MAGANIN BACIN RAI

Sau d dama za a gaya maka wata kalma mara dadi, ko kuma a aikata maka wani aiki mai bata rai...... Wannan abu kuwa zai iya zamowa daga mahaifi ne ko mahaifiya ko mata ko miji, Aboki, Dan uwa da sauransu.

Hakan kwarai yana sanya rai ya baci. Amma idan ka kawar dakai ana kiran wannan da "Tausayi ko Afuwa" amma fa wannan tabon da bacin ran yana nan damfare a cikin zuciyarka.

To ta yaya zaka tafiyar da wannan radadi na bacin ran? Tayaya zaka bawa zuciyar kariya saboda kada cututtuka su shige ta irinsu gillu (kullata) hassada ko hawan jini da waninsu?

Bari muji babban likitanmu me yace akan hakan (QUR'ANI)💡

1⃣ A cikin suratul hjr Allah yana cewa "kuma hakika mu munsan cewa kirjinka yana kuntata saboda abnda suke fada (na munanan kalamai)# Kayi tasbihi da godiya ga ubangijinka sannan ka zamo daga cikin masu sujjada"

2⃣ A karshe karshen suratu Daha Allah yana cewa "Kayi hakuri dangane da abinda suke cewa, ka kuma yi tasbihi da godiya ga ubangijinka kafin fitowar rana da gabanin faduwarta, hakanan a cikin dare da kuma wani yanki na wuni ko ka samu yarda"

3⃣ A karshe karshen suratul Qaaf Ya kuma cewa "Kayi hakuri dangane da abnda suke fada, sannan kayi tasbihi gabanin fitowar rana da gabanin faduwarta"
👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼
              👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
Don haka duk lokacin da aka gaya maka abu mara dadi don kawar dashi cikin sauqi daga zuciyarka sai ka lazimchi tasbihi.👌🏻

👆🏼👉🏼 Ka gwada kaga mu'ujizar Qur'ani.

✍🏾
Naseeb Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.