TARIHIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W (2)


TARIHIN ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM

WAIWAYE ADON TAFIYA

TATACCIYAR SIRAR MA'AIKI S.A.W

Abin da wannan rubutu ya kunsa....

  • HALAYEN LARABAWA KAFIN ZUWAN ANNABTA
  • ASALIN BATAN LARABAWA KAFIN ZUWAN ANNABTA
  • ABRAHATA YA ZO DON RUSHE KA'ABA
  • RASUWAR MAHAIFIN ANNABI
  • HAIHUWAR ANNABIN RAHAMA
  • BAYAN HAIHUWAR RAHAMA GA TALIKAI
  • SHAYAR DA ANNABIN RAHAMA
  • TSAGA KIRJIN ANNABIN RAHAMA
  • RASUWAR MAHAIFIYARSA SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM


Halayen Larabawa Kafin Zuwan Annabta

Mun ji yanayin da duniya take kafin Annabtar Annabi Muhammad (S.A.W). Tabbas Allah Mai Hikima ne, kuma mun san cewa duk Annabin da za a aiko zai sha wahala mutuka, musamman kuma Annabi ne da za a turoshi zuwa duniya baki dayanta ba wai zuwa wata alkarya ko gari ba. Don haka kafin ya aiko Annabin rahama, sai ya zabar masa wajen da yafi dacewa da shi. Wato cikin larabawa.

Duk da irin halin da larabawa suke ciki na jahiliyyah, hakan bai hana su riko da wasu halayen kirki ba, kamar gaskiya, karamchi, amana, izza, rashin daukar raini da kuma taurin kai a kan abin da suke kai. Sannan suna gujewa yaudara da ha'inchi.
(Rahiq Maktum)

Sannan ta fuskar al'adunsu, sunada riko da al'ada ta inda za su iya mutuwa a kan kiyaye al'adarsu.
(The Life of Mahomet, Vol. 1 & Muhammad Rasulullah, p. 45)

Don haka a irin wannan yanayi ma'abota addinin Hanifiyyah ba su da damar yiwa larabawa wa'azi. Domin larabawan a shirye suke da su mutu akan abin da suke kai.
(Muhammad Rasullullah 45).

Allah da ya zabarwa Annabi kabila mafi girma sai ya zabar masa dangi mafi girma wato Quraishawa, babu wani waje da Annabi zai kasanche face Allah ya zabar masa mafi girma da falala. Kamar yadda ya bayyana hakan (Annabi) a hadisai wayanda Muslim da tirmidhi da wasun su suka rawaitosu.

Kuma bawai zamowar Annabi ne a cikin larabawan ya sanya su suka zamo mafiya girma ba, dama can a cikin kabilu sune mafiya girma da falala a wajen Allah, kamar yadda Ibn Taymiyyah ya fadada bayani a littafinsa Istiqaama!


Asalin Batan Larabawa Kafin Zuwan Annabta

Asalin larabawa kafin zuwan Annabi Muhammad (S.A.W) suna kan tafarkin Annabi Ibrahim, har zuwa lokacin da Amru bn Luhayyi shugaban kabilar khuza'ata ya sauya musu tunani da Alkibla.

Amru bn Luhayyi kuwa mutumin kirki ne asali, mai ƙoƙari wajen ciyarwa da bauta da sadaka ga karamci. Don haka sai suke tsammanin shi wani babban makusancine ga Allah. Kowani waliyyi.
(Rahiq Maktum P.33)

Don haka wata rana ya je Sham sai yaga yadda ake bautawa gumaka sai abin ya burgeshi, sai ya taho da gunki guda daga gumakan inda aka ajiyeshi a Ka'aba. Sannan ya kira larabawa zuwa bautar gumaka kuma suka amsa masa.
(Kitabul Asnam Ibn Kalabi, P. 28 & Rahiq Maktum P.33 & Muhammad Rasulullah)

Da abin ya fadada sai ya zamana kowace kabila tana da nata gunkin, kuma cikin kankanin lokaci sai bautar gunki da kamun kafa da shi ya zama ruwan dare, kai har sai da ya zamana idan mutum zai tafiya sai ya tanadi gunkin da zai tafe da shi, wasu har da dabino suke hada na su gunkin in yunwa ta kusa kashe mutum a hanya sai ya cinye abin bautar nasa, ko kuma idan mutum zai tafiya sai ya dauki manyan duwatsu guda hudu, yayi murhu da guda uku, dayan kuma ya zama abin bautarsa,a takaice dai shirka ta zama ruwan dare. Mai son karin bayani sai ya duba littafin Sunan Darimiy, domin da hadisai irin wayannan ya bude littafin.

