
Rashin lafiyar tata tayi tsamari a karshe dai rai yayi halinsa.

Allahu Akbar.
Mutuwar mahaifiya a halin tafiya, tabbas Annabi yayi gaskiya dayace wanda Allah ke nufinsa da alheri sai ya jarrabeshi!

Shin yaya rayuwar Annabi zata kasance bayan rasa mahaifansa guda biyu??

Waiwaye Adon tafiya (5).

Tatacciyar sirar ma'aiki (S.A.W)

Bayan rasuwar mahaifiyar Annabi a hanya, sai kakansa Abdulmuddalib ya dawo dashi. Saboda tausayinsa da sonsa dayake saiya jawoshi a jikinsa, harma yafi sonsa akan sauran yayansa. Sun shaqu mutuka sosai domin basa nisa da juna, harma yakan zaunar dashi akan shimfidarsa wadda yayansa ma basa zama akai.

Bayan Annabi yakai shekara 8 sai kakansa Abdulmuddalib ya rasu....... Kafin ya rasu kuwa ya bada amanarsa a hannun amminsa Abi dalib.
(Rahiq maktoum 58, Muhammad Rasulullah 95)

Annabi ya taso da tarbiyya, da amana, juriya, jarumta, karfin zuciya da rashin tsoro. Baya rama mummunan aiki da mummuna, saidai shi yana afuwa ne da haquri, baya wasa irinna jahiliyyah bayajin kida, ko zancen vanza ko alfasha.........tayaya zai aikata wayannan ayyuka alhalin ya samu tarbiyya ne ilahiyya....

Ana rawaito wata qissa ta buhaira wadda zaka sameta a littafai da dama na sirah. A cikinta buhaira yaga Annabi suka gana yaga wasu alamomi na Annabta a tattare dashi don haka ya umarchi Abu dalib dayayi gaggawar komawa da Annabi izuwa gida (Makkah).

Toh! Saidai wannan qissa akwai maganganu akanta, a cikin isnadinta akwai matsaloli da illoli wanda ma'abota wannan ilmi sun sansu kamar....

* A cikin sanadin akwai Abdurrahman bn ghazwan, tirmidhi ya bayyana cewa ba'asan wanene shiba.

* Imam zahby dalibin Ibn Taymiyyah cewa yayi "shi Abdrahman ya rawaito hadisai dadama marasa kyau, kuma mafi lalacewar wanda ya rawaito shine na qissar buhaira"
(Muhammad Rasulullah 96)

* ance Bilal ne ya dawo da Annabi gida, shikuwa Bilal a wannan lokaci ba samamme bane idan ma ya samu to Abu dalib bazai hadashi da Bilal ko Abubakar don su dawo tare dashi ba, domin kuwa yana bashi gagarumar kulawa.

* Saidai akwai ruwaya ta Abu nu'aim da isnadi mai karfi tabbatacce akan wannan qissar saidai itama tanada nata illolin, da kurakurai, domin ance Bilal neya dawo dashi da kuma sayyadi Abubakar. Abin sani dai shine Annabi duk ya girme musu a bangaren shekaru, don haka bazata yiwu a hadashi da yara ba. Musamman a wannan lokaci da ake tunanin gayyar Mutane zasu cutar dashi........
(Abu Umar Alkanawy)

Duba zadul ma'ad zaka tarar da magana ta ilmi da Ibn qayyim dalibin Ibn taymiyyah yayi.

Sannan wannan qissar ta sanya wasu suke cewa buhaira shine ya koyawa Annabi Qur'ani ....... Wal iyazu billah. Kamar yadda cerra de veaux na france ya rubuta littafi (BAHIRA THE AUTHOR OF THE QUR'AN) Wanda a cikin littafin yake kokarin cewa buhaira ya kowaya Annabi surori 114 a cikin yan mintuna........
(Muhammad Rasulullah 96)

Nace (Abu Umar):

"koma dai menene zamu gane cewa buhaira baida wani katabus wajen koyarda qur'ani ko kirkiroshi, da'awa ce ta kafirai, ita kuwa wannan qissa, Ina ganin rashin inganchinta zaifi dai dai. Domin matsalolin da take dauke dasu da illoli..........."

Zamu cigaba insha Allah.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.