Posts

Showing posts from September, 2026

Matan Aure a Musulunci: Hakki, Daraja da Kyakkyawar Mu’amala.

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. Kowanne abu ba cikakke ba ne, duk halittar da Allah ya yi babu kamar mutum, amma shi kansa mutum tara yake bai cika goma ba, a dabi'ance, lafiyance da addinance. To haka idan ka duba abubuwan da suke kewaye da mu, masu rai da marasa rai za ka iske kowanne yana da bangaren da ya cika yana da kuma bangaren da ya ke da tawaya. ALLAH Buwayi Gagara Misali shi kadai ne cikakke, kuma gwargwardon kusancin bawa zuwa ga Allah gwargwadon cikarsa, kimarsa da darajarsa. Shi yasa Annabin Rahama ﷺ ya fi kowa zama cikakke domin ya fi kowa kyakykyawar alaka da Allah Mai Girma. Idan muka dauki ayyuka da kuma tsarin rayuwa za mu iske cewa cike take da kalu-bale mai yawa, kuma cike take da misalai ga masu hankali na irin hanyoyin da ta bi ta dilmiyyar game da hallakar da wayanda suka daukaka sha'aninta, kamar kuma za mu ga ba ta bar na kirkin ba, domin kuwa kowa akwai irin matsalolin da ya yi fama da su, kuma ya ke fama da su, kuma zai yi fama da su a nan gab...

BAMBANCIN BIN ALLAH DA BIN ƘUNGIYA

Image
BAMBANCI... Tambayi kanka : Shin kana bin abin da Allah da Manzonsa ﷺ suka umarta ne, ko kana neman hujja ne kawai domin kare abin da ka riga ka yarda da shi? BIN ALLAH DA MANZONSA ﷺ Musulmi na gaskiya yana ɗaukar Qur’ani da ingantacciyar Sunnah a matsayin ma’aunin gaskiya. Duk lokacin da ya san hukuncin Allah da Manzonsa ﷺ a kan wani abu, abin da ake buƙata daga gare shi shi ne sallamawa da biyayya, ba neman wata hanya ta fifita son rai ko al’ada ko ra’ayin wani a kan dalilin  ba. Allah Ya ce: يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنكُمْ ۖ فَإِن تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ “Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yi biyayya ga Allah, kuma ku yi biyayya ga Manzo, da ma'abota al'amari (ilmi ko shugabanchi) daga cikinku. Idan kuka yi saɓani a kan wani abu, ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzo...” [An-Nisā’ 4:59]. Ka lura da abin da Allah Ya koyar: idan aka samu saɓani, a mayar da al’amari zuwa ga A...