Posts

Showing posts from January, 2018

INA HANKALIN YA TAFI?

Idan aka samu bambamcin shekaru masu tazara, tabbas za'a samu bambamcin fahimta da kuma yanayin yadda kowa tsakanin babba da karami suke kallon rayuwa...... Ka tuna lokacin da kake hakikancewa abu kaza da kaza daidaine, yayinda iyayenka da sauran magabata suke nuna maka cewa ba dai-dai bane..... In kuwa hakane ina hankalin maza da yawa yake tafiya lokacin da suka auro yarinyar da aqalla tazarar shekarunsu yakai 8 ko goma sha..... Kuma suke tunanin samun tunanin ta irin nasu? Da zarar tayi wani abu wanda ke dauke da yarinta kuma sai kaga an fara samun matsaloli a haka sai kaga matsala tana ta barkewa. A lokacin da kake tare da yaro, kaima saika koma yaro wani lokacin ba don komai ba sai don ku zauna lafiya kuma ku samu fahimtar juna..... Ka dubi rayuwar Annabi (S.A.W) da Nana Aisha... Shin daya aureta hana ta komai na yarinta yayi ko kuwa? Sign Abu Umar Alkanawy.

MU FARKA YAN NIGERIA

Bugun zuciyar yana tafiya da sauri tamkar karar kofaton ingarman doki lokacin dayake sharara gudu a dandaryar kasa, yayinda ruwa ya taso daga cikin ido ya cike saman idon wanda hakan ya bada damar ganin komai dishi-dishi.... Kafin daga bisani ruwan ya rikede ya zama hawaye sakamakon satatowa da zaiyi ya wanke wadataccen filin fuskar...... A zahiri kenan, a badini kuwa bakin ciki cike yake da zuciya wanda sanin ciwon kai da kishin al'umma su suka haifar da wannan bakin ciki.... Ba imani, ba kudi, ba ilmi, ba tarbiyya, ba shugabanchi, ba tausayi, ba jinkai, ba...ba...ba........ Abin da yawa, bawai babu su bane gaba daya, akwai su amma sunyi karanchi... Wanda wani sashen ma babu wasu gaba daya. Ta yaya al'ummar da jahilanta suke mulkarta zataci gaba? Ta yaya al'ummar da manyanta basa tausayawa kanana, kuma kananan basa girmama na gaba zataci gaba? Tayaya rashin tsaro, rashin tsari, rashin tarbiyya, rashin imani, rashin ilmi zasu cakuda basu haifar da abinda yake barazana

MAGANIN BACIN RAI

Sau d dama za a gaya maka wata kalma mara dadi, ko kuma a aikata maka wani aiki mai bata rai...... Wannan abu kuwa zai iya zamowa daga mahaifi ne ko mahaifiya ko mata ko miji, Aboki, Dan uwa da sauransu. Hakan kwarai yana sanya rai ya baci. Amma idan ka kawar dakai ana kiran wannan da "Tausayi ko Afuwa" amma fa wannan tabon da bacin ran yana nan damfare a cikin zuciyarka. To ta yaya zaka tafiyar da wannan radadi na bacin ran? Tayaya zaka bawa zuciyar kariya saboda kada cututtuka su shige ta irinsu gillu (kullata) hassada ko hawan jini da waninsu? Bari muji babban likitanmu me yace akan hakan (QUR'ANI)💡 1⃣ A cikin suratul hjr Allah yana cewa "kuma hakika mu munsan cewa kirjinka yana kuntata saboda abnda suke fada (na munanan kalamai)# Kayi tasbihi da godiya ga ubangijinka sannan ka zamo daga cikin masu sujjada" 2⃣ A karshe karshen suratu Daha Allah yana cewa "Kayi hakuri dangane da abinda suke cewa, ka kuma yi tasbihi da godiya ga ubangijinka kafin fi

MISALI ZUWA GA MA'AURATA

MADUBI ZUWA GA MA'AURATA... (Muhimmam misalai) By Naseeb Auwal Umar Maigida Bilal ya shigo gidan jikinsa a sanyaye, ya lallaba ya leka dakin uwargida safiyya ya ganta zaune ta tafka tagumi tana kallon yayanta guda uku da suke kwance suna bacci... Ganin haka yasa idon Bilal ya ciko da kwalla yayi maza ya share kwallar sannan ya kira sunanta a hankali ta yanda wayannan yara bazasu farka ba, tayi saurin dagowa tayi murmushi tana mai boye damuwarta ta taso tazo inda yake cikin fara'a tace "Sannu da zuwa". "Yawwa" ya amsa, sannan ya dora da cewa "kiyi hakuri, wallahi yau ban samo komai ba, don haka na bibiya ta wajen wayanda nake tunanin zan samu rance, amma kowa saina gama gaya masa sirrina saiyace min bashi da kudi.... A hanyata ta dawowa ne na samu ana wani aikin karfi, na tsaya na nemi alfarma na danyi shine suka bani wannan kudin..." ya nuna mata naira dari, "da itane na siyo garin kwaki don ke da yaran nan kusha saboda nasan kuna jin yu