Abrahata Ya Zo Don Rushe Ka'aba

Ana cikin wannan duhun zaluncin sai Abrahata (wani shahararren sarki) ya zo don ya rushe Ka'aba, ya taho da gagarumar runduna cikinta har da wata giwa mai tsananin girma. Amma burinsa bai cika ba domin kuwa Allah ne ya saukar musu da tsuntsaye dauke da duwatsu na gidan wuta aka hallakasu.
(Sirah ibn Hisham)

Sanadiyyar faruwar hakan sai girman Quraishawa ya kuma Qaruwa a idon duniya. Kuma suka sanyawa wannan shekarar suna da S hekarar Giwa
(Muhammad Rasulullah P.75).

Al'amarin Abdulmuddalib kuwa wato kakan Annabi. Shi ne ya zabawa Abdullahi dansa matar da ta dace da shi wato Nana Aminah yar Wahb, a wannan lokacin kuwa ita ce mafi girman mata ta bangaren nasaba da gurin zama. Da ita da Sayyadi Abdullahi dukkaninsu suna da kyawawan dabi'u kuma ba su da tabo irin na jahiliyyah.

Rasuwar Mahaifin Annabi Muhammad (S.A.W)

 Bayan ya aureta ne da wasu lokuta sai mahaifinsa ya aike shi Madina inda a can rai ya yi halinsa.

A wata riwayar kuma aka ce ya tafi  Sham ne don kasuwanci. Inda ya dawo tare da tawagar Quraishawa. A lokacin da suka zo Madina bashi da lafiya don haka sai ya tsaya a nan. Ashe lokaci ne ya yi. A nan Allah ya karbi ransa aka kuma binneshi a Madina.


Haihuwar Annabin Rahama

A cikin wannan shekarar, shekarar giwa sai Allah ya yi nufin haska duniya daga duhu zuwa haske, daga zalunci zuwa adalci, daga shirka zuwa tauhidi, daga bidi'a zuwa sunnah. Malamai sun tabbatar da cewa an haifi Annabi a Shekarar Giwa, kuma ranar Litinin, kuma cikin watan Rabiul Auwal.

Dangane da kwanan wata kuwa, masana ilmin Falaki (Astronomy) da masu binciken zamani sun yi lissafin ranaku ta hanyar komawa baya don gano ranar Litinin din da aka haifi Manzon Rahama, inda kuma lissafin na su ya nuna cewa ranar ta yi dai-dai da 9 ga watan Rabiul Auwal.

Cikin masana da suke da wannan fahimtar akwai Mahmud Pasha Alfalaki, babban malami a kasar Masar, sai Safiur-Rahman Almubarakpuri, shahararren malamin nan na kasar India a littafinsa Arraheeq Almaktoum, sai kuma Allama Shibil Nomani.

Amma magana wadda tafi shahara a tsakanin al'ummar musulmi kuma malamai magabata suka fi rinjayar da ita, ita ce an haifi Annabin Rahama a 12 ga watan Rabiul Auwal. Cikin magabata akwai Ibn Ishaq shahararren malamin tarihi da ya rasu a shekarar 151 bayan Hijirar Annabin Rahama, akwai Ibn Hisham, sannan Ibn Kathir a cikin Littafin Albidayah wan Nihayah, ya ambaci cewa 12 ga wata ita ce riwayar da tafi shuhura.

Akwai wasu ruwayoyin da suke nuna an haifi Annabin Rahama 2 ga wata, ko 8 ga wata, ko 10 ga watan, sai dai maganar da ta fi inganci shi ne 9 ko 12, Allah ne mafi sani.

Shin me zai faru a duniya, tunda da mun ji Larabawa a shirya suke su ba da rayuwarsu a kan wanzuwar al'adarsu da abin bautarsu?
Idan suka fuskanci wanda aka haifa Annabi ne anya kuwa ba za su cutar da shi ba?

Tabbas an haifi gagara gasar masu gasa, Annabin karshe kuma cikamakin Annabawa. Mahaifin Annabi ya rasu tun kafin haihuwarsa, don haka Annabin tsira maraya ne.

(Rahiq maktum & Muhammad Rasulullah & Sirah Ibn Abdulwahhab)

Lokacin da mahaifiyarsa ta haife shi, sai ta aikawa kakansa da busharar haihuwar, aikuwa cikin farin ciki ya bar abin da ya ke yi, ya taho cikin sauri da gaggawa. Ya dauki wannan abin haihuwa ya shigar da shi Ka'aba ya yi godiya ga Allah tare da rokon Allah.

