INGANTACCIYAR MAGANA AKAN SIFFOFIN DA AKE SIFFANTA ALLAH (S.W.A) DA SU.

INGANTACCIYAR MAGANA GAME DA SUNAYE DA SIFFOFIN ALLAH.

Babu wanda yasan hakikanin siffofin Allah da sunayensa sai shi ubangijin daya barwa kansa sani......

To in kuwa hakane babu wata siffa wadda zamu yarda da cewar ta Allah ce sai wadda muka san cewa daga gareshi take. 

Mun kuwa san cewa babu wani abu daga Allah wanda ya wuce Qur'an da hadisi. In mun yarda da hakan to a Quran da hadisi kawai zamu dauko siffofi da sinayen Allah....

Wanda kuma yayi da'awar cewa shima yasan wasu wayanda babu su a Qur'an ko sunnah to saiya zo da hujja bayyananniya......

Dangane da maganar sunaye da siffofi gaba dayansu zamu iya rabasu zuwa kamar gida hudu.

1. Abinda Allah ya tabbatarwa da kansa, kamar ji, gani, ilmi da izzah.

2. Abinda Allah ya korewa kansa kamar rauni, nakasa da bacci.

3. Abinda Allah bai magana akansa ba amma saboda abin yana nuni da rauni dole a koreshi ga Allah. Kamar bakin ciki da kuka.
Akwai bambanchi tsakanin fushi da baƙin ciki.
Shi fushi anayinsa ne akan abin da ake da iko akai.
Shi kuma bakin ciki anayinsa ne akan abin da ba a da iko akansa.
Misali:
Wanda yayi laifi gwabnati tana fushi dashi don tana da iko akansa.

Wanda akayiwa mutuwa yana baƙin ciki sabo da bashi da iko akan hana mutuwar.

4. Abin da babu naƙasa a ciki amma Allah bai korewa kansa ko tabbatarwa da kansa ba. 
Don haka shiru akai shi yafi.

Wannan kaso da nayi nayine don a gane sosai. 
Amma ban riski wani magabaci daya kassafasu hakan ba. Abin lura dai shi ne a gane dalilin karkasa siffofin. Wanda tun daga nan mai hikima zai banbance tsakanin aya da tsakuwa.

✒️
Naseeb 
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.