BAMBANCIN BIN ALLAH DA BIN ƘUNGIYA
BAMBANCI...
Tambayi kanka: Shin kana bin abin da Allah da Manzonsa ﷺ suka umarta ne, ko kana neman hujja ne kawai domin kare abin da ka riga ka yarda da shi?
BIN ALLAH DA MANZONSA ﷺ
Musulmi na gaskiya yana ɗaukar Qur’ani da ingantacciyar Sunnah a matsayin ma’aunin gaskiya. Duk lokacin da ya san hukuncin Allah da Manzonsa ﷺ a kan wani abu, abin da ake buƙata daga gare shi shi ne sallamawa da biyayya, ba neman wata hanya ta fifita son rai ko al’ada ko ra’ayin wani a kan dalilin ba.
Allah Ya ce:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنكُمْ ۖ فَإِن تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ
“Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yi biyayya ga Allah, kuma ku yi biyayya ga Manzo, da ma'abota al'amari (ilmi ko shugabanchi) daga cikinku. Idan kuka yi saɓani a kan wani abu, ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzo...” [An-Nisā’ 4:59].
Ka lura da abin da Allah Ya koyar: idan aka samu saɓani, a mayar da al’amari zuwa ga Allah da Manzo, ba zuwa ga ƙungiya, shehi, shugaba ko ra’ayin da muka riga muka ɗauka ba.
Allah Ya kuma ce:
وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِم
“Ba ya halatta ga mumini namiji ko mumina mace, idan Allah da Manzonsa suka hukunta wani al’amari, su kasance suna da wani zaɓi a cikin al’amarinsu.” [Al-Ahzāb 33:36].
Haka kuma Allah Ya ce:
“Maganar muminai idan aka kira su zuwa ga Allah da Manzonsa domin Ya yi hukunci a tsakaninsu ita ce: Mun ji kuma mun yi biyayya.” [An-Nūr 24:51].
Kuma Allah Ya nuna cewa son Allah yana tare da bin ManzonSa ﷺ:
قُلْ إِن كُنتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ
“Ka ce: Idan kuna son Allah, to ku bi ni; Allah zai so ku kuma Ya gafarta muku zunubanku.” [Āli ‘Imrān 3:31].
Saboda haka, tsarin mumini shi ne:
Dalili → fahimta → sallamawa → aiki.
Ba:
Ra’ayi → zaɓar abin da ya dace da ra’ayi → neman hujja domin kare shi.
BIN ƘUNGIYA KO RA'AYI KO DA YA CI KARO DA DALILI
Akwai wani haɗari mai girma idan mutum ya fara da:
“Abin da malamina/ƙungiyata/ɗariƙata ta ce shi ne gaskiya.”
Sannan sai ya tafi neman hujjoji ido rufe kawai domin kare wannan matsaya.
Idan ya sami nassi da ya saba da ra'ayinsu, sai ya fara:
- Neman wata fassara ko tawili domin ya kawar da ma'anar nassin;
- Raunana sahihin nassi saboda kawai bai dace da kungiyarsu ba;
- Daukar ra'ayin nasu a matsayin ma'auni, sannan ya auna Qur'ani da Sunnah da shi.
Wannan ba ita ce hanyar da Allah Ya koyar da mu ba.
Allah Ya ce:
وَأَنِ احْكُم بَيْنَهُم بِمَا أَنزَلَ اللَّهُ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَهُمْ
“Ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar, kuma kada ka bi son zuciyarsu.” [Al-Mā’idah 5:49].
Idan har Annabin Rahama za a gaya masa haka, kai wanene da za ka dauki son zuciyarka a matsayin abu mai hukunci a kan Qur'ani da Sunnah?
Manzon Allah ﷺ ya ce:
««مَنْ أَحْدَثَ فِي أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ مِنْهُ فَهُوَ رَدٌّ»»
“Duk wanda ya ƙirƙiro wani abu a cikin wannan al’amarin namu (addini) wanda ba daga cikinsa ba ne, to shi abin juyarwa ne.”
Sahih Muslim 1718a; Sahih al-Bukhari 2697.
Saboda haka, ibada ba ta zama ingantacciya saboda kawai “mun saba yin haka”, ko “malaminmu ya ce”, ko “ƙungiyarmu haka take”. Ana bukatar a duba dalilinta da shari’a.
