MISALI ZUWA GA MA'AURATA

MADUBI ZUWA GA MA'AURATA...
(Muhimmam misalai)

By
Naseeb Auwal Umar

Maigida Bilal ya shigo gidan jikinsa a sanyaye, ya lallaba ya leka dakin uwargida safiyya ya ganta zaune ta tafka tagumi tana kallon yayanta guda uku da suke kwance suna bacci...
Ganin haka yasa idon Bilal ya ciko da kwalla yayi maza ya share kwallar sannan ya kira sunanta a hankali ta yanda wayannan yara bazasu farka ba, tayi saurin dagowa tayi murmushi tana mai boye damuwarta ta taso tazo inda yake cikin fara'a tace "Sannu da zuwa".

"Yawwa" ya amsa, sannan ya dora da cewa "kiyi hakuri, wallahi yau ban samo komai ba, don haka na bibiya ta wajen wayanda nake tunanin zan samu rance, amma kowa saina gama gaya masa sirrina saiyace min bashi da kudi.... A hanyata ta dawowa ne na samu ana wani aikin karfi, na tsaya na nemi alfarma na danyi shine suka bani wannan kudin..." ya nuna mata naira dari, "da itane na siyo garin kwaki don ke da yaran nan kusha saboda nasan kuna jin yunwa......"

Uwar gida safiyya ta katseshi "Abban yasmeen ba komai nasan kana iyakar kokarinka, kuma duk rintsi yana tare da sauki, yaran abin tausayi tun dazu suketa cewa abinci-abinci, da kyar na shawo kansu sukai bacci.... Kaga kuwa yanzu tunda an samu wannan sai in tashe su don wannan ai abin marmari ne....." bata karasa maganar ba, sai hawaye ya ganganro ta idanunta.

Bilal ya kalleta cikin mutuwar jiki yace "Haba maman yasmeen, kada ki zubar da hawayenki masu daraja, ki tuna kece jajirtacciyar uwarnan wadda bata so taga yayanta a cikin damuwa, kuma tabbas mutuqar kikai kuka to yayanki suka gani zasu shiga damuwa, idan kika saka damuwa da yawa a jikinki zakiyi zazzabi wanda dalilin hakan zai saka yayanki su samu karancin kulawa.....

Safiyya ta share hawayen ta, tayi murmushin karfin hali tace "nagode mai gidana.."

"Ya juya yana mai cewa _Bari naje ko zan samu wani abin in qaro muku dashi...

"Kai bazaka sha ba", ta fada tana mai kallonsa cikin yanayi na tausayawa.

"Karki damu yanzu zan dawo, ni dai burina da ke da yayan namu ku samu ku koshi.....

Ya fice....

Safiyya ta tsaya tana jinjina al'amarin daga bisani tayi murmushi tana mai lumshe ido tace "Yar'uwa ke dai zabi mai tsoron Allah".

Shima Bilal yana fita waje ya daga hannu ya godewa Allah sannan yace "Dan'uwa, kai dai zabi mai tsoron Allah kasha mamaki".

Sign
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.