Posts

Showing posts from May, 2026

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W (2)

Image
TARIHIN ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM WAIWAYE ADON TAFIYA TATACCIYAR SIRAR MA'AIKI S.A.W Abin da wannan rubutu ya kunsa.... HALAYEN LARABAWA KAFIN ZUWAN ANNABTA ASALIN BATAN LARABAWA KAFIN ZUWAN ANNABTA ABRAHATA YA ZO DON RUSHE KA'ABA RASUWAR MAHAIFIN ANNABI HAIHUWAR ANNABIN RAHAMA BAYAN HAIHUWAR RAHAMA GA TALIKAI SHAYAR DA ANNABIN RAHAMA TSAGA KIRJIN ANNABIN RAHAMA RASUWAR MAHAIFIYARSA SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM Halayen Larabawa Kafin Zuwan Annabta Mun ji yanayin da duniya take kafin Annabtar Annabi Muhammad (S.A.W). Tabbas Allah Mai Hikima ne, kuma mun san cewa duk Annabin da za a aiko zai sha wahala mutuka, musamman kuma Annabi ne da za a turoshi zuwa duniya baki dayanta ba wai zuwa wata alkarya ko gari ba. Don haka kafin ya aiko Annabin rahama, sai ya zabar masa wajen da yafi dacewa da shi. Wato cikin larabawa. Duk da irin halin da larabawa suke ciki na jahiliyyah, hakan bai hana su riko da wasu halayen kirki ba, kamar gaskiya, karamchi, amana, iz...

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (1)

Image
Waiwaye   Adon   Tafiya   Tatacciyar  sirar   Ma'aiki  ( S.A.W ). SHIMFIDA Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaba (S.A.W), tare da Ahalinsa tsarkaka, da Sahabbansa masu girma. Tabbas al'ummarmu tana bukatar tarihin Annabinta, tarihi wanda zai zo mata da wani salo na haska mata abin da ta rasa, tarihi da zai zo da wata rariya ta tankade dukkanin wani abu wanda bai tabbata ba a cikin tarihin Annabinmu, tarihi wanda zai zo da wani salo na fito mata da darussan da suke cikin wannan rayuwa mai albarka... Zan iya cewa babu zamanin da musulmai suke bukatar sanin Annabinsu irin wannan zamani, sakamakon yawaitar suka ga janibinsa da kuma kokarin kore ayyukansa har a cikin musulmai ka samu wasu sune zaton cewa sukar tabbatattun abubuwa daga Annabin rahama shi ne ba shi kariya. Sakamakon bukatuwar yan uwa ga sanin tarihin, na ga ya kamata in gabatar musu da ita tun daga abin da ya samu na lokacin Jahiliyya har zuwa ind...