SHIN BIYAYYA GA MALAMI KO SHUGABA BA TA HALATTA BA?
A'a.
Musulunci ya umurce mu da girmama malamai da masu iko ko mulki, dukkaninsu suna karkashin fadin Allah
وَأُولِي الْأَمْرِ مِنكُمْ
[An-Nisā’ 4:59].
Amma wannan biyayyar ta na da iyaka, ba ta zama ta marar iyaka ba, shi yasa Manzon Allah ﷺ ya ce:
««لَا طَاعَةَ فِي مَعْصِيَةِ اللَّهِ، إِنَّمَا الطَّاعَةُ فِي الْمَعْرُوفِ»»
“Babu biyayya a cikin saɓon Allah; biyayya tana cikin abin da yake na alheri.”
Hadisin na cikin sahihul Bukhari sannan hadisai da wannan ma'anar adadinsu ba zai lissafu ba.
Don haka, malamai ana girmama su, ana amfana da iliminsu, kuma ana komawa gare su wajen fahimtar nassosi. Amma ba a ɗaukar maganar wani mutum daga cikinsu a matsayin wahayi. Idan malami ya yi kuskure, ana iya girmama shi amma a bar kuskurensa ba tare da an ci mutuncinsa ba, ko an yi sukuwar sallah akansa ba.
BABBAR MAGANA
Allah Ya ambaci wasu daga cikin Ahlul-Kitāb da cewa:
اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِن دُونِ اللَّهِ
“Sun riƙi malaman addininsu da masu bautarsu a matsayin iyayengiji (ababen bauta) bayan Allah...” [At-Tawbah 9:31].
Ba wai ma'anar tana nufin cewa sun kasance suna yin sujada ga malamansu ba ne; abin da suke kuma ya kamata a lura da shi shi ne ɗaukar ikon halattawa da haramtawa ba tare da hujjar Allah ba, da kuma bin wannan a matsayin abin da ba za a tambaya ba. Idan malami ko mai bauta yace musu abu kaza halal ne to su babu ruwansu, koda kuwa sun san wannan abin haramun ne a shari'a. Wannan sai ya tuna min da hadisin Adiyyu Ibn Hatim, hadisi ingantacce wanda shi ma a ciki Adiyyu ya ke cewa ai basa bautawa malamansu, sai Annabin Rahama yace da shi shin ba sa halatta muku haram kuma su haramta muku halal sannan ku yi musu biyayya?
Adiyyu Ibn Hatim sai ya amsa da tabbatar da cewa suna aikata hakan, sai Annabi ya tabbatar masa da cewa to ai wannan ma ibada ce.
Saboda haka, ka tambayi kanka:
Idan aka kawo maka sahihin dalili daga Qur’ani ko Sunnah wanda ya saɓa wa abin da ka ke kai na kungiyanci, shin me kake yi?
Kana cewa:
“Mun ji kuma mun yi biyayya.”
Ko kuwa kana fara neman hanyar da za ka kare abin da ka riga ka yanke shawara a kansa?
KA TAMBAYI KANKA
Shin ina bin dalili ne saboda ina son gaskiya?
Ko:
Ina da matsaya tukunna, sannan nake neman hujja domin kare ta?
Shin idan Qur’ani da Sunnah suka saba da ra’ayina, zan bar ra’ayina?
Ko:
Zan nemi tawilin da zai sa ra’ayina ya ci gaba da zama dai-dai?
Ku sani, yaku yan albarka. Gaskiyar bin Allah ba wai kawai ka ce “ni Musulmi ne” ba ce.
Gaskiyar bin Allah ita ce:
Idan gaskiya ta bayyana maka, ka sallama mata ko da ta sabawa son ranka, al’adarka, ra’ayinka, ko abin da ka saba gani daga mutanen da kake girmamawa.
Tambayi kanka: A wanne bangare kake?
Ma su bin Allah, ko masu bin kungiya?
Allah Ya shiryar da mu zuwa ga gaskiya, Ya ba mu ikon bin ta idan mun gane ta, kuma Ya kare mu daga bin son zuciya.
آمين.
Abu Umar Alkanawy

Comments
Post a Comment