INA HANKALIN YA TAFI?

Idan aka samu bambamcin shekaru masu tazara, tabbas za'a samu bambamcin fahimta da kuma yanayin yadda kowa tsakanin babba da karami suke kallon rayuwa......

Ka tuna lokacin da kake hakikancewa abu kaza da kaza daidaine, yayinda iyayenka da sauran magabata suke nuna maka cewa ba dai-dai bane.....

In kuwa hakane ina hankalin maza da yawa yake tafiya lokacin da suka auro yarinyar da aqalla tazarar shekarunsu yakai 8 ko goma sha..... Kuma suke tunanin samun tunanin ta irin nasu?
Da zarar tayi wani abu wanda ke dauke da yarinta kuma sai kaga an fara samun matsaloli a haka sai kaga matsala tana ta barkewa.

A lokacin da kake tare da yaro, kaima saika koma yaro wani lokacin ba don komai ba sai don ku zauna lafiya kuma ku samu fahimtar juna.....

Ka dubi rayuwar Annabi (S.A.W) da Nana Aisha... Shin daya aureta hana ta komai na yarinta yayi ko kuwa?

Sign
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.