(Ibn Hisham & Rahiq Maktum 55)

Bayan Haihuwar Rahama Ga Talikai

A wannan lokacin da ya dauke shi bai san cewa ya dauki wani abin haihuwa ba ne wanda daga farkon halitta har zuwa karshensa babu mai darajarsa, bai san cewa ya dauki gagara misalin abin haihuwa ba ne a cikin dukkanin ababen halitta, bai san cewa ya shigar da wannan abin haihuwa dakin da za a wayi gari a hana shi shiga cikinsa ba, daga baya kuma ya zama shi ne mai iko da dakin.

Tabbas an rawaito abubuwa da dama kafin haihuwar Annabi da bayan haihuwarsa sai dai mun tsallakesu domin ba su da isnadi...

Abdulmuddalib kakan Annabi shi ne ya zabar masa suna Muhammad.

Shayar da Annabin Rahama

Mahaifiyar Annabi Aminatu Bnt Wahab ita ce ta fara shayar da Annabi kafin daga baya Suwaibatul Aslamiyyah ta karbe shi. Ita kuwa Suwaibah ta shayar da Hamza Bn Abdulmuddalib kafin ta shayar da Annabi, bayan Annabi kuma ta shayar da Abu salamata Bn Abdul'asd Almakzumiy.
(Sahih Bukhari 5101,5107,5100 & Rahiq maktum 55)

Bayan ita kuma sai Halimatus Sadiya ta karbe shi, ita ma kuma ta shayar da Sayyadi Hamza kafin Annabi Muhammad.

(Zadil Ma'ad)

Tsaga Kirjin Annabin Rahama

Bayan ta karbeshi sai Albarka ta sauka agidanta. Lamarin Annabi kuwa ya kasanche yana girma fiye da sauran yara. Don haka daya cika shekara biyu sai ta mayar da shi. Amma saboda soyayya da shakuwa sai ta kasa hakura ta nemi abata shi ta koma da shi ya kuma zauna a wajenta... Har daga karshe mahaifiyar Annabi Muhammad ta yarda da bukatar Halimatu.
(Muhammad Rasulullah 93)

Bayan komawarsa wajen Halimatu wata rana ya fita tare da yara guda biyu sai ga wasu mutane da fararen kaya sun nufosu gadan gadan. Aikuwa suna zuwa suka kama shi, suka kwantar da shi. Ba tare da bata lokaci ba suka farka masa kirjinsa suka ciro zuciyarsa suka cire wani gudan jini a cikinta sannan suka mayar da ita suka dinke kirjin nasa. Sukuwa wayannan yara yan uwansa sai suka ruga da gudu gida suna cewa an kashe Muhammad! Cikin firgici su Halimatu suka nufo inda wannan abu ya faru, ai kuwa suna zuwa suka tarar da Annabi amma launinsa ya sauya dalilin haka sai ta ji tsoro ta mayar da shi gida wajen mahaifiyarsa.
(Muhammad Rasulullah 93-94)

Wannan abu ya farune lokacin Annabi yanada shekara 4.
(Rahiq 57)

Wayannan mutanen kuwa mala'iku ne, a wata riwayar ma mala'ika Jibril ne. Sun wanke datti ne daga zuciyar Annabi don haka shaidan bai da rabo akansa.

Bayan Annabi ya dawo wajen mahaifiyarsa sai ya kasance akwai shakuwa sosai a tsakaninsu. Uwa ce da babu irinta, ga dan ta shima da ne da babu irinsa, Yaya kake tunanin wannan soyayya da shakuwa??

Rasuwar Mahaifiyarsa

Wata rana sai mahaifiyar Annabi ta yi nufin kai ziyara kabarin mahaifinsa tare da yan'uwanta da suke Madina, don haka suka shirya suka dauki hanya, tare da su har da Ummu Aimana daya daga cikin abubuwan da mahaifinsa ya rasu ya bar masa (ragowar abubuwan da mahaifinsa ya bar masa sun hada da rakuma guda biyar, awaki da wannan baiwa Ummu Aiman).
Bayan sun je a hanyarsu ta dawowa sai sai rashin lafiya ta kama mahaifiyar Annabi Muhammad. Ko yaya zai ji saboda shakuwar da su kai?
Rashin lafiyar ta ta tayi tsamari a karshe dai rai yayi halinsa.

Allahu Akbar.

Mutuwar mahaifiya a halin tafiya, tabbas Annabi ya yi gaskiya da yace wanda Allah ke nufinsa da alheri sai ya jarrabe shi!

Shin yaya rayuwar Annabi za ta kasance bayan rasa mahaifansa guda biyu??

Za mu dakata a nan, sai kuma a rubutu na gaba.


Abu Umar Alkanawy

Comments

Popular posts from this blog

KNOWLEDGE AND ITS NEGATIVE EFFECT...

JAN HANKALI GA ƊALIBAN KIMIYYA

PUBLIC DANCE!!!